Connect with us

LABARAI

Daruruwa Sun Bar Garuruwansu A Sakkwato Saboda Fargabar Daukar Fansa Daga ‘Yan Bindiga

Published

on

Kusan mutane 5000 ne daga kauyukan Karamar hukumar Isa Ta jihar Sokoto aka rahoto cewa sun bar gidajensu yayin da yan bindiga su kazo daukar fansa akan ayyukan tsaron da jamian soji ke yi a yankunan.

An samu rahoton cewa, jirgi mai aman wuta yana ta kai hari a maboyar yan bindigar dake Dajin Karamar hukumar Isa Da Sabon Birni.
Wasu daga cikin yan bindigar sun gudo zuwa cikin kauyakun dake kusa da dajin a inda suka sake taruwa suka kai hari wasu kauyukan.

An rahoto cewa, yan bindigar sun kashe mutane 6, yawan shanu da dukiyoyi kuwa dasuka kashe suka barnatar har yanzu baasan yawan suba amma babu labarin sace kowa.

Daya daga cikin mutanen kauyukan dasuka gudu ya bayyana cewa, kauyukan da abun ya shafa sun hada da: Bafarawa, Arune, Suruddudu, Sabon Gari Lugu, Tsillawa, Gwalama da Dan Adama wadanda suke cikin Karamar Hukumar Isa.

Kuma ya kara da cewa: Mutanen da aka kashe akwai Biyu a Tsillawa daya a Suruddudu sai uku daga Kauyen Gebe.

Ya ce: Sama da Mutane 5000 sun gudu sun bar garuruwansu zuwa makobtan garuruwa kamar shinkafi dake jihar zamfara wasu kuma suna zaune da danginsu a wasu garuruwan.”

“Ai lokacin da mukaji labarin yan bindigar zasu da wo mun zata wasa ne, sai ranar Talata da dare kawai mukajisu a mashinansu su da yawa, suka fara harbi kan mai-uwa-da-wabi. Kuma sun tare hanyar mota dake shiga Karamar hukumar ta Isa sun kashe wasu a daren”

Mai bada labarun karamar hukumar Ta Isa, Surajo Isa ya tabbatar da rahoton kuma ya kara dacewa daga cikin wadanda suka gudu suka bar gidajen su, suna filin makarantar Primary ta Sardauna da Maitandu dake karamar hukumar Isa suna neman tsira, Manyan Garin suna taimaka musu da ruwa da abinci acan makarantar.

A lokacin da aka samu wannan rahoto, anso aji ta bakin mai Magana da yawun jamian tsaro na yan sandan jihar Sokoto,ASP Muhammad Sadiq, da mai Magana da yawun jamian sojin garin, Lieutenant Hammaga, amma baasamu jin ta bakin nasu ba.

Sai dai cewa Mai Jiran gado na yin Magana da bakin sojin sama, Tambari yayi alkawarin zai sake kiran waya in yasamu rahoto, a lokacin ganawar manema labarai amma shima ba asamu jin ta bakinsa ba.

In ba a manata ba dai, a ranar Litinin din da ta gabata ne shugaban sojin sama Air Marshall Sadique Abubakar yaziyarci jihar ta Sokoto inda yayi bayanin cewa, dakarun nashi zasu cigaba da kai hari a maboyar yan bindigar har sai anga karshensu gaba daya a yankin na Arewa Maso Yamma.
Advertisement

labarai