Dembele Zai Yi Jinyar Wata Hudu

Dan wasan da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai yi jinyar wata hudu.

Dan kwallon da Basa ta sayo daga Borrussia Dortmund kan kudi fam miliyan 135.5 ya yi rauni ne a karawar da Basalona ta ci Getafe 2-1 a gasar La Liga a ranar Asabar.

A wa ta sanarwa da Basalona ta fitar ta ce likitoci a Finland za su yi wa dan wasan na tawagar Faransa aiki a mako mai zuwa, kuma tana sa ran zai yi jinya zuwa wata uku da rabi ko hudu.

Hakan na nufin ba zai buga wa Basalona wasar rukuni gasar cin kofin Zakarun Turai ba, kuma da kyar idan zai kara a fafatawa da Real Madrid a ranar 23 ga watan Disamba.

Dembele ba zai buga wa Faransa wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Bulgaria da wanda za ta kara da Belarus a watan Oktoba ba.

Exit mobile version