ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

by Leadership Hausa
3 weeks ago
Zamfara

A sauyin da ya kawo a shugabancinsa, jajircewarsa na kawo ci gaba a fannin tsaro, zuba jari mai yawan gaske a fannin ilimi, kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa; kazalika a ƙoƙarinsa na sake mayar da Jihar Zamfara kan turbar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, Dauda Lawal shi ne Gwarzon Gwamnanmu na wannan shekara.

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya nuna jajircewarsa na jagoranci da ci gaba a fannin samar da ababen more rayuwa tare da hidimta wa jihar, wadda kusan shekaru goma ke fama da matsalar rashin tsaro. Gwamna Lawal, baya ga nauyin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da ganin jihar ta samu ci gaba, sannan kuma yana matuƙar taka muhimmiyar rawar gani wajen ganin an bai wa harkar ilimi da lafiya matsayi na musamman a gwamnatinsa.

  • Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

A ƙarƙashin wasu ayyuka da aka fi sani da “Ayyukan ceto Zamfara”, gwamnan ya aiwatar tare da kaƙƙamar da ayyuka daban-daban da suka haɗa da gine-ginen tituna, gyaran makarantu da kuma gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a garuruwa da kuma yankunan faɗin jihar.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, ya gabatar da tsarin makarantun Tsangaya, wanda ya tabbatar da samar da ilimin farko ga dukkannin yaran da suka isa zuwa makaranta a faɗin jihar. Tsarin ya tabbatar da ganin cewa; ilimin addinin musulunci da na boko sun kasance tare. Wannan aikin ya ƙunshi gina ɗakunan kwanan ɗalibai tara, ɗakunan malamai, ginin katanga, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, wuraren koyo da koyarwa da dai sauran makamantansu.

Makarantar tana da cibiyar koyar da sana’o’i, inda ake ba da horo a kan aikin kafinta, aikin sarrafa katako, ɗinki, kwamfuta ga ɗalibai.

LABARAI MASU NASABA

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal.

Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar. 

A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta.

Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura tare da samar da kayan aiki na zamani. Haka kuma an gyara tare da samar da kayan aiki ga babban asibitin da ke Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda a jihar. Babban asibitin da ke Kauran Namoda da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da shi, an samar da kayan aiki don isar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata. Kazalika, an sanya na’urorin bincike, gadaje, injinan ECG, injin centrifuge, injinan gwaje-gwajen jini, na’urar tantance jini ta atomatik da sauran wasu kayan aiki.

Kazalika, an kuma inganta babban asibitin Nasarawar Burkullu da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum. Bayan ayyukan kiwon lafiya da suka haɗa da na gaggawa, aikin tiyata, kula da lafiyar mata da yara, tsarin wurin keɓewa, wurin ajiyar gawa, ɗakunan tiyata na maza da mata, GOPD, ɗakin gwaje-gwaje, shagon magani, kula da mata masu juna biyu da kula da yar, duk an gina su. Sauran gyare-gyaren, sun haɗa da shingen gudanarwa, wuraren ma’aikata, masallatai da rijiyoyin burtsatse.

Haka kuma, a Ƙaramar Hukumar Maru, an gyara babban asibitin tare da samar da kayan aiki na zamani.

Gwamnan ya kuma kaƙƙamar da aikin sabunta birane, wanda ya kai ga gyara manyan tituna a jihar.

Dangane da batun tsaro kuwa, a shekarun baya-bayan nan, Zamfara ta ɗan samu jinkiri. A wannan lokaci na Gwamna Lawal, kashe-kashe da garkuwa da mutane ya ragu matuƙa a jihar. Hakan ya biyo bayan kafa jami’an tsaron da aka kafa a dukkanin kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

An horar da mutanen da aka zaɓo a tsanake, bisa cikakkiyar kulawar jami’an tsaron hukumar DSS, sannan suna yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro na yau da kullum, domin yaƙi da ‘yan fashi a jihar. A kwanakin baya ne gwamnan ya raba motocin aiki guda 140 da aka ware wa ƙungiyoyin tsaro daban-daban a faɗin jihar.

An haifi Dauda Lawal Dare, a ranar 2 ga Satumbar 1965, a Jihar Zamfara. Bayan kammala karatunsa na Firamare da Sakandare, ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa. Ya kuma yi digirinsa na biyu (M.Sc) a fannin kimiyyar siyasa/Hukunce-hukuncen ƙasa da ƙasa duk a jami’ar. Ya ƙara da digirin-digirgir (PhD) a fannin harkokin kasuwanci a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

Bayan kammala karatunsa na digiri na uku, ya yi kwasa-kwasai a Makarantar Kasuwanci ta Harɓard, Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Oɗford, Makarantar Tattalin Arziƙi ta Landan, Makarantar Kasuwancin Legas da sauransu.

Gwamnan ya yi aiki a matsayin jami’in ilimin siyasa tare da MAMSER, hukumar wayar da kan jama’a, don tabbatar da adalci da dogaro da kai a Nijeriya. A 1989, ya shiga Westeɗ Nigeria Limited a matsayin mataimakin babban manaja.

An naɗa shi a matsayin mataimakin ƙaramin jami’in shige da fice (immigration), a shekarar 1994, sannan ya zama babban jami’in hulɗa da jama’a a ofishin Jakadancin Nijeriya, Washington, DC, Amurka.

A shekarar 2003, ya koma bankin First Bank, a matsayin manajan hulɗa da jama’a, kuma a lokuta daban-daban ya kasance babban manaja a ofishin Abuja. A shekarar 2011, ya samu muƙamin mataimakin shugaban zartaswa, sashen gwamnati na Arewa na bankin na First Bank, bayan ya yi ayyuka da dama. A shekarar 2012, Dauda Lawal ya zama babban darakta a sashen gwamnati na Arewa, na First Bank.

Daga baya ya shiga siyasa ya kuma tsaya takarar Gwamnan Jihar Zamfara. A zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a shekarar 2018, ya sha kaye a hannun Idris Shehu Mukhtar. A zaben Gwamnan Jihar Zamfara na 2023, ya tsaya takara; kuma ya yi nasara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
Manyan Labarai

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
Manyan Labarai

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
Manyan Labarai

Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su

November 13, 2025
Next Post
Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

November 13, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

November 13, 2025
Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya

Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya

November 13, 2025
Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

November 13, 2025
Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

November 13, 2025
NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.