Datse Layukan Sadarwa: Halifan Tijjaniyyah Na Funtuwa Ya Bukaci A Sassauta

Daga Hussaini Yero,

Sakamakon mawuyacin hali da al’ummar yankunan da a ka dauke layukan Sadarwa a awani bangare na Jihar Katsina, Halifa Tijjaniyyah, Ali Saidu Alti Funtuwa, yayi kira ga Gwamna Aminu Masari da a sassauta dan al’umma na cikin mawuyacin hali. Halifa Ali Saidu Alti ya bayyana haka ne a wajan taron Mauludi da ya gudana a Zawuyar Sheka Abubakar Alti da ke Bakori Road Funtua cikin Jihar Katsina.

Halifa ya kara da cewa, Gwamnati Jihar Katsina Karkashin jagorancin gwamna Masari da jami’an tsaro suna iyaka kokarin su wajan yaki da “yan ta’adda da suka addabi al’ummar Jihar Katsina, kuma akoda yaushe muna yimasu addu’a dan ganin sun samu nasara.inji Halifan Tijjaniyyah.

” Duk da wannan masifa mu maka jawo da hannayan mu sakamakon munanan ayyuka da muke aikatawa da Allah ya hana sun zamo ruwan dare. masu karfi basu taimakon raunana, masu arziki basu taimakon marayu da marasa karfi, kowa kansa da iyalansa ya sani, Shugabani basu yin abuda ya ya dace, an kauce ma tafarkin tsarin Allah dan haka Allah ya jarabe mu da masifu kala Kala.

Akan haka Halifan Tijjaniyyah Ali Saidu Alti yayi kira ga Gwamna Aminu Masari da Shugabanin tsaro da su taimaka wajan dawo da layukan Sadarwa, dan yana taimakawa wajan tuna asirin ‘yan Bindiga idan suka shigo gari wajan shedawa jami’an tsaro dan kai ma al’umma dauki rashin sadarwa yana kara ba ‘yan Bindiga damar cin Karen su babu babaka a cikin karkara wanda yanzu haka suna afkawa garuruwan.

Exit mobile version