Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Daraktoci Za Su Koma Karantarwa A Makarantun Nasarawa —Almakura

by Tayo Adelaja
September 13, 2017
in LABARAI, MANYAN LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abubakar Abdullahi, lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana cewa za a mayar da wasu daraktoci da mataimakan su na ma’aikatu da hukumomin gwamnati aikin koyarwa a makarantun sakandaren jihar.

samndaads

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin bikin bude taron horaswa na yini biyar ga ma’aikatan jihar wanda ke kan gudana a birnin Lafia babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce, maida daraktoci da mataimakansu gudanar da aikin koyarwa zai bai wa dalilibai damar amfana da ilimin da suke da shi da kuma kara yawan malaman makarantu a jihar.

Haka nan, ya sanar cewa kafin nan da karshen wa’adin mulkinsa a 2019, gwamnati za ta dibi wadanda suka kammala karatu har mutum 2000 aiki. Tare da cewa nan bada dadewa ba za soma shirin dibar sabbin ma’aikatan.

A hannun guda, Al-Makura ya ce ba a son ransa ne ya gaza daukar ma’aikata ba a gwamnatinsa sai dai sakamakon karancin kudi da gwamnati ke fuskanta saboda matsin tattallin arziki. Ta bakinsa, “Akwai dubban wadanda suka kammala karatu a Jihar Nasarawa idan muka ce za mu ba su aiki mu biya su,  kudaden da za a tafiyar da gwamnati ma ba za su samu ba, kenan tilas mu bi a hankali mu yi abin da ya dace”.

Da ya juyo kan taron horaswar kuwa, Gwamna Al-Makuracewa ya yi an shirya taron ne da zummar farfado da ma’aikata ta yadda gudanar da aikinsu zai inganta fiye da yadda suke yi  a yanzu.

Ya ci gaba da cewa taron horaswar zai bai wa ma’aikatan damar zurfafa ilimi da sanin ka’idojin aiki daban-daban.

“Yan siyasa ne ki kirkiro da kudurori da manufofin gwamnati, to amma aiwatarwa na ga ma’aikata, kenan ya zama tilas a horas da su yadda za su tafiyar da harkokinsu ba tare da tangarda ba”, in ji shugaban.

Ya bukaci ma’aikatan da ke halartar horon da su sanya ido da kunnuwan basira domin daukar darussan da za a koya musu yadda ya kamata.

A jawabin da ya yi yayin bude taron, Darakta Janar na hukumar kula da sanin makaman aiki wacce da hadin gwiwarta ce ake gudanar da horon, Joseph Ari Wanda, Daraktan sadarwa na hukumar Dickson Chinedo Onouha, ya ce gudanar da taron horaswar ya nuna irin kishin ma’aikata da gwamnatin Al-Makura ke da shi da kuma saka kowa cikin tafiyar da aikin gwamnati.

Tun farko, sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron shugaban ma’aikatan jihar Mr Thomas Ogiri, yaba wa gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya yi kan bullo da shirin horaswan inda ya ce baya ga horon, Gwamna Al-Makura ya yi abubuwa da dama na inganta jin dadi da walwalar ma’aikata da suka hada da aiwatar da biyan albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas da bada bashin gidaje da motoci da kuma kudaden kayan daki ga manyan sakatarori da dai sauransu.

A karshe, ya bukaci ma’aikatan da su rika yin aiki ta hanyar sakawa ga irin abubuwan da gwamnati ke musu. Baki daya, kimanin ma’aikata dari uku da arba’in da hudu ne suka halarci taron da ya gudana a babban zauren taro na Ta’al Otel.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tsakanin Nnamdi Kanu Da Sojojin Nijeriya: Kar A Bari Ungulu Ta Koma Gidanta Na Tsamiya (II)

Next Post

Zuba Jarin Naira Biliyan 100 Na Sukuk: An Yaba Wa Gwamnatin Tarayya

RelatedPosts

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

by Yahuzajere
9 mins ago
0

A kokarinta na tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan, Hukumar...

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

by Daurawa Daurawa
3 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Rahotonnin da suke fitowa daga fadar...

Tattabaru

Abin DaYa Sa Tattabarun Da Buhari Ya Saki Ba Su Tashi Ba – Adesina

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa...

Next Post

Zuba Jarin Naira Biliyan 100 Na Sukuk: An Yaba Wa Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version