Dawowar ‘Yan Bindiga: Gaskiyar Magana Kan Garuruwa Mafi Hadari A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja – Danmajen Jere

'Yan Bindiga

 

To ina alakarsu? A kan hanyarsa ce abin da ya faru, ya faru, kuma abu ne da ya shafi gona ba garkuwa da mutane ba. Wadanda suka yi aika-aikar mutane ne da aka san su da garinsu, da kauyensu, yanzu haka ma Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta sa an kama su, suna hannun jami’an tsaro.”

 

Daga Bello Hamza da Rabi’u Ali Indabawa,

 

Babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ita ce babbar mahadar yankin kudancin Nijeriya da arewacinta. Hanyar na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’ummar Nijeriya da tattalin arzikinsu. Hakan ya sa duk wata matsala da ta shafi hanyar, takan shafi kusan dukkan kasar ne bakidaya.

Yadda ayyukan ta’addanci suke kara karuwa a kan hanyar yana matukar tayar da hankulan direbobi da al’ummar da ke zirga zirga a kan hanyar a kullum. A halin yanzu fargabar gamuwa da ‘yan garkuwa da mutane da barayi ‘yan fashi ta cika zukatan matafiya a duk lokacin da aka kusa da yankin da wannan aika-aika ke faruwa

A cikin wannan shekarar kawai, an sace mutane da dama a hare-haren da suka kai, cikin wadanda aka sace sun hada da Sarkin Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru da aka sace gab da shiga garin Katari. Bayan daukar lokaci mai tsawo ba a ji duriyar ‘yan ta’addan ba a hanyar, sai gashi a ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba 2021, daidai lokacin da al’umma suka fara kwantar da hankulansu a kan cewa, masu garkuwa sun kaurace wa hanyar sun kai hari da misalin karfe 4 na yamma inda suka hallaka Alhaji Sagir Hamidu, tsohon dan takara gwamnan a Jihar Zamfara, suka kuma yi awon  gaba da mutane da dama, haka kuma sun sake dawowa washe gari, Litinin 22 ga watan Nuwamban inda suka kwashi mutane da ba a kai ga tantance yawansu ba.

Daya daga cikin direbobi da ke zirga-zirga a hanyar a kusan kullum, Maikudi Tanko Zariya, direban Sharon ya bayyana wa waklinmu cewa, ‘Ya kamata gwamnati ta dauki lamarin tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna da matuka muhimmanci, don hanyar ita ce ta sada Arewacin Nijeriya da Kudanci, ita ce kuma ta hada yankuna Arewa da Babbar Birnin Tarayya Abuja.

“Hankalimu kan kwanta in muka ga jami’an tsaro na sintiri a kan hanyar, amma kuma sai gashi ‘yan ta’addan sun sake dawowa hanyar, wannan yana tayar mana da hankali, muna kira ga gwamnati da ta dauki tsaro a kan hanyar da matukar muhimmanci” in ji shi.

Haka kuma wani direba da ya bukaci mu sakaya sunansa, ya ce, “ya kamata a sanya ido a garurunwa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna don daga dukkan alamu batagari na boyewa a wasu kauyuka suna aiwatar da mugun aikinsu, ya kuma nemi mutane a kauyukan su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri da zai kai ga bakado masu aikata ta’asar, “Don sai da hadin kan al’umma za a samu nasara a kan ‘yan ta’adda” in ji shi.

Har ila yau, wasu matafiyan da waklinmu ya tattauana da su, sun nuna rashin jin dadinsu a kan yadda matsalar tsaro ta kara tabarbarewa a hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka nemi jami’an tsaro su kara kaimi na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar masu zirga-zirga a kan hanyar, musamman ganin muhimancinta ga rayuwa da tattalin arzikin mutane Nijeriya gaba daya.

 

Dangane da matakin dakile wannan sabuwar matsala, rundunar ‘yansanda ta sanar da samar da Tankar Yaki guda 2 don fattakar ‘yan ta’adda a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun kuma kara yawan jami’an tsaron dake sintiri a kan hanyar.

