Dasuki Ya Tallafawa Matasa 350 A Mazabar Kebbe Da Tambuwal

Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Dan Majalisa Mai Wakiltar Mazabar Kebbe/Tambuwal a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honarabul Abdussamad Dasuki ya tallafawa matasa 350 da jari domin su bunkasa mabambantan sana’oi.

Honarabul Dasuki ya bayyana cewar matasa su ne kashin bayan ci-gaban kowace irin al’umma, don haka yake bayar da kulawar musamman wajen kyautata makomar manyan na gobe.

“Idan ba za ku manta ba a watannin baya lokacin da muka bayar da tallafi da kayan sana’o’i ga matan wannan mazabar a Kebbe na yi alkawalin bayar da jari ga matasan mu domin karfafa masu guiwar rungumar kananan sana’o’i. To alhamdulillahi a yau mun hadu a wannan muhimmin waje a wannan gari mai dimbin tarihi da albarka domin cika wannan alkawali.”

An gudanar da taron ne a masaukin baki na Marhaba Motel da ke a Jabo, Karamar Hukumar Tambuwal a karkashin jagorancin Mai Girma Sarkin Burmin Jabo, Alhaji Aliyu Garba II.

Hon. Dasuki wanda shine Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula da Sojojin Ruwa ya bayyana cewar da farko matasa 250 za a baiwa tallafin amma bisa ga yawan mutanen da ke akwai aka fadada tallafin zuwa matasa 350.

“A yau za mu baiwa matasa 350 jarin naira N20, 000 kowane domin taimaka masu wajen gudanar da kananan sana’o’i domin su zamo masu dogaro da kai.”

Dan Majalisar ya bayyana cewar a wakilcinsa yana iyakar kokarinsa domin ganin ya sauke nauyin da jama’a suka dora masa don haka a cewarsa ba da jimawa na zai sake gudanar da wani muhimmin abu ga mazabarsa.

A yayin da yake sanya albarka a taron, Mai Girma Sarkin Burmin Jabo, Alhaji Aliyu Garba II ya nuna farin cikinsa da tallafin tare da gargadi ga matasan da su yi amfani da tallafin yadda ya kamata.

A yayin da yake godiya a madadin matasan da suka amfana, Umar Balera ya godewa Hon. Dasuki kan tallafin da ya ba su da kuma kulawar musamman da yake bayarwa wajen bunkasa jin dadi da walwalar matasa da al’ummar mazabarsa bakidaya. “Muna godiya kwarai ga kyakkyawan wakilcin da wakilin mu ke yi mana kuma za mu yi amfani da wadannan kudaden yadda ya kamata.” Inji shi.

A zantawarsa da LEADERSHIP A Yau, Mataimaki na Musamman ga Hon. Dasuki kan Ayyukan Majalisa, Bashir Muhammad Umar (Tiger) ya bayyana cewar matasan da suka ci gajiyar wannan tallafin na musamman an zabo su ne daga kowace mazaba. Ya ce Karamar Hukumar Tambuwal ta na da mazaba 11, yayin da Kebbe ta ke da mazaba 10.

Ya ce “Wannan tallafin kari ne ga ayyukan alhairin da Hon. Dasuki ke yi wa al’ummarsa na wakilci nagari. Yanzu haka a kowane wata yana bayar da naira milyan daya ga mazabar Kebbe/Tambuwal domin gudanar da ayyuka da dama na wakilci nagari.

Bashiru Tiger ya bayyana cewar Hon. Dasuki ya himmatu wajen gudanar da mabambantan ayyukan wakilci a fannin ilimi, ruwan sha, bunkasa kiyon lafiya, rage radadin fatara, taimakawa marasa galihu da sauransu da dama da yake yi a wakilcin da al’ummarsa ke bayyana cewar tuni kwalliya ta biya kudin soso da sabulu.

Wakilinmu ya labarto cewar a watan Afrilu 2017 ne Hon. Dasuki ya tallafawa mata dubu daya da kayan sana’o’i da suka kunshi teloli da injunan nika da kuma naira milyan uku akan naira dubu 30 ga kungiyoyi 100 baya ga telolin hannu 40 da aka baiwa masu fama da lalura domin zama masu dogaro da kai.

Rahotanni a mazabar dai sun nuna da yawa daga cikin ‘yan adawa sun fara canza tunanin su a bisa ga yadda suka ga Hon. Dasuki ya himmatu wajen  gudanar da amintaccen wakilci tare da rungumar dukkanin al’umma a matsayin nasa ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

Exit mobile version