Darussan Da APC Za Ta Koya Daga Babban Taron PDP

Daga Yusuf Shuaibu

A makonnin da suka gabata ne, jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na kasa wanda ya ba ta damar zaben sababbin shugabanni da za su tafiyartar da ragamar harkokin jam’iyyar, inda a yanzu kallo ya koma kan jam’iyya mai mulki ta APC wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yake shugabanci a karkashinta.

Was una ganin daga ranar Lahadi, 31 ga watan Oktoba, an yi bankwana da rikicin shugabanci na jam’iyyar PDP, bayan ayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, Ayorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar. Ayu da sauran jami’ai 19 cikin 21 daga kowane yanki na kasar nan za su jagoranci babbar jam’iyyar adawar duk da ta kasance cikin rarrabuwar kawuna da rashin daidaito da suka addabi jam’iyyar a baya.

Kafin samun wannan sauyi, jam’iyyar ta kasance cikin mummunar rikicin cikin gida wadanda suka hada da rarrabuwar kai, rikici a tsakanin shugaban jam’iyyar, Uche Secondus da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike. Tun lokacin da mulki ya subuce wa jam’iyyar a zaben sherakarar 2015, abubuwa suka rika hargitse mata, inda take ta fadi-tashin ganin ta dawo cikin hayyacinta.

A yanzu haka, jam’iyyar APC tana cikin matsanancin hali na shugabanci, inda aka samu rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki. A daidai lokacin da wasu ‘yan Nijeriya suka zura ido su ga irin sauyin shugabancin da za a samu a jam’iyya mai mulki, yayin da jam’iyyar PDP ta samu nasarar gudanar da sauyin ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba.

Bisa zaben Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP, wanda ya kasance malamin jami’a mai karantar da zamantakewa kuma tsohon minista a zamanin mulkin Obasanjo karkashin shugabancin jam’iyyar PDP, ana ganin wata nasara ce ga jam’iyyar. Mafi yawancin masana harkokin siyasa suna ganin cewa wannan yunkuri ne na dawo da martabar jam’iyyar a daidai lokacin da masanin dimokuradiyya ya amshi ragamar shugabancinta.

Tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma jakadar Nijeriya a kasar Kenya, Fidelis Tapgun ya bayyana cewa zaben Sanata Iyorcha Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP, ya kasance jam’iyyar ta sake dawowa turbar da magabata suka dorata a kai.

Tapgun ya ce, “Ba ana kiran jam’iyyar ba ne a matsayin PDP haka kwai. Da farko dai, ina taya sabon shugaban jam’iyyar murna da shugabannin kwamitin da suka gudanar da aikin babban zabe, inda a yanzu jam’iyyar ta fada hannun mutanen da suka fahimci alkiblar da ta sa aka kafa PDP a kai.

“Babu wani mutumin da ya yi tsammanin hakan zai iya faruwa a cikin jam’iyyar. Lokacin da mutane suka ga yadda asalin dimokaradiyya take a jam’iyyar PDP bayan kammala zaben shugabannin na kasa, mafi yawancin mutane sun shiga jam’iyyar.

“A daidai lokacin da jam’iyyar PDP ta samu sabon shugaba wanda ya kasance daya daga cikin jagora a PDP, ina tabbatar da cewa shi da tawagarsa za su ceto jam’iyyar.”

Muhimman matakan da jam’iyyar PDP ta bi tun lokacin da ta fadi zabe a shekarar 2015 su ne, gwamnoni karkashin jam’iyyar sun kasance masu karfi wajen gudanar da ragamar shugabancin jam’iyyar tare da gudanar da yarjejeniya ga ‘yan takara a kowani yanki. Ko da yake an samu kalubale wajen hada ra’ayoyin mutane masu yawa a wuri daya karkashin wannan jam’iyyar wanda ‘yan Nijeriya za su amince da shi. Yarjejeniyar da aka cimma da ‘yan takara shi ne a samu hadin kan dukkanin ‘ya’yan jam’iyya.

Wannan shi ne ya zame wa jam’iyya mai mulki ta APC kadangaren bakin tulu wajen rashin amincewa da gudanar da babban taro na kasa da rarrabuwar kawunan da aka samu a zaben shugabanni na jiha da kuma mataki na mazabu, inda ya kasance abu mai wahala wajen tsayar da lokacin gudanar da babban taro na kasa.

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2021, jam’iyyar APC ta gudanar da zabe na mazabu, sannan ta gudanar da zaben a mataki na kananan hukumomi a ranar 4 ga watan Satumba, yayin da ta gudanar da zaben a mataki na jiha a ranar 16 ga watan Oktoba. Tun a farko dai, an shirya za a gudanar da babban zabe a mataki na tarayya a watan Disambar shekarar 2020, inda aka dage zuwa watan Yunin shekarar 2021 bayan gudanar da taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar wanda Shugaban Kasa Buhari ya jagoranta a fadarsa da ke Abuja, a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2020.

