Darasi Daga Tafiya Mabudin Ilimi  

Shimfida

Ina farawa da sunan Allah, Buwayi gagara misali, na farko da babu komai kafin shi, na karshe da babu komai bayan shi, na sarari da babu komai a samansa, na boye da babu komai koma-bayansa, mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga Shugaban Halitta kaf, macecinmu bayi, farkon Bawan Allah, Annabi Muhammad (SAW), tare da Iyalansa da Sahabbansa da dukkan Waliyyan Allah da Salihan Bayi.

Mai karatu na fara da wannan shinfida ce domin neman kamun kafa; abin da zai gudana a wannan shafi ya zama bai yi talalabiya ba. Sannan da kwadayin nema daga Allah bayyanar da kyakkyawar fahimta ga zukatan dimbin al’ummar da za su rika karanta shafin, daga yanzu har zuwa abin da ya sauwaka.

Bukata daya daga masu karatu ita ce, neman hanzari daga gareku tare da rokon ku kalli duk abin da shafin zai rika zuwa da shi da zuciya ta rahamaniyya.

Kai tsaye, na zabi fara tattaunawa da masu karatu ne kan abin da ya shafi wata tafiya da muka yi zuwa Bangon Duniya, watau Kasar Sin, domin fadakarwa da ilmantarwa har ma da nishadantarwa garesu dangane da sababbin abubuwan da muka ci karo da su ko kuma in ce muka karu da su a can. Kasancewar masu iya Magana kan ce, “tafiya mabudin ilimi”, hakika na kara samun yakini da fahimtar ma’anar wannan Karin Magana a aikace ta dalilin wannan doguwar tafiya.

Watakila, mai karatu ya tafi duniyar tunanin yadda aka yi na samu zuwa kasar Sin ko?, to sha kuruminka, gyara zama ka ji zancen. Da farko, alakata da kasar Sin ta kullu ce sanadiyyar wani hadin gwiwa na aiki a tsakanin Sashen Hausa na Kamfanin Jaridun LEADERSHIP da ke Nijeriya da kuma Sashen Hausa na CRI, wadda tsohon Manajan Daraktan Kamfanin LEADERSHIP, Malam Abdul Gombe da kuma jagoran tawagar CRI, shugaban kula da hadin gwiwar CRI a bangaren Afirka da Asiya, Mista Wang Bico, suka tabbatar da ita ta karshe-karshen shekarar 2017 a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja.

Sauran ‘yan tawagar ta CRI da suka zo kulla zumunci da Kamfaninmu sun hada da mataimakiyar daraktar kula da ma’aikata ta CRI, Madam Yu, da shugaban sashen Hausa na CRI, Malam Sanusi Chen, da jami’ar fassarar harshen Faransanci ta CRI da kuma wani mawallafin jarida dan kasar Sin a Botsuwana, Mista Miles Nan, da ya rufa musu baya.

A karkashin hadin gwiwar ne muka amsa wani goron gayyata daga Ofishin Jakadancin Sin na Nijeriya zuwa kasar ta Sin, domin wata ziyarar aiki ta kwana goma.

A wani bangare na shirye-shiryen tafiya, ofishin jakadancin ya shirya mana wata walimar cin abincin dare tare da mataimakin jakadan Sin a Nijeriya, Mista Lin Jing a gidan Jakadan Sin da ke Unguwar Maitama a Abuja.

Wani abu da ya fara birgeni game da kasar Sin shi ne irin bayanan da muka ji kan bunkasar tattalin arzikinta a sulusin farko na shekarar 2018, daga bakin Mista Lin Jing, yayin gudanar da walimar, kasancewar mun yi tafiyar tamu ce a goman karshe na watan Afirilun 2018.

A ta bakin Mista Lin, “tattalin arzikin Kasar Sin ya bunkasa fiye da adadin abin da ake tsammani a sulusin farko na wannan shekarar, inda kididdiga ta nuna tattalin arzikin yana samun ci gaba mai dorewa. A sakamakon da Hukumar Kididdiga ta Kasar Sin ta fitar na irin bunkasar da tattalin arzikin kasar ya yi a sulusin farko na shekarar, bangaren kere-kere ya samu ci gaba da kashi 51.5 a cikin dari wanda ya nuna alamar bunkasa mafi girma a wannan tsakanin. Sashen kananan masana’antu shi ma ya habaka daga kashi 44.8 a watan Fabarairu zuwa kashi 50.1 a cikin dari a watan Maris. ‘Yan kasuwa masu masana’antu suna kara samun natsuwa da yakinin habakar tattalin arzikin kasar inda suka yi amannar da ba a taba gani ba tun daga sulusi na uku na shekarar 2011”.

Mataimakin jakadan ya kara da cewa ba wannan ne kadai ba, har ila yau amfani da wutar lantarki a kasar ya karu zuwa kashi 9.8 a sulusin farko na shekarar ta 2018, sannan ga tururuwar da ake kara samu daga bangaren masu sayen kayayyaki wadanda gamsuwarsu da kayayyakin da ake sarrafawa a kasar ta yi sama da maki 124, maki ma fi girman da ya kasance rabon a ga irinsa tun a watan Oktoban 1993.

Mista Lin Jing ya kuma bayyana cewa a bitar cigaban da Kasar Sin ke samu da Bankin Duniya ya yi a ranar 12 ga Afirilun 2018, daga watan Oktoban 2017 zuwa lokacin da ya yi bitar, Sin ta samu habaka daga kashi 6.4 zuwa kashi 6.5 a cikin dari. Wakazalika, a rahoton da Bankin Raya Kasashen Asiya ya fitar a ranar 11 ga Afrilun 2018, ya ce ana sa ran tattalin arzikin Kasar Sin ya cigaba da karuwa har ya kai da kashi 6.6 a wannan shekarar tare da buga misali da karuwar bukatar kayan da kasar ke sarrafawa a cikin gida da waje.

Ya kuma ce an samu karuwar sababbin ayyukan yi a Kasar Sin sama da milyan uku duk dai a sulusin farko na shekarar ta 2018, tare da ta’allaka ci gaban da aka samu da irin sauye-sauyen da ya ce shugaban kasar ya kaddamar.

Ba ni kadai irin ci gaban da Sin ke samu a wannan lokacin ya birge ni ba, hatta tsohon Manajan Daraktan namu, Malam Abdul Gombe, ya bayyana cewa,“yana da matukar ban-mamaki yadda Kasar Sin ke kara samun bunkasar tattalin arziki alhali galibin kasashen duniya suna cikin kaka-ni-ka-yin tsamo tattalin arzikinsu daga mawuyacin hali.”

A wannan lokacin, bincikena ya gano cewa Kasar Sin tana ba da gudunmawa ga cigaban tattalin arzikin duniya baki daya da kashi 30 a cikin dari.

Duk wadannan bayanai na ci gaban tattalin arzikin kasar mun ji su ne da kunne kafin tashinmu zuwa kasar, abin da ya rage shi ne mu gani da idanuwanmu kuru-kuru, kasancewar masu iya magana kan ce “gani ya kori ji”.

Mu kwana nan, mako mai zuwa za mu hau jirgin da zai isa da mu kasar, da kuma jin abubuwan da suka fara mana iso.

Exit mobile version