Tabbas jami’an tsaro na kokarinsu amma akwai bukatar su kara kaimi don tabbatar da tsaro a kan hanyar.

A nata martanin, Kungiyar Tuntuba ta Arewa, (ACF) ta bayyana hare-hare da garkuwa da mutane da ake yi a kan babar hanyar Abuja zuwa Kaduna da cewa, abin kunya ne da takaici ga Nijeriya kuma ba abin da za a amince dashi ba ne.

Jami’in yada labarai na kungiyar, Mr. Emmanuel Yawe, ya bayyana haka a yayin da yake Allah wadai da kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa Alhaji Hamida Sagir, tsohon ma’aikacin Hukumar Raya Babbar Birnin Tarayya Abuja, kuma tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara, da aka kashe ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Kungiyar ta bayyana cewa, ana cutar da al’umma a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a kullum kuma daga dukkan alamu gwamnatin Kaduna da Gwamnatin tarayya sun kasa tabuka komai, kamar abin ya fi karfinsu.

Sanarwa ta kuma ce, “Hankalin ACF ya tashi a kan ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a kullum duk da muhimmancin hanyar a zirga-zirga tsakanin Babban Birnin Tarayya Abuja da yankunan Arewacin Nijeriya”.

“Wannan wani babban kalubale ne ga jami’an tsaro, ya kuma zama dole su kawo karshe lamarin, sannan ya kamata su gano daidai inda aka fi aikata wannan ta’asar don su dakile ayyukan ‘yan ta’addan,” in ji kungiyar.

Kungiyar ta kuma nemi gwamnatin tarayya da ta Jihar Kaduna su ceto al’umma daga tashin hankalin da suke fuskanta a wannan hanyar.

Wannan lamari dai na dawowar ‘yan bindiga masu sace mutane suna garkuwa da su ya yi matukar tayar da hankulan ‘Yan Nijeriya musamman ‘yan arewa da suka fi yawan amfani da hanyar.

Abin da ya faru na kwashe matafiya zuwa cikin daji a tsakanin Rijana da Katari, a wani kaulin kuma Gidan Busa, a farkon makon nan baya ga kisan tsohon dantakarar gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Sagir Hamidu ya haifar da tunani daban-daban da tofa albarkacin bakin ‘yan kasa a kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance matsalar wacce ta zama kamar cin kwan makauniya.

Daga cikin masu ruwa da tsaki a garin Jere, daya daga cikin manyan garuruwan da ke hanyar da matsalar ke aukuwa, Danmajen Jere, Bashir Isah ya warware zare da abawa kan wani rahoto da wata kafar yada labaru ta yi a kan wasu garuruwa uku da suka kasance mafiya hadari a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Ya yi bayanin ne a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa ta wayar tarho. Inda ya fara da zancen yadda aka kasafta garuruwan akwai kuskure a ciki.

“Akwai wani rahoto da BBC Hausa ya fitar a kan garurwa uku da aka fi sace mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Cikin garuruwan nan uku, ta fadi Katari, Jere, sannan suka fadi Rijana. To abin da suka fada a kan Jere babu gaskiya kwata-kwata, hasali ma inda suka ce garin Jere mai nisan kilomita 117.4 kafin zuwa Kaduna ba gaskiya ba ne, domin daga Jere zuwa Kaduna tafiyar kilomita 105 ce.

“Sannan kuma rahoton ya kuma fadi cewa abubuwan da yake faruwa na hadari da ake yi tsakanin Katari daidai yake da Jere saboda kusa suke, to tsakanin Jere da Katari akwai kauyuka, kauyukan nan za su kai biyar. Akwai Bakin Gada, akwai Unguwar Jibo, akwai Nasarawa, Azara, sannan ka yi maganar Bishini, ka ji kauyuka guda biyar kenan.”

