Dawowar Hazard Za Ta Taimaka Mana, Cewar Zidane

Hazard

Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasa Eden Hazard ya fara buga wa Real Madrid wasa a bana ranar Talata a wasan da ta tashi 2-2 a gidan kungiyar Borussia Monchengladbach ta kasar Jamus a Gasar cin kofin zakarun turai na Champions League.

Tun kafin hutu Borussia Monchengladbach ta ci kwallo biyu, bayan da aka kusan tashi ne Real Madrid ta farke ta hannun ‘yan wasanninta guda biyu da suka hada da Karim Benzema da Casemiro.

Real Madrid din wacce ta yi rashin nasara a gida da ci 3-2 a hannun Shakhtar Donesk tana da maki daya a wasa biyu da ta buga a bana kuma wannan ne karon farko da dan kwallon tawagar Belgium din ya fara buga wa Real Madrid wasa a shekarar nan, sakamakon jinya da ya yi ta faman yi.

Dan wasan ya yi fama da jinya tun komawarsa Spaniya da buga wasa, inda ya yi wa Real Madrid wasanni 22 kacal a kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 kuma cikin wadanda ke jinya a Real Madrid kawo yanzu sun hada da Dani Carbajal da Albaro Odriozola da Nacho da Martin Odegaard da kuma Mariano.

Wasan ranar Talata shi ne wasa na uku da kungiyoyin suka fafata a Gasar ta Zakarun Turai, bayan da suka tashi 2-2 a gidan Real Madrid a ranar uku ga watan Maris a shekarar 1976 sannan a karawa ta biyu kuwa ranar 17 ga watan Maris a Borussia Mönchengladbach tashi suka yi 1-1.

Karawa tsakanin Real Madrid da Borussia Mönchengladbach a gasar:

Laraba 3 ga watan Maris 1976 EUROPEAN CUP

B M’gladbach 2 – 2 Real Madrid

Laraba 17 ga watan Maris 1976 EUROPEAN CUP

Real Madrid 1 – 1 B M’gladbach

Wasanni biyar nan gaba da Real Madrid za ta fafata:

Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga

Real Madrid da Huesca

Talata 3 ga watan Nuwamba Champions League

Real Madrid da Inter

Lahadi 8 ga watan Nuwamba La Liga

Balencia da Real Madrid

Lahadi 22 ga watan Nuwamba La Liga

Billarrea da Real Madrid

Laraba 25 ga Nuwamba Champions League

Inter da Real Madrid

Exit mobile version