Connect with us

Uncategorized

Darasi Daga Wasikar Shehu Atiku Sanka

Published

on

Fassarar Rabi’u Umar Attijjaniy
Bisimillahir rahamanir Rahim. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu da Sahabbansa Ababan Alfahari, Allah ya kara yadda ga Shehinmu Ahmad Dan Muhammadu Attijjani da sauran abokansa ma’abota kusanci ga Allah.
Bayan haka, na rubuta wannan sako ne izuwa dukkanin ‘yan’uwanmu Tijjanawa wadanda suke a kasar Nijeriya da ma wadanda suke wasu kasashen.
Assalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu,
Ina tabbatar muku da cewa muna jin dukkan abubuwan da suke faruwa da ga masu inkari wadanda suke fitowa da suffar masu wa’azi kuma suke haifar da fitina tsakanin Musulmi da Musulmi. Duk da cewa wasu daga cikinsu suna danganta kansu da hukumominmu, har sukan ce su ne suka yi musu izinin yin hakan. To abin da za mu fada muku a nan shine, ka da ku soma waiwayawa zuwa wadannan mutanen kuma ka da lamarinsu ya dame ku. Kawai dai ku yi hakuri a bisa dukkan cutarwarsu gare ku. Kuma ka da ku kai karar kowa daga cikinsu izuwa hukumomi ko izuwa wasu. Saboda tabbas suna da alaka da su da kuma jagora izuwa gare su.
Saboda hakika manya-manya daga cikin ma’abota inkarin suna zaune ne a kasan hukumominmu, kamar yadda muke jin hakan daga bakin wasu daga cikinsu, wannan shi ne abin da yake rudarsu a kan hakan, suna cewa idan ma mun kai kararsu wajan hukuma ba za a duba wannan kara tamu ba.
To saboda haka muke umartar ku da ku kai kararku izuwa Allah Mai Karfi kuma Mabuwayi Wanda Babu Wanda ya isa ya gagare Shi. Kuma ku sani cewa yawan inkari da Kuma cutarwar Munkirai a gare mu, dalili ne wanda yake nuni izuwa ingancin nasabarmu da alakarmu izuwa Shehu Tijjani da kuma kasancewarmu Magadansa, kasancewarsa wanda ya samu kansa a cikin matsanancin inkari da cutarwa tun daga zamaninsa har izuwa yau kuma haka abin zai ta tafiya har izuwa gaba, kamar yadda Imamul Hatimi ya fada daga wajansa.
“Hakika na ganshi a cike da Munkirai a cikin dukkan abin da yake tabbata daga halinsa”.
Duk da cewa wasu daga cikin Mukaddamai sun kai kara wajan Shehu Tijjani Ibn Usman (Shehu Malam Tijjani Na ‘Yan Mota), na yawan cutarwar Munkirai kuma suka nema daga wajansa da ya isar wa da Shehu Ibrahim (RTA) dan a nemi addu’a daga wajansa.

Lokacin da ya gaya wa Shehu (RTA) sai ya ce “ka yi musu Albishir da cewa su Tijjanawa ne na gaskiya”, bayan wannan bai kara cewa komai ba.
Amma wannan mutumin wanda yake raba takardu wanda suke nuni a bisa kafirta mu, to ka da kuyi la’akari da shi da wadanda suke taimakonsa. Kuma ina horanku da ku karbe ta kuma ku ga abin da yake cikinta na hauka da wauta, don ku tabbatar da cewa wannan ba komai ba ne.
Kuma maganarsa ba ta bukatuwa izuwa nuni, saboda fadin Annabi (SAW) ko kuma wasu daga cikin Malamai. Ku dai kawai Soyayya Dan Allah ta Ishe ku, kuma ku tabbatar da cewa shi Batacce ne kuma Mai batarwa. Ku dai kawai ku nemi taimako da KARFIN ALLAH.
Wassalamu alaikum , Dan’uwanku, Alhaji Abukar Atiku Sanka
Laraba, 2 ga Jumada Sani, 1387, Bayan Hijira
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: