Abubakar Abba" />

Darajar Naira Na Iya Faduwa, Kuma Bukatu Na Iya Karuwa -Bincike

Mai yuwa naira za ta kara sauka akan dala a cikin sati mai zuwa a babban bankin kasa CBN da kuma kudin musaya saboda karin bukatar ganin cewar, kamfanoni suna neman su mayar da riba tare da abinda suka samu na shigar su a karshen kaka da kuma jarin da masu zuba jari suka zuba.

A cewar ‘yan kasuwa masu hada-hadar kudi naira ta sauka zuwa 361 a ranar juma’a a data gabata a kasuwar daga  360 bayan tsawar data yi a cikin wattani shida da suka wuce. A rahoton da kafar yada labarai ta Reuters ta wallafa, ya nuna cewar, amma a hukumamce, naira ta kai  305.70, bayan da CBN ya bayar da tallafin da ya saba bayarwa. Akan bayar da bashi, kudin sun kai dala  314.50 a ranar Alhamis din da ta gabata.

Sashen kasuwar ta rufe akan dala 362 a ranar juma’ar data gabata harda ta ranar Litinin.

A ranar Larabar data gabata CBN ya zuba dala miliyan  210m  a tsinikayya ta tsakanin bankuna dake samar da kudadenb musaya a ci gaba da kokarin da ake yi don kaucewa durkushewar naira a kasuwar.

CBN ya zuba dala miliyan 100 ga dilolin da aka amince dasu a kasuwar. A shashen matsakaitun sana’oi sun samu dala miliyan 55, inda kuma kuma aka ware dala miliyan 55 ga kamar biyan kudin makaranta da bil din kiwaon lafiya dana tafiye-tafiye.

Daraktan riko na sashen sadarwa na CBN Mista Isaac Okorafor, ya tabbatar da wannan alkaluman kuma ya kara jadda da cewar, bankin ba zai yi kasa a gwaiwa ba wajen bayar da tallafin na kudin musaya.

A karshe Okorafor ya shawarci bankuna masu ajiye kudaden su dasu ci gaba da girmama bukatun abokan huddar su, musamman wadanda keda bukata ta musamman, inda yace bankin ba zai gajiya ba wajen kokarin sa don ganin bai bari hada-hadar ta kudin musayar kudaden musayar basu durkushe a kasuwar ba.

Exit mobile version