A cewar Danmajen Jere, abin da aka fada na sace mutane a Jere cikin watan Mayu kwata-kwata bai faru ba, “Na farko da mai rahoton ya ce a watan Mayun wannan shekara, wadannan mutane suka tare hanya suka rika kama matafiya a garin Jere da misalin karfe hudu na yamma, to ba mu taba jin an yi hakan a garin Jere ba, kuma wannan batanci ne.

“Sannan ya alakanta abin da yake faruwa yanzu da wani al’amari da ya samu Sarkin Jere a 2014, wanda kwata-kwata abubuwa ne biyu da suka yi hannun riga. Ba ‘yan bindiga ne suka yi wa Sarki abin da aka yi masa ba, Gwari ne makotanmu da suka yi rigimar gona tsakaninsu da shi, gonarsa ce ya saya, suka ce sam tasu ce har kotu suka je Sarki (Allah ya gafarta masa) ya yi nasara. Ranar wata Juma’a bayan zaman fada, sarki zai tafi Abuja ta hanyar Bwari, in ka bar Jere za ka nufi Bwari ba nan hanyar Kaduna zuwa Abuja take ba, hanyoyi ne daban-daban. Ta Kaduna zuwa Abuja tana yamma, ita kuma ta zuwa Bwari tana gabas. To ina alakarsu? A kan hanyarsa ce abin da ya faru, ya faru, kuma abu ne da ya shafi gona ba garkuwa da mutane ba. Wadanda suka yi aika-aikar mutane ne da aka san su da garinsu, da kauyensu, yanzu haka ma Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta sa an kama su, a yanzu haka ma suna hannun jami’an tsaro. To me ya alakanta wannan da za a zo a sako shi cikin wannan rahoton. Wannan labari ne na batanci, ba za mu lamunta ba, ya zama wajibi wannan majiya ta janye wannan kalamin domin batanci ne ga mutanen Jere masu zaman lafiya.”

Da aka tambaye shi game da abubuwan da tsohon Sanata Shehu Sani ke fada a kan garin na Jere da ke alakanta ta’asar ‘yan bindiga garin, Bashir Isah ya ce, “Sanata Shehu Sani, ai ya wallafa labarin a shafinsa na sa da zumunta, kuma kowa ya san Sanata Shehu Sani, dan gwagwarmaya ne ba mu san wa ya kira shi ba, babu wanda ya sani, ko a’a yana neman suna ne ko menene mu ba mu sani ba. Amma ya ce an kira shi gaban jama’a an tare mutane, da ma cewa ya yi a hanya misali, tun da mun san akwai jeji, jejin nan kuma in ka yi maganar Katari sai ka wuce can wajen Rijana wanda za ka yi tafiya har sai ka shiga Zamfara, ka shiga Neja, ka fita ka shiga Kaduna, kuma nan ne duk mattarar wadannan ‘yan ta’addar kowa ya sani, in an koro su daga Zamfara su zo nan, in sun kare abin da suke yi su koma can, haka suke yi cikin dajin.

“Kuma kowa ya san kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, tun da (‘yan bindigar) daukar mutane suke suna karbar kudin fansa, sun san dai cewa Abuja dai garin manyan mutane ne, to harinsu na manyan mutane ne, amma a ce a garin Jere, wannan munafunci ne, ai mu ma an dauke mana mutane, a kwai yara guda biyu da aka taba dauke mana sai da muka biya kudi muka karbo su.”

Da aka tambaye shi a ina aka dauke musu yaran nasu, ya ce “Sun shigo mota ne a Abuja ‘Junction’ daga Kaduna zuwa Jere, ana zuwa nan gaba kusa da Rijana, nan aka farmake su aka debi mutane da yawa, yaran sun zo har gidana suna bani labarin abin da ya faru. Wannan labari ba gaskiya ba ne, ya kamata wannan kafa ta janye kalamanta kuma su yi gyara, maganar Sarkin Jere ba na ‘yan bindiga ba ne, kodayake wadanda suka yi aika-aikar sun yi ta’addacin da manufarsu sun sassare shi sun nemi rayuwarsa da manufarsu, amma ba wadannan ba ne da suke fita daji su sace jama’a su karbi kudin fansa ba.”

