Alkaluma daga hukumar lura da kudin musaya ta kasar Sin, sun nuna yadda kasar ta samu karuwar darajar cinikayyar waje ta fuskar hajoji da hidimomi, wadda a watan Afirilun da ya gabata ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 4.37, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 606.8, karuwar da ta kai ta kaso 6 bisa dari a shekara.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna karuwar darajar hajoji da hidimomi da Sin ta fitar ketare zuwa dala biliyan 326.5, yayin da darajar wadanda ta shigo da su ta kai dala biliyan 280.3, inda aka samu rarar dalar Amurka biliyan 46.2. (Mai fassara: Saminu Alhassan)