Connect with us

SIYASA

Dawo Da Martabar Talaka Ce Mafita A Kasar Nan, inji Umar Faruk

Published

on

Matashin dan siyasa kuma dan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Katsina, a karkashin tutar jam’iyya NARP, Honarabul Umar Faruk Yakubu ya ce, dawo martabar Talaka a kasar nan ita ce mafita, duba da yadda ake mayar da talakawan saniyar ware bayan an kammala zabe kowa ya dare kujerarsa. Barista Umar Faruk ya bayyana haka a hirarsu da wakilinmu, Rabiu Ali Indabawa ga yadda hirar ta kasance.

Masu karatu za su so saninka a takaice.

To a takaice sunana Umar Faruk Yakubu, kamar yadda a baya na fada, an haife ni a bakin Korau Kofar Bai cikin jihar Katsina, ranar 19 ga watan Satumbar shekarar 1983. Na yi karatu mai zurfi a kan koyon aikin Lauya, kuma a yanzu ina aiki a Abuja, abinda ya sa na takaice, saboda idan masu karatu na biye da wannan jarida sun san irin gwagwarmayar da na yi bayani akan karatuna har kawo wannan lokaci, tunda dama ka ce a takaice.

Ya kake kallon matsayin talakawan kasar nan a hannun masu mulki?

To a hakikanin gaskiya halin da talakawa ke tsintar kansu a hannun masu mulki, abu ne bai dace a halayyar dan Adam ace a kasa kamar Nijeriya ana samunsa ba. Bai dace talakan da kullum da shi ake amfani wurin cin zabe kuma ya zama koma baya ba. Kuma babban abin bakin cikin shi ne, za a zo ana ta yin rantsuwa akan abinda an san ba zai yiwu ba, ka ga yin haka ba dattaku ba ne. To ka san za ka ga masu mulki suna amfani da su kamar yadda na fada a baya don cimma manufarsu, in sha Allahu za mu dawo da martabar talakawa, domin dawo da martabar talaka ita ce kadai mafita a kasar nan. Mu ‘ya’yan talakawan ne, kuma mun shiga siyasa muna tunanin za mu bayar da gudunmawarmu, masu mulkin suna ji suna gani za su hakura, tunda kundin tsarin mulkin kasa ya ba wa kowa dama a kan haka. To bisa ga haka zai zamo kamar mun jawo hankalin talakawa su sani cewa, duk fa in da za a je a dawo da su ake zuwa ake dawowa, sanna kuma su sani su ne kashin bayan Dimokuradiyya, kuma a wannan matakin ne  wadanda suke ganin ba za su iya komai a kasa, za su san ashe su ma akwai gudunmawar da za su iya bayar wa a kasar.

Kuma kazalika idan Allah ya cika mana muradinmu, za mu zaburar da bangaren zartarwa domin a rika kaddamar da dokokin abubuwan da aka gabatar a majalisa ta hanyoyin da za su kawo cigaba ga kasa, to in sha Allahu ba abu ne na fariya ba, abubuwan da muka yi baya na zaburar da matasa cewa su ta shi su nemi na kansu, to har ila yau za mu tabbatar da cewa duk abubuwan da za a zartar su kasance masu alfanu ne ga al’umma gabaki daya. bisa ga wannan ne in sha Allahu muka shiga siyasa, kuma muke ganin za mu ba da muhimmiyar gudunmawa da za ta kawo wa kasarmu cigaba, musamman kuma al’ummar jihar Katsina ta Tsakiya.

wannan takara da ka fito a wane matsayi ka fito?

Na fito ina neman takarar dan majalisa a karamar hukumar jihar katsina wato Katsina ta tsakiya.

ka fadi kadan daga ayyukan da kuke sa ran gabatarwa in kun yi nasara, ya kake ganin karbuwar jam’iyyarku ga jama’a?

To Alhamdulillahi, batun samun jam’iyya ai dama ba wai daga kafa ta take samun karbuwa ba, mutane ne su ke shiga cikin jam’iyyar sai ta samu katbuwa, daga sai ta yi tasiri a zukatan al’umma, saboda wadanda ke cikin jam’iyyar. To Alhamdulillahi mun samu karbuwa, saboda mutane sun san mu, kuma sun dsan abubuwan da za mu iya, sun san mu mutanen kirki ne, sun san cewa da ikon Allah ain Allah ya sa muka cimma gaci za mu yi abinda ya kamata wanda zai ka wow a al’ummarmu cigaba. To shi ya sa muke ganin mun samu cigaba da karbuwa sosai, ba kamar wasu jam’iyya da za ka ga an yi musu rijistar amma kamar bas a cikin jam’iyyun da aka yi wa rijista. Amma Alhamudulillhi cikin shekara daya da aka yi wannan rijista lallai mutan Katsina musamman Katsina ta Tsakiya sun san lalli akwai wata jam’iyya ANRP, kuma wadanda ma ba su san da ita ba ma su ma za su san da ita kwanannan in sha Allahu.

