CRI Hausa" />

Darektar WEF: Matakan Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Su Taimakawa Sauran Kasashe

Babbar darektar dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) Sa’adia Zahidi ta bayyana cewa, matakan da kasar Sin ta yi amfani da su, har suka kai ga farfadowar tattalin arzikin kasar cikin hanzari fiye da yadda aka yi zato, bayan fama da annobar COVID-19, wata alama ce mai haske wadda kuma ka iya zama abin koyi ga sauran kasashe.

Sa’adiya Zahidi wadda ta bayyana haka jiya Litinin, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta ce, wannan ya kara nuna cewa, kasar Sin ce kasa daya tilo cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, da ta samu karuwar bunkasuwar tattalin arziki sosai.
Ita ma hukumar kididdigar kasar ta Sin (NBS) ta bayyana a jiyan cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kaso 2.3 cikin100 a shekarar 2020 fiye da shekarar da ta gabata, karuwar da ta zarce wadda aka yi hasashe.
A cewar hukumar, ana sa ran kasar Sin ce kadai, cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, wadda tattalin arzikinta zai bunkasa bayan wannan annoba.
Hukumar ta ce, karuwar GDPn kasar, ya zarce Yuan Triliyan 100, kwatankwacin dala triliyan 15.42 a shekarar 2020. (Ibrahim Yaya)

Exit mobile version