Darektar ofishin binciken manufofi na kasar Sin na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da bunkasuwa (OECD) Margit Molnar, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin ce kasa ta farko da ta farfado bayan tasirin annobar COVID-19, wadda hakan ke da matukar muhimmanci ga duniya.
Molnar ta bayyana cewa, kasar Sin tana taimakawa kokarin kasashen duniya na yaki da wannan annoba, da samarwa sauran kasashe kayayyakin yaki da cutar. Haka kuma kasar Sin tana samar da kayayyakin sadarwa, don taimakawa sauran kasashe jure sauye-sauye a hanyoyin da suke rayuwa da ma yin aiki.
Ta kara da cewa, yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ci gaba da farfadowa, kasar Sin za ta ci gaba da samarwa sauran kasashe muhimman kayayyakin da suke bukata, za kuma ta farfado daga bukatar kayayyakin sarrafa kayayyaki daga ketare da ma kayayyakin bukatun jama’a na yau da kullum, kuma hakan na da matukar muhimmanci ga duniya baki daya.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hasua)