Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Kowane mutun nada irin tasa baiwar da Allah ya yi masa kuma mutane ke amfana da kyakkyawan tunani, yakana, sanin ya kamata da tsattseniinsa, wannan itace mahangar da al’ummar Jihar Kano kullum suke auna jajircewa da kwazon wanda Allah ya damka amanar Kanawa a hannusa.
Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi, gogaggen gogaggen malamin Makaranta, tsohon shugaban karamar Hukumar Tofa wanda ya shugabanci Karamar Hukumar har Karo biyar, wanda ya taba rike mukamin Kwamishina a Ma’aikatar kimiya da fasaha, yanzu kuma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake laluboshi tare da damka Ma’aikatar Ayyukan ta Jihar Kano a hannunsa, mukamin da a halin yanzu yake kai.
Tunda farkon zuwan gogaggen, Kuma jajirtaccen can kishin Kasa, sai da ya yiwa tsare tsaren Ma’aikatar kallon tsanaki, sannan ya dubi ma’aikatan da zai aiki dasu kuma ya fahimci masu mutane nee masu kishin cigaban Jihar Kano, hakan ta bashi damar shiga aiki ka’in da na’in, Wanda zuwa yanzu kwalli a key ci gabs biyan kudin sabulu.
Akwai muhimman ayyukan da Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bujiro dasu musamman batun mayar da Jihar Kano wani kasaitaccen birni, wannan kuma ko hasidin iza hasada ya yarda ba’a taba Gwamnan da ya samar da manyan ayyuka tare da kammala wasu da Gwamnatocin da suka gabata suka yi watsi dasu ba, musamman manyan asibitocin nan biyu wadanda a halin yanzu suke gogayya do kowane irin asibiti a duniya.
Gwamna Ganduje ne Gwamnan da sakewa wuraren da akayi watsi dasu shekara da shekaru, har wasu wuraren suke neman zama kufai, amma cikin kyakkyawan hange irin nasa ya sake masu fasali wanda ahalin yanzu wasu daga ciki tuni jama’a suka fara kwankwadar alhairansu.
Aikin samar da cibiyar koyon sana’u wanda matasa zasu dogara da kansu, wanda kuma aka zuba masu kayan aiki irin na zamani, wannan da ma sauran da lokaci banzai bari ayi gudu harda da zamiya wajen bayyana su ba, hakanne yasa wasu masu baki da kunu keta kokarin yiwa Gwamnatin Ganduje zagon wasa, wanda kuma ba zasu samu nasara ba.
Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi da yake tambihi kan cikar Gwamna Ganduje shekara 71 cewa ya yi, shekaru 71 na Gwamna Ganduje alhairi ne ga al’ummar Jihar Kano da ma Kasa baki daya. Domin masana da kungiyoyi masu zaman kansu sun jinjinawa Gwamna Ganduje tare da bashi lambobin yabo dake nuna jarumta da sadaukar da kai ga cigaban Kano da Kanawa.
Don haka jama’a da yawa daga ciki da wajen kasarnan ke tururuwa domin taya al’ummar kano murnar cika wadannan shekaru masu albarka, babu shakka cikar mutuntaka da sanin ya kamata tasa kullum jama’a ke godiya da sa albarka ga Jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
“Kanawa zamu jima muna amfana da kyakkyawan Jagoranci kan Samar da manyan ayyukan raya Kasa, musamman batun daga darajar asibitocinsu zuwa masu daukar gadaje 400-400.
A irin wannan lokaci da duniya ke fuskantar Matsalar tattalin arziki Wanda Haka ke barazana ga dorewar ayukan Raya Kasa, Amma duk da Haka Gwamna Ganduje shi ne Gwamna daya tilo da Bai taba yin batan watan albashin ma’aikatan Jihar Kano da ‘yan fansho, inji Unguwar Rimi.