Saminu Alhassan">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Darashin COVID-19 Ga Bil Adama

by Saminu Alhassan
December 31, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Darashin COVID-19
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A halin da ake ciki yanzu haka, annobar cutar COVID-19 na ci gaba da haifar da mummunan illa ga rayuwar bil Adama, inda karin mutane masu yawan gaske ke ci gaba da harbuwa da cutar.

Baya ga asarar rayuka da ake fuskanta, cutar ta kuma gurgunta yanayin rayuwa da aka saba da shi, ta dakile kyakkyawar zamantakewa, da tafiye tafiya, ta kuma takawa wasu manyan sassan cinikayya da harkokin raya tattalin arziki birki. Hakan ya jefa ayar tambaya a zukatan masharhanta da dama, game da ko yaya duniya za ta kasance bayan wannan annoba?

samndaads

Darashin COVID-19

Daya daga sabbin kalubale da ake fuskanta a yanzu haka, shi ne gano sabbin nau’oin cutar da aka yi a wasu kasashen duniya, wanda hakan ya haifar da halin rashin tabbas, don gane da tasirin da ake hasashen alluran rigakafin cutar da ake samarwa yanzu haka ka iya yi.

Wannan kalubale ne da ya kamata a dauki matakan shawo kan sa. Domin kuwa, a kasashe da dama da suka samu shawo kan cutar ta hanyar daukar matakan kandagarki, shigar baki da ‘yan kasa masu komawa gida dauke da cutar na mayar da hannun agogo baya. Wannan na nuni da cewa, ba wata kasa da za ta iya tsira daga barazanar wannan annoba ta COVID-19, don kawai ta kare kan ta, ba tare da yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya wajen ganin bayan cutar a matakin kasa da kasa ba.

A takaice dai, ba wata kasa da za ta samu cikakken tsaro daga COVID-19, har sai dukkanin duniya ta samu tsaro daga cutar. Lallai wannan aiki ne mai wahalar gaske amma kuma ya zama tilas!

Idan an kalli wannan batu da idon basira, ana iya ganin wasu kalubalen dake gaban bil Adama masu kama da hakan, kamar sauyin yanayi, da karewar albarkatun da bil Adama ke bukata, da matsalolin tsaro, da zaman lafiya, da rashin daidaito tsakanin sassan duniya, wadanda dukkanin su kalubaloli ne da ya dace bil Adama ya yi hadin gwiwar shawo kan su cikin hadin gwiwa.

Cutar COVID-19 ta jaddada wannan bukata, ta kuma zamo darasi na irin bukatar da daukacin bil Adama ke wa juna, wajen daukar matakan magance matsaloli tare, don a gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)

SendShareTweetShare
Previous Post

Ma’aikatan Bogi: An Bankado Masu Watandar Biliyan N2.3 A Borno

Next Post

Yarjejeniyar Zuba Jari Tsakanin Sin Da Turai Za Ta Amfani Kowane Bangare

RelatedPosts

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

by Saminu Alhassan
16 mins ago
0

Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

by Saminu Alhassan
23 mins ago
0

Jiya Laraba, ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fidda bayanin...

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

by Saminu Alhassan
28 mins ago
0

Kakakin ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur...

Next Post
Yarjejeniyar Zuba Jari

Yarjejeniyar Zuba Jari Tsakanin Sin Da Turai Za Ta Amfani Kowane Bangare

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version