Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home MANYAN LABARAI

Darewar Gandujiyya Da Jami’an Buhari Ne Za Su Kawo Wa APC Cikas – Sanata Hanga

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in MANYAN LABARAI, RAHOTANNI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mustapha Ibrahim Tela,  Kano

Tsohon sanata kuma daya daga cikin masu fashin baki a al’amura siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulkin kasa, Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya ce, manyan matsalolin da za su hana APC cin zabe a 2019 a jihar Kano da kasa su ne wasu manyan matsaloli guda biyu, wadannan su ka hada da darewar mabiya gwamnan jihar Kano, wato ’yan Gandujiyya, da kuma wasu jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan bayanin ya fito daga bakin Sanata Hanga a wata hira da ya yi daban-daban a kafafen yada labarai a jihar cikin makon nan, inda ya ce, “a nan Kano akwai matsalar darewar Gandujiyya gida biyu. Wannan rigimar ta fi kowacce rigima hatsari a jam’iyarmu ta APC a nan Kano, domin ta fi rigimar Gandujiyya da Kwankwasiyya kuma ga shi a na so a maimaita, kuma maimaita kujerar zabe abu ne mai wahala, domin ya fi hawan farko wahala wajen cin zabe. To, ga shi kuma mutane ba sa jin dadin gwamnatin tarayya. Mutane su na cikin matsi wadda yakamata a taimaka mu su su fita daga cikin halin matsi.”

Sanata Hanga ya ce, su a matsayinsu na ’yan Gandujiyya kuma masu goyan bayan gwamnatin Ganduje da ta Buhari burinsu shi ne, a yi gyara domin idan ba a gyara ba, to lissafin ba shi da dadi kuma su ba za su daina fada ba, sai an gyara, kuma ba za su yi fushi ba, domin gyaran su ke so, saboda ya na sane da manyan matsalolin da ke cikin wannan tafiya kuma burinsa ya samu dama ya zayyana su, ya kuma ya bada shawarwari.

Ya nanata cewa, haka zai ta yi. Idan kuma hakan ba ta samu ba, to watan watarana zai tara ’yan jarida ya fada mu su matsalolin da su ka cukwikwiye APC a Kano, domin ya lura ba a gaya wa gwamna, sai dai a gyara ma sa magana da dai ji dadi kuma hakan ba daidai ba ne shi a matsayinsa na dan siyasa da bai iya fadanci ba da bambadanci ba.

Haka kuma Hanga ya ce, ya san wannan matsala ta na damun mutane da dama, musamman masu goyan bayan Ganduje da kuma son ya maimaita, amma ya na sane da cewa wanda wannan matsala ta fi damu shi ne shugaban jam’iyyar APC na Kano, Hon Abdullahi Abbas Dan Sarki Bafulatani. Ya ce, wannan ce ta sa Abdullahi Abbas ba zai fito fili ya yi kuka ba, amma ya tabbatar halin da ya ke ciki a tafiyar Gandujiyya ta na damun Hon Abbas, don yanzu a zuci kukan jini ya ke yi, saboda damuwa da kuma halin da jam’iyya ta ke ciki, domin bai samu wata dama da zai yi gyara da ya ke so ba a cewar Sanata Hanga.

“Haka kuma wata matsalar da za ta kada mu a zaben shugaban kasa 2019 ita ce rashin nade-nade da ba a yi ba na shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati wadda sun haura sama da 5,000 shugabannin hukumomi da gwamnati da duk ’yan PDP ne gwamnatin Jonathan ne ta nada su kuma su ita su ke yiwa aiki a yanzu, kuma ita za su taimakawa a zabe mai zuwa. To, kuwa ai matsala ne a ce kashi 90 cikin 100 ba naka ba ne na ’yan adawa ne.

“Ai su za su ka da kai don haka akwai matsala in ba a gyara ba wadannan sai sun tuntsirar da gwamnatin nan. Yanzu akwai shugaban hukumar NAFDAC da ya sauka wata tara har yanzu mataimakiyarsa ce a kan kujerar ba a nada wani ba, kuma har yanzu fayil ta ke dauka ta kai gida, ba a san me su ke yi ba a kan harkar aiki. Amma dai wannan ni ganau ne kuma Ina da shaida kuma hakan ta na faruwa a Abuja,” a cewar Sanata Hanga.

“Haka kuma kowa ya yi tsamanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga jinyar rashin lafiya ta kwana 103 daga Ingila an yi zaton abu na farko da dai yi shi ne cire mafiya yawan ministocinsa, musamman irinsu Chris Ngige na ma’aikatar kwadago wanda a ka zarga da batar kudi kimanin Naira Miliyan 500, musamman idan a ka yi la’akari da yadda Buhari ya nuna rashin jin dadinsa a lokacin da ya samu labarin haka, amma sai a ka ji shiru.

“To, wadannan matsaloline da za su kada mu kamar yadda tun a baya matar shugaban kasa ta fad. Ta ce, mafiya yawa wadanda a ka sha wuyar zabe da su Buhari ba ya tare da su, to wannan matsala ce ga kuma abinda Aisha Alhassan ta fada duk magana ce da yakama a yi la’akari da su.”

Haka kuma a karshe Sanata Hanga ya ce, duk wadda zai tsaya zabe, indai ba Buhari ba, ba kuma wani daga Arewa ba, to shi kam gwaninsa shi ne Kwankwaso, duk da ya san Kwankwaso ba ya kaunar sa kuma idan ya ci ba zai yi ma sa komai ba, “amma abinda na yi imani da shi,” in ji Hanga, “shi ne na san zai taimaki

SendShareTweetShare
Previous Post

Tun Sani Dankwairo Ba A Sake Samun Kamar Lil Ameer A Kasar Hausa Ba — Farfesa Abdalla

Next Post

Kanu Ya Garzaya Kotu Kalubalantar Kiran Su ’Yan Ta’adda

RelatedPosts

Makarantu

Idan Har Ana Son Tsaro A Makarantu: A Tarwatsa Dazukan ‘Yan Bindiga Da Bama-bamai –el-Rufai

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad, Hanya guda daya da za a...

Riga-kafin

Osinbajo Ya Nemi Amurka Ta Taimaka Wajen Samar Da Riga-kafin Korona

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Mataimakin Shugaban kasa  Farfesa Yemi Osinbajo...

Da Dimi-diminsa: An Maye Gurbin Idris Deby Da Dan Shi

Da Dimi-diminsa: An Maye Gurbin Idris Deby Da Dan Shi

by Muhammad
23 hours ago
0

Sojojin kasar Chadi sun zabi dan Idris Deby don maye...

Next Post

Kanu Ya Garzaya Kotu Kalubalantar Kiran Su ’Yan Ta’adda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version