Darasin Da Za Mu Koya Daga Shirin Mata A Yau (1)
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darasin Da Za Mu Koya Daga Shirin Mata A Yau (1)

byLeadership Hausa
2 years ago
Mata

Shafukan sada zumunta, musamman manhajar Facebook da WhatsApp sun cika da muhawara da rubuce-rubuce game da wasu kalamai da ake danganta su da shirin nan na Mata A Yau da tashar talabijin ta Arewa 24 ke gabatarwa, wanda ke tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar mata da ta iyali.

Jama’a da dama sun yi ta bayyana ra’ayoyi mabambanta game da zargin da suke yi na cewa; manufofin shirin suna karo da koyarwar addinin Musulunci, da al’adar al’ummar Arewa.

Haka kuma yadda masu gabatar da shirin suke zakewa wajen bayyana rashin dacewar wasu abubuwa da suka shafi kare mutuncin mata da shawarwarin su na neman kawo gyara, ba su dace da zamantakewar Malam Bahaushe ba, wanda wasu ma ke ganin sun yi hannun riga da koyarwar addini.

Har ma da masu fadar maganganu na aibatawa da cin zarafi ga masu gabatar da shirin, suna musu zargin ana amfani da su ne don ya ki da addini ko rusa tsarin auratayya baki daya. Wadannan zarge-zarge sun yi muni ainun, duba da kasancewar su mata musulmi, iyaye, kuma ‘yan uwa a gare mu.

Sannan a matsayin su na ‘Yan’adam, suna iya yin kuskure a wani wuri, kuma akwai hanyoyi daban-daban na yin gyara ba sai an kai ga cin mutunci ba.

Kodayake tashar Arewa 24 na da ‘yancin fitowa ta kare kanta, ko ta yi magana don daidaita tsakaninta da masu kallonta, ko al’ummar da suke gabatar da shirye-shiryensu gare su.

Hakan ba zai hana mu yin sharhi ko tsokaci game da abubuwan da suka faru ba, don kara fadakar da jama’a, da samar da fahimtar juna.

Duk da yake a ta bakin daya daga cikin masu gabatar da shirin Halima Ben Omar, su a karan kansu suna ta kokarin ganawa da malamai da masu fada a ji, domin samun fahimtar juna da fayyace abubuwan da shirin yake fadakarwa a kai, don a daina musu gurguwar fahimta. Kuma in sha Allahu nan gaba zan yi kokarin tattaunawa da wasu daga cikinsu, don kawo muku sakamakon abubuwan da suka biyo baya, daga bangarensu.

Sai dai kafin lokacin zan so mu fahimci cewa; kowacce kafar watsa labarai na da manufofi da dalilan da ya sa ake kafata ko watsa shirye-shiryenta.

Sannan kafin a fara kowanne shiri sai hukumomin da abin ya shafa sun tantance su, sun kuma tabbatar da tsarin ayyukansu bai ci karo da dokokin kasa ko tsarin mulkin Nijeriya ba, wanda a cikinsa an tsare mutuncin kowanne addini da al’ada.

Kodayake tun bayan fitowar tashar a shekarar 2014 ‘Yan Nijeriya da dama sun rika nuna shakku da kokwanto kan manufofin kafuwar tashar mai amfani da harshen Hausa tsawon awa 24, musamman jin cewa tana da alaka da kasar Amurka.

An yi ta zarge-zarge kan cewa tashar na kawo shirye-shirye masu gurbata al’adu da tarbiyya, musamman shirin nan na wake-waken hip hop wanda Aminu Abba Umar Nomis Gee ke gabatarwa, wato Top 10, da wasu shirye-shirye da suka shafi wasan kwaikwayo na Dadin Kowa, Manyan Mata, da kuma shi wannan shiri na Mata A Yau.

Zan so in takaita bayanai na kan shirin Mata A Yau, wanda a kansa ne wannan dambarwa ta taso, kuma kamar yadda wani fitaccen marubuci, dan kishin Arewa, kuma mai fada a ji a harkokin ci gaban al’umma, Dr Aliyu Tilde ya rubuta a shafinsa na Facebook, “Wannan yana daga shirye-shirye masu amfani ga al’umma, inda mata suke tattauna matsalolinsu kuma suke kiran kwararru don karin haske. Na kan kalla, kuma na kan karu sau da yawa.” Nima zan iya cewa, ina kallon shirin Mata A Yau, kuma ina bibiyar yadda suke gabatar da tsarin shirin, duk da kasancewar ina da bambancin ra’ayi da su a wasu bangarori. Amma wannan ba zai hana in bayyana muhimmancin shirin ga rayuwar mata ba, da kuma kyakkyawan tsarin da aka yi wajen gina tsarin gabatar da shirin. Lura da yanayin bambancin shekaru da gogewar matan da ke gabatar da shirin, kowacce da bangaren da ta fito da kuma gungun matan da take wakilta. Don haka hadin gambizar matan da suke gabatar da shirin, shi ma wani abu ne muhimmi, da yake nuna manufar shirin.

Sai dai duk da kokarin da tashar ke yi wajen kiyaye koyarwar addini da al’ada, ba a rasa wani lokaci da akan samu kurakurai a wasu maganganu da akan yi amfani da su. Wannan kuma dole ne mu yi musu uzuri kasancewar duk dan’adam tara yake bai cika goma ba. Kamar lafazin da ake korafin daya daga cikin masu gabatar da shirin Aisha Umar Jajere ta yi amfani da shi, inda ta nuna cewa idan mata ba ta gaishe da mijinta ba, shi me zai hana ya gaisheta! Wannan a ra’ayin wasu masu tsokaci da kallon shirin ya sabawa tarbiyya da zamantakewar auren Bahaushe, kuma yanayin kalaman nata za su iya sa mata su rika raina mazajensu. Kodayake na san ba hakan ne manufarta ba, sai dai kokarin kawo maslaha tsakanin wadannan ma’aurata da aka ce maigidan ya aika da korafi a kan matarsa ba ta gaishe shi. Kuma ko nima na goyi bayan ra’ayinta, don bai kamata rashin gaisuwa ya kawo sabani ba, musamman tunda ma’auratan suna zaune lafiya da juna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Babu Abin Da Na Fi So Kamar Faranta Ran Marayu Da Raunana – Adesuwa Udo

Babu Abin Da Na Fi So Kamar Faranta Ran Marayu Da Raunana – Adesuwa Udo

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version