CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Dawowar Tsagin Sauka Na Tauraron Chenge-5 Babbar Nasara Ce Da Duniyar Kimiyya

by CRI Hausa
December 17, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Dawowar Tsagin Sauka Na Tauraron Chenge-5 Babbar Nasara Ce Da Duniyar Kimiyya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ga duk mai bibiyar labarai masu nasaba da irin ci gaban da bil Adama ke samu a fannin binciken kimiyya da fasaha, ba zai kasa jin labari mai faran ta rai, na dawowar tsagin sauka na tauraron dan Adam samfurin Chenge-5 da kasar ta harba zuwa duniyar wata a karshen watan Nuwamba ba.

Ko da yake ba wannan ne karon farko da wani tauraron dan Adam ya taba gudanar da aiki debo samfuran sinadarai daga duniyar wata ba, amma masana kimiyyar sama jannati sun ce, ayyukan da Chenge-5 ya yi a wannan karon a duniyar wata suna da sarkakiya, sun kuma shafi tattaron samfuri daga duniyar wata, ta saukowa da su nan duniyar bil Adama, da ma wasu karin ayyuka masu nasaba da hakan.
Hakika Chenge-5 ya kafa tarihi a kasar Sin da duniya baki daya, a fannin nazarin sararin samaniya. Ya zamo wata gada ta sada binciken da aka jima ana yi, da wanda za a yi a nan gaba. Zai kuma baiwa masana yan samajannati karfin gwiwar ci gaba da bincike, da dorawa inda aka tsaya, karkashin manufar kasar Sin ta kafa tashar binciken samaniya mallakin kan ta.
Tuni dai shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jinjinawa wannan aiki, tare da fatan alheri ga daukacin maaikata da suka ba da gudummawar kammalar sa cikin nasara.
A hannu guda kuma, laakari da wannan nasara, kasar Sin ta nunawa duniya irin jajircewar ta, wajen cimma manyan nasarori daga dukkanin fannoni. A wannan gaba da duniya ke fuskantar wahalhalu da kalubale, kuma masana ke kara yayata bukatar komawa ga matakan kimiyya da fasaha wajen warware matsaloli, Sin ta nuna himmar ta a wannan bangare.
Ana sa ran sinadarai da sundukin dawowa na Chenge-5 ya zo da su, za su kara haskawa masu bincike yanayin kasa, da sinadarai, da ma tarihin duniyar wata, wanda ilimi ne da duniya ta dade tana kishirwar sa.
Ko shakka ba bu, Bahaushe kan ce “yabon gwani ya zama dole”, kammalar aikin Chang’e-5 zai dade yana tunawa duniyar bil Adama, irin rawar gani da Sin ta kara wajen fadada binciken duniyoyin dake kewaye da duniyar bil Adama, ciki har da duniyar wata, da ma daukacin sassan ayyukan samajannati.(Saminu Alhassan)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

A Hakika Dai Matan Kasar Sin Na Taka Rawa Sosai Wajen Yaki Da Talauci

Next Post

Sin Za Ta Raba Wani Bangare Na Samfuran Da Ta Debo Daga Duniyar Wata Tare Da Masana Kimiya Na Sauran Kasashe

RelatedPosts

Rayukan Amurkawa

Rayukan Amurkawa Na Fuskantar Babbar Barazana Sakamakon Tsarin Kiwon Lafiyar Kasar

by CRI Hausa
22 hours ago
0

A lokacin da cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba...

Allurar Rigakafin COVID-19

Samar Da Allurar Rigakafin COVID-19 Cikin Adalci Zai Taimaka Wa Afirka Wajen Yakar Annobar

by CRI Hausa
22 hours ago
0

Bisa labarin da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Tarayyar Najeriya wato...

Shugaban Kasar Turkiyya

An Yi Wa Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Allurar Riga-Kafin Cutar COVID-19 Kirar Kasar Sin

by CRI Hausa
22 hours ago
0

An yiwa mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay allurar riga-kafin...

Next Post
Sin Za Ta Raba Wani Bangare Na Samfuran Da Ta Debo Daga Duniyar Wata Tare Da Masana Kimiya Na Sauran Kasashe

Sin Za Ta Raba Wani Bangare Na Samfuran Da Ta Debo Daga Duniyar Wata Tare Da Masana Kimiya Na Sauran Kasashe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version