Yusuf Shuaibu" />

Dawainiyar Da Ta Kamata Mata Ta Yi Wa Mijinta

Ya kasance matar aure ta zamanto mai mutunta aure saboda zaman gidan miji shi ne rufin asiri da cikar daraja gareta. Kula da hakkokin aure ga mace shi ne asirin jin dadin rayuwar aure da zaman lafiya a tsakanin ma’aurata, saboda haka wajibi ne mace ta kula da hakkokin da kanta ko dan ingantuwar zaman aure.

Ga wasu daga ciki kamar haka:

 

-Mace tilas ne ta lura da dukiyar mijinta ta hanyar tattalin abin da ya ba ta da kiyaye abubuwan da ya tanada dan rayuwar yau da kullum. Yin almubazzaranci ko wulakanta dukiyar miji na jawo bacin rai ga mai gida, sannan ga tsoron fushin Allah.

 

-Mace ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba sai da izinin sa, ko da gidan mahaifinta ne.  Ta kare kanta daga mazajen da ba nata ba ta hanyar gujewa magana da su ko matsanan cin kallo da dai sauran abubuwan da ya saba wa shari’a. Mace ta guji fidda halittarta ko caba ado da turare mai kamshi lokacin da lalura ya sanya za ta fita daga gidanta. Mafi yawan mata ba su tashi ado da sa kaya masu dauke hankali sai za su fita unguwa. Wannan mummunan dabi’a ne da yake yada alfasha a bayan kasa.

 

-Mace ta zamo mai tsoron Allah ta yadda za ta kaunaci rahaman Allah a lahira maimakon bin tafarkin bokanci ko sihiri don a mallake miji ko korar kishiya. Zuwa wurin boka tare da gaskata shi masiba ce mai tsanani da ke halakar da mai yi.

 

‘Yan’uwa mata ku nisanci bin wannan kazamar hanya mai tabarwa na bin bokaye don gujewa azabar Allah da kwadayin rahamarsa. Hakuri da biyayya da kyautatawa da soyayya da tsafta da agazawa da sauran dabi’u masu kyau suke kawo zaman lafiya tsakanin ma’aurata ko kishiyoyi ba shaidanin boka ba. Domin haka ya kamata mata su kula da wadannan abubuwa wajen samun zamantakwar aure mai daurewa a cikin rayuwa. Idan aka rige wadannan abubuwa, to za a sami karancin rabuwar aure. Allah ya sa mu dace.

Exit mobile version