Taro na 60 na majalisar kula da hakkokin dan Adam ta MDD, ta amince da kuduri mai taken “Ingantawa da Kare Hakkokin Tattalin Arziki da Zamantakewa da Al’adu domin Kawar da Rashin Daidaito,” wanda kasar Sin ta gabatar a madadin kasashe kusan 70, cikinsu har da Bolivia da Masar da Pakistan da Afrika ta Kudu.
Da yake jawabi albarkacin cika shekaru 80 da kafuwar MDD da shekaru 30 na amincewa da yarjejeniyar Beijing ta kare hakkokin mata, Chen Xu, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa dake Switzerland, ya ce wannan kuduri da Sin ta gabatar na da nufin cike gibi da cimma matsaya daya da bukatar daukar matakai.
Kudurin na kira ga karfafa cudanya da hadin gwiwar kasa da kasa da tattaunawa kan batutuwa da musayar ra’ayoyi a majalisar kare hakkokin dan Adam da goyon bayan ofishin babban kwamishinan MDD mai kare hakkokin dan Adam domin ya inganta ayyukansa a fannin tabbatar da hakkokin da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa da al’adu, da sakar wa dandalin intanet na cibiyar ilimi kan kula da hakkokin tattalin arziki da zamantakewa da al’adu na MDD mara, don ya taka rawar da ta kamata, ta yadda za a samar da taimako bisa kwarewa da bunkasa kwarewar kasashe masu bukata.
Kasashe masu tasowa sun yi jawabi daya bayan daya, suna masu bayyana kudurin a matsayin wanda ya haska bukatar da daukacin jama’a ke da ita ta amsa kiraye-kirayen kasashe masu tasowa na kara zuba jari a fannin tabbatar da hakkokin da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa da al’adu. Haka kuma bangarori da dama ciki har da Tarayyar Turai, sun yaba wa kudurin. (Fa’iza Mustapha)