Daga Nasir S. Gwangwazo,
Rundunar Sojojin kasa ta Nijeriya ta bayyana cewa, babu bangaranci ko kabilanci a tsarinta yayin nada jami’an kwamiti mai kula da daukar sababbin jami’ai masu karatun gajeren zango (wato Short Service).
Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, a yayin da rundunar ke mayar da martani kan wani rahoto da aka wallafa a yanar gizo mai suna Global Sentinel, a ranar 29 ga Maris, 2021, tana mai cewa, an watsa labarin ne da mummunar manufa.
A cewar Yerima, rahoton ya yi zargin cewa, wadanda aka dauka din a karo na 47 da aka wallafa sunayensu ranar 26 ga Maris, an ’yan Arewa sun mamaye jerin sunayen, yayin da kuma aka bai wa yankin Kudu mafi karanci, musamman ma Kudu maso Gabas.
Rundunar ta bayyana cewa, ko kadan ba haka ba ne, domin “yana da kyau a san cewa, ta yi amfani da Tsarin Dokar Hukumar Daidaito ta Tarayya (Federal Character Commission),” inji ta.
Daga nan sai rundunar ta baje bayanin yadda ta dauki jami’an tana mai cewa, an ware wa kowacce jiha gurbi guda shida ne, idan banda a guraren da aka samu jihar da ba ta da yawan hakan da suka cancanta, inda sai aka yi la’akari da yawan yanki wajen cike wannan gurbin da aka samu.
Yerima ya ce, “kasancewar a haka tsarin yake, Yankin Kudu maso Gabas yana da jihohi guda biyar, wanda hakan ke nuna sun cancanci samun gurbi 40, amma duka da haka suka samu 42. Ita ma Arewa ta Tsakiya mai johohi bakwai har da Babban Birnin Tarayya Abuja ya kamata ta samu guda 56, ta samu karin guda biyu, don haka ta tashi da guda 58.”
Daga nan sai rundunar ta yi tir da kafafen yada labarai masu nuna son rai akan abinda za a iya gane shi a filin Allah.
Bugu da kari, sojojin sun yi kira ga al’umma, ciki har da manema labarai, da su rika neman cikakken bayani, kafin yin gaban kai wajen wallafa labaran da za su iya kawo shakku a zukatan jama’a, kuma “a karshe su zubar da mutuncin Rundunar Sojojin kasa tare da haifar da illa ga hadin kan Nijeriya.”