Daraktoci Za Su Koma Karantarwa A Makarantun Nasarawa —Almakura

Daga Abubakar Abdullahi, lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana cewa za a mayar da wasu daraktoci da mataimakan su na ma’aikatu da hukumomin gwamnati aikin koyarwa a makarantun sakandaren jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin bikin bude taron horaswa na yini biyar ga ma’aikatan jihar wanda ke kan gudana a birnin Lafia babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce, maida daraktoci da mataimakansu gudanar da aikin koyarwa zai bai wa dalilibai damar amfana da ilimin da suke da shi da kuma kara yawan malaman makarantu a jihar.

Ya kara da cewa ba wai wadanda za a mayar da su azuzuwa karantarwar ba su tabuka komai ba ne a wuraren aikinsu a’a, sai dai domin a samar da karin malaman da ake bukata a makarantun sakandaren jihar.

Haka nan, ya sanar cewa kafin nan da karshen wa’adin mulkinsa a 2019, gwamnati za ta dibi wadanda suka kammala karatu har mutum 2000 aiki. Tare da cewa nan bada dadewa ba za soma shirin dibar sabbin ma’aikatan.

A hannun guda, Al-Makura ya ce ba a son ransa ne ya gaza daukar ma’aikata ba a gwamnatinsa sai dai sakamakon karancin kudi da gwamnati ke fuskanta saboda matsin tattallin arziki. Ta bakinsa, “Akwai dubban wadanda suka kammala karatu a Jihar Nasarawa idan muka ce za mu ba su aiki mu biya su,  kudaden da za a tafiyar da gwamnati ma ba za su samu ba, kenan tilas mu bi a hankali mu yi abin da ya dace”.

Da ya juyo kan taron horaswar kuwa, Gwamna Al-Makuracewa ya yi an shirya taron ne da zummar farfado da ma’aikata ta yadda gudanar da aikinsu zai inganta fiye da yadda suke yi  a yanzu.

Ya ci gaba da cewa taron horaswar zai bai wa ma’aikatan damar zurfafa ilimi da sanin ka’idojin aiki daban-daban.

“Yan siyasa ne ki kirkiro da kudurori da manufofin gwamnati, to amma aiwatarwa na ga ma’aikata, kenan ya zama tilas a horas da su yadda za su tafiyar da harkokinsu ba tare da tangarda ba”, in ji shugaban.

Ya bukaci ma’aikatan da ke halartar horon da su sanya ido da kunnuwan basira domin daukar darussan da za a koya musu yadda ya kamata.

A jawabin da ya yi yayin bude taron, Darakta Janar na hukumar kula da sanin makaman aiki wacce da hadin gwiwarta ce ake gudanar da horon, Joseph Ari Wanda, Daraktan sadarwa na hukumar Dickson Chinedo Onouha, ya ce gudanar da taron horaswar ya nuna irin kishin ma’aikata da gwamnatin Al-Makura ke da shi da kuma saka kowa cikin tafiyar da aikin gwamnati.

Ya yaba wa gwamnatin Jihar Nasarawa kan shirinta na koyar da sana’o’in hannu a jihar, yana mai cewa kasa ka iya zama cibiyar masana’antu da cigaba ne  kawai ta hanyar koyar da sana’o’in hannu ga jami’anta.

Tun farko, sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron shugaban ma’aikatan jihar Mr Thomas Ogiri, yaba wa gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya yi kan bullo da shirin horaswan inda ya ce baya ga horon, Gwamna Al-Makura ya yi abubuwa da dama na inganta jin dadi da walwalar ma’aikata da suka hada da aiwatar da biyan albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas da bada bashin gidaje da motoci da kuma kudaden kayan daki ga manyan sakatarori da dai sauransu.

A karshe, ya bukaci ma’aikatan da su rika yin aiki ta hanyar sakawa ga irin abubuwan da gwamnati ke musu. Baki daya, kimanin ma’aikata dari uku da arba’in da hudu ne suka halarci taron da ya gudana a babban zauren taro na Ta’al Otel.

Exit mobile version