Darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, yana farin cikin hada kai da kasar Sin a fannin samar da allurar riga kafi da gano asalin cutar COVID-19.
Tedros wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka kira jiya Litinin, Ya ce, wata tawagar masanan hukumar lafiya ta duniya, da ta kunshi masana daga kasashen Australia, da Denmark, da Jamus, da Kenya, da sauran kasashe, za su yi tattaki zuwa kasar Sin, don gudanar da bincike game da asalin cutar da takwarorinsu na kasar Sin.
Tawagar masanan dake karkashin jagorancin Micheal Ryan, ta bayyana cewa, sakamakon binciken tawagar masanan na kasa da kasa a kasar ta Sin, ka iya taimakawa wajen hada bayanan kimiyya, haka kuma watakila ya taimaka wajen yin jagora kan bukatar kara fafada nazari a sauran kasashe. A game da batun gano asalin cutar da fahimtar tasirin annobar kuwa, WHO za ta je duk wata kasa ko yanki don tattara bayanan, idan bukatar hakan ta taso.(Ibrahim Yaya daga sashen Hausa na CRI)