Mustapha Ibrahim" />

Darikar Tijjaniyya Ta Allah Ce –Baba Impossible

Kwamishinan Al`amuran Addini na Jihar Kano, Dakta Muhammad Tahir Adamu Baba Impossible, wanda shi ma guda ne cikin mabiya Darikar Tijjaniyya ya bayyana cewa, wannan Darika ta Allah ce.

Don haka, babu wani wanda ya isa ya kwashe su dungurungum ya kai su wajen wani Gwamna ko Sarki da sunnanta, ko kadan ba za mu lamunta da haka ba.

Dakta Tahir Adamu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron Inuwar Matan Tijjaniya, karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Sayyada Fatima Muhammad Tahir, wanda aka gudanar a dakin taro da ke Masallacin Juma`a na Shehu Ahmadu Tijjani da ke Kofar Mata, ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan ya kara da cewa, kowane Dan Darikar Tijjaniyya yana da ‘yancinsa na kasancewa tare da Gwamna, sannan yana kuma da ‘yancin ya so Sarki ko akasin haka.

Haka zalika, mutum yana da `yancin yin kowace irin Jam’iyya da yake so ko ya ga ta kwanta masa, ko kadan wannan ba zai zama laifi ba. Amma kadai abinda ba za mu yarda da shi ba shi ne, wani ya dauke mu da sunan Tijjani ya kai mu wajen Gwamna ko kuma Sarki, ba za mu taba lamuntar wannan ko kadan ba, a cewar tasa.

Impossible ya cigaba da cewa, Shehu Ibrahim Inyas (R.A) a matsayinsa na Babban Malami, Bawan Allah, ko kadan bai kai darajar Sahabbai ba ballanta darajar Annabi Muhammadu (SAW). Amma dai ko shakka babu Bawan Allah ne, mai kuma kaunar Manzon Allah (SAW) ne tare da riko da sunnoninsa.

Haka nan, shi kansa Babban jagoran Tijjaniyya, Shehu Ahmadu Tijjani Abul Abbas (R.A), ba Annabi ba ne ba kuma Sahabi ba ne, amma masoyin Allah ne da Annabinsa (SAW), wanda ya karar da rayuwarsa wajen binsu har ya koma ga Allah.Saboda haka, a cewar ta Dakta Tahir, duk wanda ya kwatanta Shehu Ibrahim Inyas da Allah ko Annabinsa, ko kadan ba ya tare da mu, ba ya tare da Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyas, ba ya kuma tare da wan-nan Darika tamu ta Tijjaniyya kwata-kwata.

Ita ma a nata jawabin Shugabar Inuwar Matan, Sayyada Fatima Mu-hammad Tahir ta bayyana cewa, wannan Darika ko kadan ba ta tare da ‘yan hakika, masu yin maganganun da suka saba da koyarwar Shehu Ahmadu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyas. Don haka, an kafa wannan kungiya ta Inuwar Matan Tijjaniyya ne, domin bunkasa koyarwa tare da koyar da kyawawan dabiu da aikace-aikace na zikirin Tijjani a tsa-kanin mata da sauran alumma baki-daya.

Har wa yau a cewar ta Sayyada, yanzu haka wannan Inuwa ta Matan Tijjaniyya ta horar da Marayu guda 10 sanao’i tare da ba su tallafi, wanda zai taimaka musu wajen tafiyar da rayuwarsu cikin sauki. Kazalika, ta kuma nemi mata da sauran alumma, da su rike wannan Darikar ta Tijjaniyya tare da tallafawa al`umma, musamman mabukata a kodayaushe.

Sannan, a karshe ta yabawa Sayyada Ummahani Shehu Ibrahim Inyas (R.A), bisa irin gudunmawar da take ba yarwa wajen yada ilimi da kuma wannan Darika ta Tijjaniyya a nan Kano da ma duniya baki daya.

Exit mobile version