A ranar Talata ne tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ya kaddamar da fara aikin gina manyan tituna guda uku a sassa daban-daban na jihar Bauchi.
Da ya ke jawabi a yayin aza-tubalin ayyukan a Katanga Warji domin fara gina hanyoyin da suka tashi daga Warji zuwa Gwaram da kuma wanda ya tashi daga Bogoro zuwa Lusa tare da titin Boi zuwa Tapship da nisan hanyoyin ya zarce kilomita 35.5, Mark ya shaida cewar bude ayyukan za su kai ga bada damar bunkasa cigaban jama’a da jawo musu harkokin ci gaba kusa da su.
Tsohon shugaban majalisar sai ya jinjina tare da yaba wa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad a bisa himmarsa na raya jihar musamman ayyukan da ya ke budewa a birane da karkara, ya na mai jawo hankalinsa wajen ganin ya sake samar da wasu karin hanyoyin da za su kara hada kauyuka da kauyuka domin tabbatar da ci gaba mai ma’ana.
Mista Mark ya ce idan aka kammala aikin hanyoyin za a samu nasarar kyautata harkokin kasuwanci, saukaka wa jama’a wahalhalun rayuwa, sada jama’a da wasu jama’a ta fuskacin kyautata zamantakewar rayuwa da ingancinsa.
A cewarsa a karkashin mulkin PDP an samu sauye-sauye ta fuskacin gudanar da ingantattun ayyukan kyautata shugabanci da jagoranci idan aka kwatanta da wasu gwamnatocin.
A cewar gwamnan ayyukan tituna uku din an ware musu lokuta daban-daban da za a kammala su, amma wanda zai fi daukan lokaci shine wanda za a kammala shi zuwa nan da watanni 24 masu zuwa, ya na mai cewa dukkanin ayyukan an bada kwangilarsu ne kan kudi naira biliyan bakwai da digo uku 7.3bn.
Ya kuma ce, an bada kwangilar ne wa kamfanin Habibu Nigeria Engineering tare da yin tsare-tsare masu nagarta da za su kai ga samun nasarar aikin cikin hanzari da nagarta.
A gefe daya, Bala Muhammad ya yaba da irin kyakkyawar hadin kai da ake samu a tsakanin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar ta fuskacin tabbatar da kyakkyawar shugabanci da nemo wa jihar cigaba masu nagarta ba tare da la’akari da banbance-banbancen jam’iyya ko ta siyasa ba.
Ya bada tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da samar da ababen more rayuwa da jawo jama’a kusa da gwamnati domin kyautata musu rayuwa a kowani lokaci.
Tun da farko a jawabinsa, kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Cikasoro, ya shaida cewar muddin babu kyawawan hanyoyi a cikin al’umma to tabbas samun ababen more rayuwa zai ke musu wuya matuka.
A bisa haka ne ya nuna gamsuwar da cewa muddin hanyoyin nan suka kai ga kammaluwa tabbas al’ummomin da aka samar da titinunan dominsu za su samu ingantuwar rayuwa matuka.