Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAUSAYIN MUSULUNCI

Dausayin Musulunci Musulunci Daya Ne, Saboda Cikarsa Yana Da Matakai Uku (2)

by Tayo Adelaja
September 26, 2017
in DAUSAYIN MUSULUNCI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani) 08051529900 (Tes kawai)

Wani ya taba tambayar Sayyidina Aliyu (Allah ya girmama fuskarsa) cewa “ya Imam, shin Allah yana da iko ya shigar da duniyar nan bakidaya cikin kwai ba tare da ya rage duniyar ya motse ta ba kuma ba tare da ya kara wa kwan girma ba?”

samndaads

Sai Sayyidina Aliyu ya kama shi ya ce, “Zo, kalli Dutsen Ukhudu ga shi can”, mutumin sai ya kalla, Sayyidina Ali ya ce “ka gan shi gabadaya” ya ce “eh”, sai Sayyidina Ali ya ce “shin Allah rage dutsen nan ya yi ya motse har ya shiga cikin idonka koko kwayar idonka ya buda (aka kara ma sa girma) har dutsen ya shiga cikin idonka?”, mutumin ya ce “duk ba a yi ko daya ba”, Sayyidina Ali ya ce “amma kuma gashi kana ganin dutsen ko?”, ya ce “eh”, sai Sayyidina Ali ya ce “to Allah mai iko ne, amma kuma ba a irin wannan tambayar. Kai dai ka san Allah mai iko ne kawai”. Ma’ana Allah mai iko ne ya shigar da duniya cikin kwai ba tare da ya motse ta ba; ba kuma tare da ya kara girman kwan ba. To wannan shi ne fagen Imani.

Sannan ka yi Imani da Littafan Allah. Attaura, Injila, Zabura da Alkur’ani maigirma. Ga su littafai ne da aka rubuta da bakar tawada amma kuma daga sama Allah ya sauko da su. Yana daga abin mamakin Alkur’ani ko sauran Littafan da Allah ya sauko da su, Allah ya ce da duk bishiyoyi (da tsinken) duniya za su zama alkalami, duk tekun duniya su zama tawada su dinga rubuta kalmomin Allah, za su kare amma kuma kalmomin Allah ba za su kare ba. Amma kuma ikon Allah; sai ka ga Alaramma ya dauk alkalami da ‘yar tawada a cikin kwalba guda daya sai ya shiga daki ya rubuto Alkur’ani bakidaya ya dauro a cikin wasu takardu. A zahiri iya Alkur’anin kenan, amma a badini ba iyakarsa ba kenan domin kalmomin Allah ba za su taba karewa ba. Nan ka ga fagen Imani ne wanda ake ce ma “Ilmul Kalami”.

Haka nan, ka yi imani da ranar lahira, ka san bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwa a gaba. Sannan ka yi imani da abubuwann lahirar, Aljanna, Wuta, Siradi da sauransu. Gada mai kwari da mota da sauran abubuwan hawa suke hawa mun san su, mun san kwarinsu. Duk abin da wani ya hau kansa ya iya daukar sa, wannan abin ya fi shi kwari, idan ba haka ba abin zai rushe. To, gadar da keke zai iya hawa mun san ta, wadda babur zai iya hawa, mun san ta; haka nan wadda mota za ta iya hawa, amma wata irin gada da ta fi zare siriri, ta fi reza kaifi, ta fi allura tsini a ce kuma duk halitta za ta hau kanta ba mu san irin ta ba. Wannan gada ita ce siradi kuma mun yi imani akwai, Tabaraka wa Ta’ala. Da sauran abubuwa na lahira masu dadi duk mun yi imani da su. Wannan ne abin da ake nufi da Akida ba wata hayaniya ba. Wato Imani da Allah, da mala’iku, da Littafai, da Manzanni, da Lahira, da Kaddara (mai dadi da akasin haka). Duk wanda ya samu wannan ya gode wa Allah, domin akwai wanda Musulmi ne amma bai iya karbar su ba; sun yi ma sa nauyi, don haka ake ce wa wanda ya hau wannan matakin Mumini saboda ya hau matakin Imani.

