Rabiu Ali Indabawa" />

Dangote Ya Mayar Da Martani Ga Dan Wadan Da Ya Ce Ya Fi Shi Kudi

Hamshakin dan kasuwan nan Nijeriya kuma wanda ya fi kowa dukiya a nahiyar Afrika, wato Alhaji Aliko Dangote, ya mayarwa da fitaccen dan wadan nan dan kasar Ghana da a ke kira da Shatta Bandle, wanda ya bayyana cewa yafi Dangote arziki, martani.

Dangoten ya mayar da martani ga wadan ne bayan an yi wata hira da shi, inda ya ce, “ba zan yi gasa da kowa a kan kudi ba. Duk wanda ya ce ya fi ni kudi, ni Ina ganin ba matsala ba ne a wurina. Ina da iya arzikina kuma Ina matukar farin ciki da abinda Allah ya arzurta ni da shi.

“Ba ni da wani abu da zan nuna wa duniya da zai bayyana cewa Ina da kudi. Duniya ta san da ni ne saboda irin ayyukan da na ke yi na taimakon al’umma.”

Wadan, wanda ainihin sunansa shi ne Idrissu Firdau, ya yi suna sosai a kafofin sadarwa bayan ya fitar da wani bidiyo ne, inda ya ke bayyana cewa ya fi Alhaji Aliko Dangote kudi, sannan kuma ya bayyana kudurinsa na zuwa ya yi magana da mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, wato Bill Gates, inda ya yi ikirarin cewa akwai wata harkalla da za su hada tare da shi.

Exit mobile version