Daga Abubakar Abba
Kamfanin Rukunin Dangote zai zuba jarin Dalar Amurka Biliyan 4.6 a harka noma nan da shekaru biyar masu zuwa.
Shugaban Kamfanin Rukunin na Dangote Alhaji Aliko Dangote ya sanar da hakan a taro baje kolin kayan noma karo na shida na shekarar 2017 da ya gudana a Abuja. Aliko ya ce, kamfanin zai zuba jarin ne a dangaren Sukari da Tumatir da Shinkafa da Manja.
Dangote wanda Daraktan sashen masu ruwa da tsaki da sadarwa na kamfani,n Alhaji Mansur Ahmed ya wakilta a wurin taron, ya yi kira ga matakan gwamnati uku da ake dasu a kasar nan dasu gyara da giggina hanyoyin da ke Karkara don samun saukin jigilar amfanin gona, musamman ganin yin hakan zai rage tsadar aiki da farashin amfanin gona.
Dangote ya ci gaba da cewa, idan aka inganta kimiyya wajen aikin noma, da aka samar da nagartaccen iri da taki, manoma zasu samu amfanin gona mai yawa.
Ya yi nuni da cewa idan har ana son harkar noma ta ci gaba a kasar nan, dole ne manoma su sake zage damtse, kuma wajibi ne a ja matasa cikin harkar.
Daga karshe, Dangote ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su kirkiro da shirye-shirye da ke da nasaba da harkar noma, musamman don marawa gwamnatin tarayya baya akan kokarin ta na kara wadata kasar nan da
abinci.