Connect with us

SHARHI

Darussa Kan Rasuwar Abba Kyari Daga Mairo Muhammad Mudi

Published

on

Allah, Madaukakin Sarki ya fada a Alku’aninSa mai girma cewa, duk wani rai, sai ya dandana mutuwa kuma daga Allah muka zo , daga gare Shi za mu koma.

Sa’in Abba Kyari ya kai, kila kuma wanda za a dauka daga shi said ni, ko kai ko ke. Ko dai a yashe ne ne, mutuwa ta zan dole a gare mu gabadaya in lokaci ya zo.
Ban taba ganin wanda wasu gungun ‘yan jarida da ‘yan Shoshialmidiya su ka sa gaba da surfa irin Abba Kyari ba.
Menene suka ce laifinsa a gare su banda zargin cewa shi ke sa shugaban kasa ya ce yi, ya yi, bari, ya kuma bari. Sun ce ya mai da shi kan keke saboda haka duk matsalolin kasar nan sun jigina ma sa.
Lokacin da labarin kamuwarsa da cutar zamani ta sarke numfashi ya barke, a bayyane wasu ke murna, tuni har suna fada cewa ya mutu. A ganinsu, Allah ne ke azabtar da shi baisa laifin da su ke ganin ya na aikatawa kasar nan.
Amma yau zan fada maku cewa Abba Kyari Dangatan Allah ne kuma ina kyautata masa zanton shi mutumin kirki ne ba yadda wasu makiyansa ke son mu fahimci sabanin haka ba.
Dukanmu mun yi imanin cewa Shi Allah ba azzalumin kowa ba ne kuma ba Ya fifita azzalumi kan wanda ake zalunta.
Ganin yadda Abba Kyari ya wanku sosai kan baiwa da daukaka da Allah Ya yi ma sa, sai yau ga shi a mace ma, Allah Ya fifita shi duniya suna kallo. Allah Kadai ne mai wa bawanSa baiwa a duk lokacin da Ya so ko da makiyansa ko masu kyashi ba su so ba.
Duk da mun San cewa watarana za mu tsallake mu bar duniyar nan amma abinda ya fi ba mu fargaba shine karshenmu da abinda za mu tarar a makwancinmu da kuma ranar sakammako. Duk wanda ya yi imani da Allah, wannan na cikin ransa, ba ta zo ba ba ta kuma wuce ba. Da shi ya ke kwana ya ke kuma tashi.
A matsayinmu da Muslimi mun fi mai da hankali a yadda za mu bar duniya saboda haka ko an haifi mutum yau ne addu’ar ba ta wuce, Allah Ya sa a gama da duniya lafiya, Allah Ya kyautata karshenmu, Allah Ya ba mu kyakyawar cikawa, Ya sa mu cika da kyau da imani.
Mun yi imani, Allah bai ya bai wa azzalumi, mugu kyakyawar karshe face ya yafe masa. Kuma in mun lura, azzaluman mutane ba su cika gamawa da duniya lafiya ba run wadanda suka addabin bayin Allah, don’t Shi Allah yana amsa addu’o’in bayinSa da aka zalunta cikin gaggawa kana Allah Ya na yafewa bayinSa zununbansu a kowane lokacin amma ban da cutar da dan Adam dan’uwanka face ya yafe ma ka.
Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a, ranar da ake kyautata zanton duk wanda ya mutu a ranar, ya dace, Abba Kyari ya rasu da cutar annoba wanda aka kwadaita wa duk musulmi cewa mutuwar shadata ce. Ya yi jinya, ya kuma samu wannan ciwo ne a hanyar aiki wa kasarsa da neman halal dinsa! Kun ga kenan ya yi babban rabo kuma muna kyautata ma sa rahamar Allah.
Darasi a gare mu shine, Allah Ya wanke Abba Kyari a idon duniya, Ya nuna mana shi ba macuci ko azzalumi da wasu suka dage da sai sun nuna mana hakan ba ne. Saboda haka mu dauki darasi cewa duk wanda muka gan shi a wani mukami, toh Allah ne Ya ajiye shi a wurin saboda haka mu bi shi da addu’a da fatan alheri. Mu roki Allah Ya sada mu da alherin da ke tattare da wannan bawa nasa da mukami da ya ba shi kana Ya kare mu daga dukan mugun gani nasa da mukaminsa maimako daura ra’ayoyinmu kan zanto da kunji-kunji da kuma wai-wai. Sai bayan ya wuce mu dawo muna cewa ai gara jiya da yau! Mu yi ta nadama!
Na yi imani, Allah da ya dauke Abba Kyari Ya fi duk masoyansa son shi, Ya kuma nuna wa makiyansa cewa baiwar tasa ce kuma zai Iya ba shi a duniya da kiyama, babu wani runutun batanci da zai iya tasiri.
Ga masu murnar Abba Kyari ya bar duniya, tsawon wani lokaci ne za Ku kai kuna murnar? Sannan mutuwarsa, kwanakin nawa za ta kara maku bisa kwanakin da Allah Ya deba maku kuma. Mu tuna duk mai rai mamaci ne.
Wani babban darasi shine cewa, wannan ciwo dai gaskiya ne kuma babu wanda zai yi wasa da shi ya kalla wa kansa don’t neman duniya. Sannan masu cewa, ciwon na manya ne ko masu mulki, ina da tamabaya, in har bai kyale manyan ba da komai ya ishe su, fada mani dalili guda da zai kyale ka kai talaka.
Don Allah mu kula da kanmu, mu bi dokoki da aka tsara ma na don hana yaduwarta, mu kasance masu addu’o’i akan komai da kowa.
Allah Ya jikan wadanda suka rasu, Ya bai wa wadanda suka kamu lafiya, Ya Kate wadanda ba su kamu ba daga kamuwa. Ya kawo mana karshen wannan anoba cikin gaggawa da koshin lafiya, amin.
Advertisement

labarai