To baya ga karbuwa da jam’iyyarku ta samu, kawo yanzu wane cigaba aka samu?

To Alhamdulillahi an samu cigaba a bangarori daban-daban, mun samu jajitattun matasa da suka fito suka ce su ma za su fito su tsaya a wannan jam’iayya tamu, kuma mun samu wasu mutane sun fito takara ko da yake su ba a wannan jam’iyyar ba ne, kuma mun samu wasu matasa da suke ganin tunda mun fito su ma mai zai hana su fito a wata jam’iyyar? To wannan shi ma gudunmawa ce a siyasance, kuma Alhamdulillahi ba fariya ba fitowar mu ta zaburar da matasa lallai su fito su ba da ta su gudunmawar.

Ko wace jam’iayya tana jagororinta, wasu a masu mulkin kasa wasu kuma a fannoni na ilimi, shi ku ma kuna da irin wadannan jagororin?

Ai manyan nan dai mu ne, to mu raina mu ka yi? Ai mu ne manyan nan na jam’iayyar, kuma shi yaro ai da sannu yake girma, kuma ba wani wanda komai isarsa da yake da izza, yake tunanin a lokaci guda ya samu izzar nan, da sannu a hankali Allah ya sa ya zama wani abu. To da ake cewa jam’iyya sai wane da wane to mu ne wane da wanen a tamu jam’iyya.

To tunda ka ce jam’iyyarku ta matasa ce, wane irin shiri kuka tanadar wa matasan idan Allah ya ba ku dama?

Alhamdulillahi shirin da muka tanadarwa matasa suna da dama, kamar yadda zan iya zayyana maka shi ne, misali muna da mazabu 15 a karamar hukumar Katsina, muna rumfunan zabe 481, kuma muna da wakilanmu a wadannan mazabu da da rumfunan zabe wadanda da su za mu yi amfani yayin zabe. Sannan akwai kamar cibiyar hadaka da zamu bude domin su zaga suna jin me al’umma suke bukata, ba wai mu abinda muke so ba, a a abinda su mutane ke bukata wanda zai kawo musu cigaba.

Sai kuma maganar zamana kashe wanda, mun san dai gwamnati ba ta iyayin komai ba, amma muna sa rai gudunmawar da za mu bayar da tallafin jari ga matasa, wanda za mu samar da kungiya-kungiya wadda a ko wacce za a samu kamar mutum 50 wadanda za a ba su jari ne na sana’o’in hannu. Ba wai dole ne a ce sai gwamnati ta bayar da jari ba, amma dai ya zama an yi hadaka tsakanin gwamnati da mutanen gari ya zamana su ma mutanen garin sun shirya sun tanadar wa kansu sana’a ta hannu, wadda wasu za ka ga ba su da hali, wani za ka ga dubu 20 kacal sai ka ga ta sauya masa rayuwa, mutanenmu suna nan bila adadin, wato matsalar shi ne raina wa muke, to da sannu in Allah ya sa muka cimma gaci, za mu yi wa wadannan matasa abinda muke ganin ko yaya ne dai za su iya rike kansu, ko a gwamnatance, ko kuma ta aljihunmu in sha Allahu.

Jam’iyyarku sabuwa ce, ya kake kallon kwarin jam’iyyar wajen karo da su APC da PDP, a daya bangaren kuma ga irinsu Labour Party?

Ai mu yanzu lokaci kawai muke jira kawai a rantsar da mu mun ci zabe in sha Allahu, abinda amanna da shi shi ne, mun sani Allah ne ke ba da mulki, don haka mu a shirye muke, domin ba mu dogara ga kowa wajen bayar da muliki ko hanawa ba sai Allah. Amma dai ina mai tabbatar maka da cewa, ashirye muke da mu bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen maido da martabar talaka a kasar nan, tare da wayar da kansa ya san shi mutum ne mai ‘yanci, ba wai kawai a yi amfani da shi wajen yin zabe bayan an ci kuma a mayar da shi saniyar ware ba.

To mun gode.

 

Ni ma na gode.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: