Dattawan Arewa Na NEF Sun Amince Da Tsarin Shugabancin Karba-karba

Arewa

Kungiyoyin zamantakewar siyasa na Arewa sun cimma matsaya kan sake fasalin kasar nan. kungiyoyin sun yi imani da cewa sake fasalin zai amfani Nijeriya musamman ma a daidai lokacin da ake fuskantar zabe na shekarar 2023. A baya dai yankin Arewa ya taba adawa da kiran da ake na sake fasalin lamuran kasar nan.
kungiyar dattawan Arewa (NEF) da sauran shugabannin yankin sun bayyana cewa, ba za a shafa wa yankin bakin fenti ba wajen daukar manyan shawarwari game da shugabancin karba-karba. Jaridar banguard ta ruwaito cewa, kungiyoyin sun yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a, 9 ga Afrilu, bayan taron kwanaki biyu a Arewa House da ke Jihar Kaduna.
kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da kungiyar dattawan Arewa (NEF) da kungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) Arewa Consultatibe Forum (ACF) da sauransu. kungiyoyin sun bayyana sake fasalin kasar a matsayin abu mai mahimmanci ga ci gaban Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa daya.
A cewar jaridar Guardian, sun lura cewa Arewa za ta fi karfi idan ta magance gazawarta na cikin gida.
kungiyoyi sun ce, don rayar da Nijeriya, dole ne dukkan bangarorin kasar su dukufa wajen tallafawa ci gabanta a matsayin abu daya ba tare da sanya wani takamaiman sharadi ba.
A baya mun ji cewa, Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya bayyana cewa Arewa ba za ta yi amfani da kabila da addini ba wajen zaben shugabanni a shekarar 2023.
Jaridar Nation ta rahoto cewa yace ‘yan Arewa sun koyi darasi mai tsadar gaske.

Exit mobile version