An dai kaddamar da kwamitin ruko wanda Gwamna Mai Mala Buni yake jagoranta a watan Yunin shekarar 2020, inda aka bai wa kwamitin watanni shida da ya shirya babban zaben jam’iyya.

Sai dai an kara wa kwamitin Buni wa’adin wata shida a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2020, wanda ya kamata ya kare a watan Yunin shekarar 2021. An samu baraka a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2021, inda aka kara samun taron masu zartarwa na jam’iyyar da Shugaban Kasa Buhari ya jagoranta, ta kai ga an sake kara wa’adin kwamitin domin ya cimma abubuwan da ya sa a gaba.

Jim kadan bayan zaben sabon shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Iyorchia Ayu, ya fara shagube ga jam’iyyar APC wajen gaza wa shirya babban taronta na kasa.

Ayu ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki tana da shugabanni 92 a jihohi 36 da ke fadin kasar nan.

Da yake mayar da martani a kan rashin shirya babban zaben jam’iyya mai mulki, Darakta Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Dakta Salihu Lukman ya bayyana cewa zai yi wa babban jam’iyyar adawa wahala gudanar da amintaccen zaben jam’iyyar idan ita ke rike da shugabanci.

Lukman ya kara da cewa babbar jam’iyyar ta rasa mulki ne sakamakon rikicin cikin gida wanda ya dabaibaye ta na tsawan shekaru 16.

Ya ce, “’Yan Nijeriya sun rabu da jam’iyyar PDP da shgabanninta da kuma dukkan ‘ya’yan jam’iyyar. Ya kamata ‘yan Nijeriya su sani cewa jam’iyyar PDP ta samu gudanar da babban zabe ne domin ta sake dawo da martabarta.

“Bisa abin da ke gudana, shugabannin jam’iyyar PDP sun yi kokarin warware rikicin cikin jam’iyyar ne saboda ba sa kan kujeran mulki. Zai yi wa jam’iyyar PDP wahala ta gudanar da babban zabe cikin ruwan sanyi idan tana kan garagar mulki.

Sakamakon zaben Sanata Ayu, Taofeek Arapaja, Umar Damagum da sauran su, a karon farko a tarihin jam’iyyar PDP ta samu shugabanni bakin fuska ba kamar a baya ba. A baya, shi kansa shugaban jam’iyyar na yanzu ya fuskanci rashin adalci bayan ya kammala wa’adinsa na minista, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar AC daga PDP, inda ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar AC, Atiku Abubakar a zaben watan Afrilun shekarar 2007. Su dai Arapaja, Damagum, Anyanwu, Kosheodo bakin ido ne a rike mukamin na matakin tarayya.

Haka kuma jam’iyyar ta zabi dan shekara 25 mai suna Mohammed Kadade daga Jihar Kaduna a matsayin shugaban matasa na kasa. Ko shakka babu zabensa ya nuna gagarumin sauyi a cikin jam’iyyar, har ma PDP tana cewa APC da ba ta kokarin damawa da matasa tun lokacin da ta hau karagar mulki a shekarar 2015.

Matasa su ne suka fi yawa wajen gudanar da zabe, amma duk da yawansu gwamnatin APC ta kasa damawa da su a cikin harkokin siyasa. Duk da gwamnatin Buhari a karkashin jam’iyyar APC ta samar da dokar da zai bai wa matasa damar damawa da su a cikin harkokin siyasa, amma har yanzu an bar matasa a baya wajen shiga cikin majalisar zartarwa na shugaban kasa, ko da yake magoya bayan jam’iyyar sun bayyana cewa an zabi matashi mai shekaru 41 a matsayin shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

A daidai lokacin da jam’iyyar APC take kokarin bai wa dan shekarar 69, Bola Tinubu takarar shugabancin kasa wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari mai shekaru 78, jam’iyyar PDP tana kokarin mayar da hankali wajen damawa da matasan Nijeriya wanda take kokarin gyara kuskuran da ta tafka na watsi da matasan a baya kafin APC ta hau karagar mulki a shekarar 2015. A daidai lokacin da jam’iyyar APC take neman ranar da ta dace domin gudanar da babban taron jam’iyyar wanda zai ba ta damar samun zababben shugabanni, kuma tana ci gaba da samun kalubale na rikicin cikin gida wanda suke bukatar a magance su kafin gudanar da babban taron.

Exit mobile version