Connect with us

WASANNI

De Bruyne Zai Dawo Daga Ciwo A Ranar Wasan Manchester United

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Kebin De Bruyne zai dawo buga wasa kungiyar bayan yaje doguwar jinya a ranar da kungiyar Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester United.

De Bruyne dai yaji wani mummunan rauni ne a lokacin daukar horon kungiyar a mako na biyu na fara gasar firimiya hakan yasa dole sai da aka yi masa aiki kuma bazai buga wasanni ba da dama da kungiyar za ta buga nan gaba.

Sai dai anyi zaton ciwon zai dauki tsawon lokaci bai warke ba amma rahotanni sun bayyana cewa an hango dan wasan ya cire robar da aka rufe masa inda aka yi masa tiyata hakan yana nufin dan wasan zai dawo daga jinya akan lokaci.

Ana ganin dan wasan zai dawo hutu gabanin wasan da kungiyar za ta karbi bakuncin abokiyar hamayyarta wato Manchester United a wasan da zasu fafata a ranar 11 ga watan Nuwanban shekarar nan.

Dan wasan, mai shekaru 27 da kasar Belgium ya zura kwallaye 8 sannan kuma ya taimaka kungiyarsa ta zura kwallaye 16 a kakar data gabata inda kungiyar ta Manchester City ta lashe kofin firimiya da maki dari.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: