Dawowar Abdussalam Abdulkareem APC Babbar Nasarar Jam’iyyar Ce A Kano – Nazifi Sharif  

APC

Daga Isah Ahmed,

Fitatcen mawakin Jam’iyyar APC nan na kasa, da ke Kano Nazifi Sharif, ya bayyana cewa babu shakka dawowar da matashin nan Alhaji Abdussalam Abdulkareem ya yi zuwa jam’iyyar APC daga Jam’iyyar GPN, wata babbar nasara ce ga jam’iyyar da al’ummar Jihar Kano bakidaya.

Mawaki Nazifi Sharif ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

 

Ya ce Abdussalam Abdulkareem mutum ne  mai kaunar matasa,  kuma an  ga irin kokarin da yake yiwa  al’ummar Jihar Kano da kasa baki daya.

 

Ya ce ya yi abubuwan alheri da yawa musamman gina matasa, ta hanyar basu tallafi da samar masu ayyuka a wurare daban daban, a Jihar Kano da Kasa baki daya.

 

“A kullum maganganunsa  kan cigaban Jihar Kano da kasa baki daya ne.  Don haka muka fito domin mu nunawa   al’ummar Jihar Kano shi,  su gane wane ne shi, su bashi goyan baya. Domin idan aka  bashi dama ya zama gwamnan Jihar Kano, karkashin jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2023,  zai kawowa al’umma Jihar gagarumin  cigaba.  Don haka muna  kira ga al’ummar Jihar Kano, su marawa wannan matashi baya, domin ya kai ga kujerar gwamnan jihar Kano. Domin yana da manufofi  da za su zamo al’heri ga al’ummar Jihar Kano’’

Exit mobile version