Abba Ibrahim Wada" />

De Gea Zai Cigaba Da Zama A Manchester United

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa sabanin rahotannin da ake ya dawa cewa mai tsaron raga David De Gea zai bar kungiyar Manchester United zuwa Jubentus yanzu ya amince zai cigaba da zaman kungiyar.

Duk da cewa a kwanakin baya akwai rade radin cewa mai tsaron ragar dan kasar Sipaniya, ya kasa cimma yarjejeniya da kungiyar domin sake sabon kwantiragi yanzu an bayyana cewa Magana tayi nisa wajen sabunta cigaba da zaman kasar ta Ingila.

A farkon wannan satinne aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus zata fara tattaunawa da Manchester United kan sayan mai tsaron ragarta Dabid de Gea a watan Janairun shekara ta 2020 bayan da mai tsaron ragar yaki amincewa da sabon kwantiragin cigaba da zama.

Sai dai wasu rahotanni kuma daga kasar Ingila sun ruwaito cewa tuni Magana tayi nisa tsakanin mai tsaron ragar da shugabannin kungiyar domin ganin ya cigaba da zaman Manchester United bayan da suka amince zasu kara masa albashi mai yawa.

Sannan rahoton ya bayyana cewa De Gea, wanda tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ne zai zama yana daukar albashi irin wanda dan wasan tsakiyar kungiyar, Paul Pogba yake dauka.

De Gea ya fara tsaron ragar Manchester United ranar 23 ga watan Yunin shekara ta 2011 a wasan sada zumunta da kungiyar ta yi nasara a kan Chicago Fire da ci 3-1 haka kuma shi ne ya kama raga a wasan Community Shield a karawar hamayya tsakanin Manchester United United da Manchester City ranar 7 ga watan Agustan 2011.

Tun lokacin da De Gea ya koma Manchester United da buga wasa a shekara ta  2011, kawo yanzu ya yi wasanni sama da 300, sannan ya bayar da gagarumar gudunmawa a kungiyar haka kuma ya lashe gasar firimiya da kofin kalubale na  FA Cup da League Cup da Community Shield uku da kuma Uefa Europa League.

Exit mobile version