Da a iya nan Musulunci ya tsaya, mai tambayar nan (Mala’ika Jibirilu AS) sai ya tafi, amma da yake ba a nan Musulunci ya tsaya ba, sai ya sake tambayar Manzon Allah (SAW) cewa “mene ne Ihsani?”, wato kyautayai.

Manzon Allah (SAW) ya amsa da cewa “Ihsani shi ne ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ka zamanto kai ba ka ganin sa, to (ka sani) shi yana ganin ka”. Manzon Allah (SAW) ya fara da mushahada (ganin Allah) sai ya kare da mukarakaba (kusanci da Allah).

Misalin wannan, idan wani makaho ya zo wurinka yana magana, koda shi makahon ba ya ganin ka ai yana da yakinin cewa kai kana ganin sa. Duk da ba ya ganin ka kuru-kuru; ba zai yarda ya yi wani wargi ko abin kunyar da ba ya so ka gani ba, saboda yakininsa cewa kana ganin sa. Toh, kamar yadda makahon nan yake haka muke zuwa Fadar Allah, sai dai wadanda a cikinmu zuciyoyinsu suka wanku suke ganin Ubangiji da haka’ikun zuciya, ba ido na kai ake nufi ba a nan. So ake mu zamo a gaban Allah muna ganin sa, idan kuma mun kasa (Allah ya sauwake) tofah mu san Shi (SWT) yana ganin mu. Wannan wani fage ne mai ilimi da yawa.

Abin lura tun daga bayanan da muka fara a farko shi ne. Kowane mataki a cikin matakan Musuluncin da Manzon Allah (SAW) ya bayyana mana, yana da ilimin da ake sanin sa da shi. Ilimin da zai sanar da mu Matakin Musulunci da za mu bauta wa Allah (SWT) da shi, kamar sanin hukunce-hukuncen Sallah, Zakkah, Azumi, Hajji da sauran hukunce-hukunce shi ne Fikihu. Duk ilimin fikihu a tsakanin wadannan abubuwan yake kewayo, sai zancen su gado, kasuwanci, aure da sauran su. Malaman da suke karantar da wannan ilimin (Allah ya saka musu da alkhairi) su ne ake kira da Fakihai. Akwai manya-manyansu har da masu Maz’haba ma irin su Imam Malik, Imam Abu Hanifa, Imam Ahmadu bin Hambal da Imamus Shafi’i da sauran su Auza’i. Sannan akwai manyan littafai na fannin. Kamar mu a Maz’habar Imam Malik muna da Muwadda, Mudauwana, Mukhtasar, Askari, Risala, Iziyya har zuwa su Rashada. Sauran Maz’habobin ma suna da nasu.

Ilimin da yake koyar da matakin Imani kuma shi ne ake ce wa “Ilmul Kalami”. Fannin yana da manyan Malamansa da suka yi fice a cikinsa. Kamar Abul Hasanil Ash’ariy, Imamul Maturidiy da Imamu Ahmadu bin Hambal, Imamu Abu Hamidul Gazali da sauran su. Littafansu sun kunshi tun daga Ummul Barahiyn har zuwa Ilmut Tauhidi da sauran su.

Shi kuwa Ilimin da zai sanar da mu Matakin Ihsani wanda shi ne kololuwa, ana kiran sa Tasauwuf. Babu yanda za a yi ka san Ihsani na Musulunci idan ba ta hanyar Tasauwuf ba. Kamar yadda babu yanda za a yi ka san Ilimin Shari’a idan ba ta Fikihu ba ko Ilimin Imani ba ta Ilmul Kalami ba.

‎A mako mai zuwa za mu cigaba daga inda muka tsaya cikin yardar Allah (SWT). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Sauya Fasalin Nijeriya: Dole Arewa Ta yi Magana Da Murya Daya -Gwamna Masari

Next Post

Fahimta Fuska

RelatedPosts

kebance

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Masu karatu assalamu alaikum...

Kebance-kebancen Manzon Allah

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) I

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

A uzu billahi minas shaidanin rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Wa...

Annabi Isah

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (II)

by Muhammad
4 weeks ago
0

Tare da Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Bismillahir rahmanir Rahim....

Next Post

Fahimta Fuska

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version