Wakazalika, da yake karin bayani a kan ko nuna masu garkuwa ga ‘yan jarida da jami’an tsaro ke yi a garin na Jere ya sa ake alakanta garin da su? Ya ce, “Ai Jere babban gari ne da ke kan hanyar Abuja, kuma Jere na da ‘Area Command’ na ‘yansanda da ke kula da shiyyoyi shida, shi ya sa idan aka yi kamu sukan baje kolinsu a nan, tun da a nan babban jami’in da ke kula da wannan shiyya yake… amma ba ‘yan Jere ba ne kuma babu abin da ya hada su da Jere. A karshe muna kira ga masu yin wannan abin, su ji tsoron Allah su tausaya wa bayin Allah, kuma muna addu’a Allah ya shirye su, Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasarmu, wannan abu babu dadi.” In ji shi

A halin yanzu kuma rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama wani gawurtaccen dan ta’adda wanda ya shahara a ayyukan ta’addanci a yankin Abuja, Nasarawa da Jihar Neja, dan ta’adda mai suna Umar Samaila dan shekara 50 ya shiga hannun ne a ranar Asabar a kauyen Buku dake Jihar Neja.

Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiudun ya bayyana haka a takardar sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Minna.

Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa, dan ta’addan yana cikin shugabannin ‘yan ta’adda a yankunan Neja Abuja da Jihar Nasarawa.

Hankalin Majalisar Wakilai Ya Tashi, Ta Kafa Kwamiti

 

 Daga Bashir Bello,  

 

Hankalin Majalisar Wakilai ya tashi game da sake tabarbarewar tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan munanan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a farkon makon nan, inda majalisar ta kafa wani kwamiti da zai rika ba da rahoton abubuwan da ke faruruwa na sha’anin lokaci-lokaci tare da yin kira ga hukumomin tsaro su gaggauta daukar matakin samar da tsaro a kan hanyar.

Bukatar hakan na kunshe a cikin wani kudiri da ya bukaci daukar matakin na dakile hare-haren da ‘yan binga da masu satar mutane domin karbar kudin fansa suka jera kwanaki suna yi a hanyar, wanda Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Awe/Doma da Keana  daga Jihar Nasarawa, Abubakar Hassan Nalaraba ya gabatar a zaman majalisar na ranar larabar nan.

Da yake gabatar da kudirin Hon. Abubakar Hassan Nalaraba ya ce abin takaici ne yadda ‘yan bindiga suka jera kwanaki suna kai hari a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, lamarin da ya yi sanadiyyar garkuwa da mutane da yawa tare da hasarar rayuka, ciki kuwa har da wani tsohon dantakara Gwamnan jihar Zamfara, Sagir Hamidu.

Ya ce duk da irin matakan da majalisar dokoki ke dauka a game da rashin tsaro dake addabar babbar hanyar da ta hada yakin Arewa da kudancin Nijeriya, amma hare haren sai karuwa suke a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Ya ce rahotanni sun nuni da cewa garin Rijana dake kan hanyar yana zama matattarar ‘yan bindiga da masu satar mutane domin karbar kudin fansa  sannan, ‘yan bindiga da suka sauya sheka daga wasu wurare suna zuwa garin, lamarin dake ci gaba da yin barazana ga rayukan ‘Yan Nijeriya.

Da take amincewa da kudirin, Majalisa ta bukaci hukumomin tsaro da su dauki dukkan matakan da suka wajaba domin tabbatar da tsaro a kan hanyar don amfanin duka ‘Yan Nijeriya.

Kana ta bukaci kwamitocin ta na tsaro da su rika gabatar wa majalisar rahoto na wata-wata da Kuma wattanni uku-uku a game da halin da tsaron kasa yake ciki, domin daukar matakan magance matsalolin tsaron.

 

Exit mobile version