Dawo Da Martabar Tutar Nijeriya

Tutar

Kamar yadda lamarin yake a kusan dukkan kasashen duniya, Tutar kasa tamkar kudin kasar take ko kuma taken kasa, wata alami ne mai muhimmancin gaske da ke alamta tsayuwar kasar. Tuta na da kala da wasu alamomi masu ma’ana da ke zaburar da kishin kasa da al’ummar kasa ke alfahari da su. Takardar kudi na dauke da nauyin tattalin arzikin kasa kamar yadda kalmomin da ke cikin taken kasa ke  tayar da tsimin kishin kasa.

Haka yakamata abin ya kasance a Nijeriya, yadda ‘yan Nijeriya ke kallon tutar kasa, wannan shi ne yake  kunshe a ra’ayinmu na wannan makon. Michael Taiwo Akinkumi ne ya tsara tutar Nijeriya a shekarar 1959 aka kuma amince da ita a ranar 1 ga Oktobar 1960, tana bayyana wasu muhimman abubuwan da ke tattare ne da kasarmu Nijeriya.

Duk da muhimmancin tutar ga kasancewa alami da ke nuna tsayuwar Nijeriya a matsayin kasa daya, da kalolin nan nata na Kore da Fari da Kore, tutar ta fuskanci gwagwarmaya a lokuta daban daban. Baya ga sauko da ita da aka yi tsibirin Bakassi lokacin da Kamaru ta karbi mallakin yankin a watan Agusta na shekarar 2008 (sakamakon yarjejeniyar ‘Green Tree Agreement’), kalolin kore da farin cikin tutar sun fuskanci matsaloli daga kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram, inda suka tunbuke tutar suka kuma dora nasu a wasu yankin Arewa maso Gabas kafin sojojin Nijeriya su tarwatsa su. Haka kuma kungiyoyi masu neman ballewa daga Nijeriya na tozarta tutar Nijeriya don biyan bukatun su na neman kafa kasarsu.

Ire-iren wadannan kungiyoyin, wadanda ya kamata su san muhimmancin mutunta tutar kasa amma suke wulakanta ta kamar yadda suke wulakanta kudin Nijeriya (Naira). Sun gwammace su yi ado da alamomin tutar wata kasa suna kuma ajiye dukiyarsu da kudin wata kasa ba Naira ba, wannan halayyar yake kara taimakawa wajen karya darajar Nairar a ciki da kasashen wajen Nijeriya.

A ra’ayinmu, wadannan na daga cikin matsalolin da ke fuskantar kasancewar Nijeriya dunkulalliya da kuma yadda ake muhimmantar da kalar kore da fari da turar Nijeriya ke dauke da su.

Haka kuma akwai wasu hanyoyi da dama da al’umma Nijeriya ke bi wajen wulakanta tutar Nijeriya, wandanda yakamata su san muhimmancin tutar, musamman ‘yan siyasarmu.

Muna kara nuni da yadda akan lillika tutar Nijeriya a tituna inda za a yi wani buki amma kafin wani lokaci sai ka ga ana shafa wa tutar datti ko kuma ka ga ana yagawa, ba tare da damuwa da matsayin tutar ba, wannan wani abu ne da ya yi kamari a lokacin mulkin sojoji. Fiye da kasance alami na kishin kasa, ana karrama shugaban sojoji kamar wasu alamin kishin kasa, har ta kai ga ana kwatanta su da kasancewa wasu ginshikai a rayuwar kasa.

A yau, mutum zai lura da tutar Nijeriya a wurare kamar gidajen gwamnati, heikwatar kananan hukumomi, makarantu da ma’aikata masu zaman kansu, wannan abu ne mai kyau, amma abin haushin shi ne yadda zaka ga tutar ta yage ko ta yi dakandakan babu wanki tamkar bola kamar wadanda suka sa ba su san muhimmacinta ba.

Ya kamata a fahimci cewa, ba wai muna fada da sanya tutar Nijeriya a kan motoci ko kuma masu yin rigar sawa da ita ba ne, amma ra’ayin wannan jaridar ita ce, dole a mutunta tutar da kuma bata girmarda ya kamata.

A kasashe irin su Amurka, babban laifi ne da za a iya hukuncin kisa lalata tutar kasa, ana kallon tutar a matsayin alami na mulki da mutuncin kasa, ana sa ran Ba’amurke ya tsayu wajen kare martabar tutar Amurka ko da zai rasa ransa ne kuwa.

A lokuttan baya ana koyar da ma’ana da muhimancin tutar Nijeriya ga yara a makaratu. Amma a yau abin takaici shi ne kokarin koya wa yara masu tasowa muhimancin alamomin kasa ya shiga rudu, an mayar da wannan koma baya, yara masu tasowa ba su san cikkaken ma’ana da muhimancin tutar Nijeriya ba.

Muna tsoron halin da tutar Nijeriya za ta fada a nan gaba, a kan haka muke kira ga Majalisar Kasa da ta samar da dokar da za ta martaba da muhimmantar da alamomin kasa, ciki har da tutar kasa. Wannan na da matukar muhimmanci don tabbatar da yara masu tasowa sun tsayu da kishin kasa tare da mutunta alamomin kasa.

Exit mobile version