Khalid Idris Doya" />

DCCN Ta Kalubanci Kudurin Kafa Dokar Daidaito Jinsin Mace Da Na-Miji

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Kungiyar Da’awah a Nijeriya mai suna ‘Da’awah Coordination Council of Nigeria’ wacce take da kungiyoyin Da’awa sama da 54 a karkashinta, ta bukaci Sanatocin Nijeriya da su yi watsi gami da yin fatali da kudurin nan da wani sanata ya gabatar na bukatar a daidaita jinsin mace da na miji a Nijeriya ya zama doka.

DCCN ta bayyana wannan bukatar nata ne a cikin wata takardar manema labaru da suka raba a Bauchi dauke da sanya hanun Sakatare Janaral na kungiyar Engr. Ahmad M Y Jumba ya bayyana cewar kai tsaye wannan kudurin zai shafi addini da al’adar wasu bangaren jama’a.

Ta cikin sanarwar “Kai tsaye muna kalubalantar kudurin da yake gaban majalisa na batun daidaita jinsin maza da mata; gaskiyar magana kai tsaye wannan kudurin yana kalubalantar addininmu da kuma al’adarmu,” In ji Jumba.

Don haka ne kungiyar ta bukaci Sanataci da su yi watsi da batun kwata-kwata, domin hakan ba zai kawo wa Nijeriya wani alfanu ba.

Baya ga nan kuma, DCCN ta yi kira da babban murya ga gwamnatin tarraya da ta shiga cikin lamarin makarantu masu sanya dokar hana sanya Hijabi da sauran bangarorin da suke da irin wannan tunanin “Dole ne a bayar da daman a doka mata suke sanya hijabi a makarantu da sauran wurare a Nijeriya domin hijabi na daga cikin musulunci,”

Baya ga nan kuma, Kungiyar Da’awa ta kasar ta kuma yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su samar da mafita mai daurewa dangane da matsalolin tsaro da suke fuskantar Nijeriya hade kuma da lalubo hanyoyin magance mummunar dabi’ar ‘yan siyasa na ramakon gayya wacce hakan bai haifar wa Nijeriya da ma ido a cewar kungiyar.

 

Exit mobile version