Connect with us

LABARAI

Daren Sallah: An Tsinci Gawarwakin Mata Bakwai A Wajen Gyaran Gashi

Published

on

Akalla mata Bakwai ne aka tsinci gawarwakinsu a cikin wani shagon gyaran gashi a garin Rijau, ta Jihar Neja.

Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da dare a lokacin da matan wadanda biyu daga cikinsu masu aure ne, suka je shagon gyaran gashin da yammacin ranar da nufin gyaran gashin na su cikin shirin da suke yin a bukin Sallah.
Kawo lokacin hada wannan rahoton dai ba a tantance dalilin mutuwar na su ba, sai dai wasu majiyoyi a garin suna cewa ana zaton matan sun mutu ne a dalilin hayakin janareta.
Rahotanni sun nu na cewa a sakamakon ruwan sama da aka yi ta tafkawa a wannan yammacin da kuma matsuwar da matan suka yi na su gyara gashin na su domin shiryawa bukin Sallah, sai matar da ke da shagon ta shigar da janaretan nata cikin shagon ta kulle duk da su a ciki sannan ta ci gaba da yi masu gyaran gashin.
A kan hakan ne aka bayar da rahoton cewa nan take hayakin ya shake biyar daga cikin matan suka kuma mace a nan take. Rahoton ya nu na cewa biyu daga cikin matan sun dan tsira da numfashinsu har ya zuwa washegari da aka gano su ma sun mace.
Duk kokarin da mutane suka yi na su garzaya da sauran biyun zuwa Asibitin da ke kusa da garin a Tungan Magajiya abin ya ci tura a sakamakon jinkirin da wani babban dan siyasa a garin ya haifar, wanda ya dage a kan cewa har sai shugaban karamar hukumar, Bello Bako, ya zo ya shaidi lamarin da idonsa tukunna kafin a kwashe su daga wajen.
Rahotanni sun nu na tuni an bai wa dangin mamatan gawarwakin in da suka yi masu jana’iza kamar yanda addinin Musulunci ya shimfida.
Ko da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayar da sunayen mamatan ba. Kakakin ya kuma bayyana cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike ne a kan dalilin mutuwar na su.
Advertisement

labarai