Dausayin Musulunci: Yabon Da Allah (SWT) Ya Yi Wa Annabi SAW (6)

Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani) 08051529900 (Tes kawai)

A wata fassarar Kuma, ayar ta “wa wada’ana anka wizhrak, allazhi ankadha zahrak”, tana nufin “mun kiyaye ka wanda ba domin haka ba da zunubi ya nauyaya bayanka”. Malam Samarkandi ya fadi wannan.

Ayar “wa rafa’ana laka zhikrak” Malam Yahya bin Adama ya ce ma’anarta Allah yana nufin “mun daukaka ambatonka da manzanci”. Wato idan an fadi Allah da kadaitakarsa sai a fadi Manzon Allah da Annabtarsa. Idan aka fadi “La’ilaha illallahu” sai a ce “Muhammadur Rasulullah (SAW)”. Babu yanda za a yi kuma a raba.

A wata ma’anar kuma ayar tana nufin, Allah ya ce “idan aka ambace ni sai a ambace ka tare da ni” kamar yadda aka buga misali da kalmar shahada a sama.

Kila kuma ana nufin a cikin kiran sallah idan aka ambaci Allah; “Ash’hadu an la ila ha illallah” sai a ambaci Manzon Allah “Ash’hadu anna Muhammadur Rasulullah (SAW)”. Haka nan a cikin Ikama.

Malam Alkadiy Iyad ya ce wannan tabbatarwa ne daga Allah wanda sunansa ya daukaka cewa, ya yi wa Manzon Allah ni’ima mai girma da daukaka a wajensa. Allah ya ce ya yalwata zuciyar Manzon Allah (SAW) da Imani da Shiriya, ya kuma yalwace ta don haddace ilmi da daukar hikima (ma’arifa).

Kuma dama Allah ya ce “za mu karanta ma ba za ka manta ba”. A lokaci daya Allah (SWT) ya saukar da Surar Bakara kuma Manzon Allah (SAW) ya haddace ta ya karanta wa marubuta suka rubuta.

 

Har yanzu dai muna nan a cikin bayanin irin yabon da Allah (SWT) ya yi wa Annabi (SAW) a cikin Alam nash’rah, ayar da ta ce “mun daukaka ambaton ka”, wato aya ta 4 a cikin surar.

Sahabin Annabi (SAW) Katadatu (RA) ya ce, “Allah ya daukaka ambaton Annabi (SAW) a cikin duniya da kuma lahira. Babu wani mai yin huduba ko mai shaidawa ko sallah face yana fadin cewa na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Ma’aikin Allah ne”. Ma’ana a nan, Allah ya daukaka ambaton Annabi ta yadda idan aka fadi sunansa sai a fadi na Annabi (SAW).

Abu Sa’idul Kudri (RA), Sahabin Annabi kuma Dan Badar ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce “Jibrilu (AS) ya zo mun sai ya ce, Ubangijina kuma Ubangijinka – ya Muhammad – yana cewa shin ka san ma’anar fassarar ayar da ta ce Allah ya daukaka ambatonka? Sai na ce Allah ne da Dan Aikensa (Jibrilu) ya sani. Sai Jibrilu ya ce ma’anar an daukaka ambatonka ita ce Allah ya ce idan aka ambace shi sai a ambace ka tare da shi”.

Ibn Ada’in ya ce ma’anar “mun daukaka ambatonka” tana nufin “Allah ya sanya ambatonsa tare da ambaton Annabi ya zama cikar imani”. Wato idan aka ce “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah”, imani ba zai cika ba dole sai an hada da “Hakika na shaida Muhammadu Manzon Allah ne, (SAW)”.

Ko kuma Ibn Ada’in ya ce a wata ma’anar, ayar tana nufin “Allah ya sanya ambaton Manzon Allah a matsayin ambatonsa”. Wato duk wanda ya ambaci Manzon Allah (Muhammadu) tamkar ya ambaci Allah ne.

Shi ya sa ma wasu Malamai suka ce sunan “Muhammadu” daya ne daga cikin sunayen Allah da ya baiwa Annabi (SAW), kamar yadda ya bashi “Ra’ufu” da “Rahimu”.

A wurin Imamu Ja’afarus Sadik (RA) kuma, ma’anar ayar ta “mun daukaka ambatonka tana nufin “Babu wani mutum da zai ambaci Manzon Allah (SAW) da Manzanci face sai ya ambaci Allah, duk kuwa da cewa Allah ne Ubangiji”.

A bangaren wasu malamai kuwa, sun yi nuni da ma’anar ayar zuwa mukamin ceto a ranar Alkiyama. Ranar da kowa zai ce takaina nake yi, sai shi kadai (SAW) zai tashi ya nemi ceto a wurin Allah ya bashi. Kowa sai ya ambace shi a ranar, da Annabawa da mabiyansu kowa zai gaza, Annabi (SAW) kadai ne zai iya. Shi ya sa kowa za a ji yana kiran sunansa (Muhammadu, Muhammadu don godewa) har ma Allah a cikin Alkur’ani yake cewa “Allah zai tsayar da kai a wani bigire abin godewa”.

