Diego Costa, wanda ake yiwa kallon dan wasa wuyar sha’ani ya yi sallama da kungiyar wasa ta Chelsea zuwa ta Atletico Madrid; masoya kungiyar was an kwallo ta Chelsea ba za su taba mantawa da irin gudummawar da Costa ya bayar wurin raya kungiyar ba.
Masu fashin baki na hasashen ko za a sake samun wani dan wasa mai wuyar sha’ani irin Costa, a kungiyoyin wasannin Firimiya.
Tafiyar Costa ta harzuka magoya bayan kungiyar Chelsea, sai dai masana na cewa daga baya, dole ne magoya bayan su sauko, har ma su rika yabawa Costa bisa rawar da ya taka wurin lashe gasar Firimiya da Chelsea ta yi har sau biyu.
Ba zai yiwu a manta da tarihin Costa a kungiyar Chelsea ba, duk kuwa da yake bai kamo kafar asalin jiga-jigan kungiyar irin su Didier Drogba ba, sai dai za a tuna da irin kwallayen da ya zura a tsawon zamanshi a kungiyar. A wasanni 120 da ya buga, ya zura kwallaye 58.
Diego Costa ya samu sakon barin kungiyar Chelsea ne ta hanyar sakon wayar hannu daga shugaban kungiyar, akan cewa kungiyar Chelsea ba ta bukatarsa. Wannan kuma ya biyo bayan sabanin da aka samu a tsakanin Costa din da Kocin kungiyar, Antonio Conte a filin horo na Stamford Bridge.
Masu kallon wasannin firimiya sun isa zama shaida akan cewa Costa ya taimaka matuka a sansarorin da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu a ‘yan baya-bayan nan. Matsalarsa daya kawai ita ce ta rashin da’a da nuna isa. Har sai da ta kai ‘yan was an baya a was an Firimiya suna matukar shakkar Costa. Ba wai kawai ya iya zura kwallo a raga bane, zubinshi na firgita masu tsaron baya.
A watan Janairu ne ake sa ran komawar dan wasan, bayan an kammala duba lafiyarsa da kuma sauran tsarabe-tsarabe.
Atletico ta ce, za a duba lafiyar dan kwallon mai shekara 28 wanda ya bar kulob din ya koma Chelsea a 2014, kwanaki kadan masu zuwa.
Dan wasan, bai murza wa kulob din Chelsea leda a bana ba, ya kuma shafe watan Agusta a kasarsa ta haihuwa Brazil.
Shekara uku da ta gabata ne haifaffen Brazil din ya koma Chelsea daga Atletico a kan kudi fam miliyan 32.