Haka nan, yana daga daukaka ambaton Annabi (SAW) da Allah ya yi, sa’ilin da ya gwama (hada) bin Manzon Allah a matsayin bin sa (SWT). Allah ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW).

Allah yana cewa a cikin Alkur’ani “Ku bi Allah ku bi Manzon Allah daidai-da-daidai (kamar yadda ma’anar wawun na ayar ta nuna)”. A wata ayar kuma ya ce “Ku yi Imani da Allah ku yi Imani da Ma’aikinsa daidai-da-daidai (ita ma wawun din ayar irin ta ayar baya ce, wato ta adafi)”.

Malamai sun ce bai halatta a hada irin wannan magana ba in ba a cikin hakkin Manzon Allah (SAW) ba. Shi kuma tunda Allah ne da kansa ya yi hakan, waye ya isa ya cire?

Malam Alkadiy Iyal ya kawo hadisi wanda ruwayarsa ta daukaka zuwa Sahabin Annabi Khuzaifatul Yamaniy (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce “Kar in ji wani dayanku ya ce Allah ya so (wani abu); wane ya so (shi ma, wato a sanya harafin wawun da ke nuna daidai-da-daidai), sai dai mutum ya ce Allah ya so; sannan wane ya so (ma’ana sai da Allah ya so, sannan daga baya wane ya so, ba tare da daidaitawa”. A ka’idar Larabci ba za a yi amfani da “wawun na adafi” ba sai dai harafin “summa”.

Malam Khaddabi ya ce Annabi (SAW) ya shiryar da Sahabbai yin ladabi ga Allah ta yadda sai an gabatar da son Allah sannan a gabatar da son wani (Kamar yadda ya zo a bayanin da muka yi a sama), don haka ne Annabi ya zabar musu amfani da “summa” ma’ana “sannan ko daga baya” domin jera magana da jinkirtawa. Wato sai an fadi na Allah, sannan daga baya a fadi na Bawansa.

Ya zo a wani Hadisi cewa wani mai huduba ya mike a gaban Annabi (SAW) zai yi huduba sai ya ce “Duk wanda ya bi Allah da Ma’aikinsa; ya shiryu, wanda ya saba musu su biyu kuma…” daga nan Annabi (SAW) ya ce “Tir da mai yi ma mutane huduba irin ka, tashi ka tafi”, ma’ana mai hudubar bai iya magana ba.

Abu Sulaiman ya ce Annabi (SAW) ya kyamaci hada sunayen guda biyu (na Allah da nasa) ne da harafin kinaya (jirwaye mai kaman wanka). Amma wani Malamin ya ce ba haka ake nufi ba, ya ce Annabi ya hana ne saboda mai hudubar ya yi wakafi a wurin. Sai dai kuma fahimtar Abu Sulaiman ta fi inganta saboda abin da aka ruwaito a Hadisi Sahihi shi ne mai hudubar bai yi wakafi ba a wurin harafin na kinaya (jirwaye), ya cike maganarsa inda ya ce “wanda ya saba musu su biyu ya halaka”.

Shi kuwa Imamun Nawawi ya ce duk ba haka ba ne. Ya ce sababin da ya sa Annabi (SAW) ya hana irin wannan hadawar saboda a huduba ne ya fada, kuma ita huduba ana so ne a fadi ma’ana wara-wara yadda za a fahimta filla-filla ba a yi kinaya ba. Shi ya sa Annabi (SAW) idan ya fadi wata magana sai ya maimaita don a gane. Amma ba wai ya ki a hada sunayen guda biyu (na Allah da nasa) ba ne. Domin hakan ya zo a cikin Alkur’ani da Hadisi.

Malaman Tafsiri sun yi sabani cikin ma’anar ayar da ke cewa “Allah da Mala’ikunsa “suna” yiwa Annabi salati…”, shin ma’anar “suna salatin” za ta zama a hada Allah Tabaraka Wa Ta’ala da Mala’iku ne cikin yin salatin ko kuma ayar ana kaddarata ce da ma’anar “Allah Yana salati”, “Mala’iku (su ma) suna salati”?.

Wane sashe na malamai sun tafi a kan “Allah Yana salati, Mala’iku suna salati ga Annabi…”, wasu kuma sun kyamaci a ce hakan. Sai suka kaddara fi’ilin (aiki) na “suna” ga Mala’iku bayan sun gabatar da Allah shi kadai Yana salatin a matsayin abin kaddarawa cikin “Yusalluu”, mana “suna”. Alkur’ani yakan kawo irin wannan abin kaddarawan.

To duk fahimtar da mutum ya dauka dai a cikin wadannan ya yi daidai.

Ba gyaran akida ba ne a rika cewa kar a rika ambaton Allah tare da Annabi, a’a, imani ma ba zai cika ba sai an ambaci Allah tare da Annabi (SAW). Shi ya sa ma idan ana neman wani abu ake cewa “don Allah don Manzon Allah”.

Exit mobile version