Daga Sabo Ahmad da Khalid Idris Doya
A daren juma’a 7 ga Yuni, 2013, aka fara shirye-shiryen wani ƙasaitaccen buki a Caɓalli Club da ke ƙasar Dubai. Kulub ɗin wani ƙayataccen guri ne na musamman da aka keɓe, wanda aka sa masa sunan shaharren maɗinkin nan ɗan ƙasar Italiya, Roberto Caɓalli, a cikin Otal ɗin 5-star luɗury Fairmont Hotel. Akwai shahararrun masu sa kaɗe-kaɗe irin su, DJ Jimmy Jatt, da shahararrun masu wasan barkwanci irin su, Basketmouth, da mawaƙa irin su, Wizkid da rapper Naeto C. waɗanda suka fara sheƙe ayarsu tun kafin ranar bukin.
Gari na waye wa, sai aka ɗunguma zuwa wani ƙaton Otal JW Marriot Marƙuis Hotel waɗanda dukkansu suna kan layi ɗaya ne, inda a nan aka fara wannan buki gadan-gadan. Kan ka ce kwabo guri ya cika maƙil, wanda aka ƙiyasta cewa sama da mutum 300 daga ƙasashe daban-daban ciki har da Nijeriya suka halarci wannan gagarumin buki. Manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siysa da manyan ma’aikatan gwamnati da sarakunan gargajiya suka dinga shigo wa wannan ƙasa da ke Daular Larabawa, don kar a bar su a baya wajen wannan gwangwaje wa da ake yi a ƙasar ta Dubai.
A cikin kwanakin ƙarshen makon babu abin da ake yi sai cashe wa, kowa na gwada irin basirar da yake da ita, don ya faranta wa mahalarta wannan buki rai. Shi kuwa Ango, Oluwatosin Omokore, ɗan fari a gurin hamshaƙin ɗan kasuwar Man nan Olajide Omokore, da Amaryarsa Faiza Fari, ita ma ‘yar fari ce a wajen mahaifinta Abdulkadir Fari, wanda shi ne babban sakatare a Ma’aikatar kula da albarkatun Man Fetur ta ƙasa, sun nuna cikakken farin ciki a wannan rana. Mujallar Encomium Magazine ta ruwaito cewa, an kashe kimanin Dala miliyan 8 wanda ke daidai da Naira biliyan N1.2 wajen sayen kayan da aka bayar na kyaututtuka irin su, wayoyi ƙirar Blackberry Ƙ10 wadda ita ake yayi a wannan lokacin da sauran wasu ire-iren wayoyi masu tsada da wasu kayan ƙyale-ƙyale a wajen wannan gawurtaccen buki.
Da ana tunanin Mista Omokore ne zai yi hidimar auren, wanda kuma ake ganin ba zai iya bayar da kuɗin da za a sayi kyaututtukan da za a bayar ba a wajen wannan bukin ba. Shi kuwa Mista Fari, wanda ake ganin sa da bin ƙa’ida a wajen gudanar da harkokin kasuwancin Mai, sai ya zama babu yadda zai yi, dole sai ya bi ra’ayin ogarsa Misis Alison-Madueke na dole a yi bushasha.Yana daga cikin tsofaffin ma’aikata a kamfanin Mai na NNPC, wanda ya yi aiki da Daraktoci da Sakatarori a shugabancin da Misis Alison-Madueke ta yi na tsawon shekara biyar.
Idan muka koma baya, a cikin watan Mayu, na shekara ta 2010, lokacin da Umaru Musa Yar’aduwa ya rasu wadda ita ta yi sanadiyyar kasancewar Goodluck Jonathan ya zama shugaban ƙasar Nijeriya. Ya fuskanci matsin-lamba a wajen iyayen gidansa da kuma shugabannin jam’iyyar, PDP, kan batun tsayawarsa takara a shekara ta 2011. Daga nan ya fahimci cewa, bari ya yi amfani da Ma’aikatar albarkatun manfetur don ya samu kuɗin da zai gudanar da zaɓe wanda kuma bisa al’ada haka aka saba tun da aka fara mulkin dimokaraɗiyya a shekara ta 1999.
Don ganin al’amura na tafiya kamar yadda suka kamata ministan wancan lokacin, Rilwanu Lukman, ya yi wa kamfanin NNPC garambawul,yadda zai gudanar da harkokin kasuwanci gadan-gadan, wanda bayan gama wannan aiki, sai aka maye gurbinsa da Diezani Alison-Madueke, lokacin da aka yi wa ma’aikatu gyaran fuska. Misis Alison-Madueke ba ta samu wani cikakken ikon gudanarwa ba, har sai a watan Mayu, na shekara ta 2015, lokacin da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa. A wannan lokacin ne ta samu cikakken iko domin kuwa takan kori duk wanda ba ta so a gurin, ko kuma kai tsaye ta sa fadar shugaban ƙasa ta kore shi.
A lokacin da Nijeria ke samun sama da Naira tiriliyan 39.5 daga ɓangaren albarkatun Man fetur, wanda a lokacin ake sayar da gangar Mai a kan Dala 112, a wannan lokacin daga shugaban ƙasa sai Ministan mai ke faɗa a ji, musamman saboda ƙarfin da Ministan ke da shi, a cikin dokar da ta kafa Ma’aikatar a shekarar 1969. A tsawon shekara biyar da Misis Alison-Madueke, ta yi ta samu ɗaukaka fiye da yadda ake tsammani.
- Wacece Diezani?
An haifi Diezani Kogbeni Agama a garin Fatakwal wata biyu bayan samun ‘yancin kan Nijeriya, Ita ce ‘ya ta uku a gurin mahifinta daga cikin ‘ya’ya shida da yake da su. Mahaifinta Frederick Adama babban ma’aikaci ne a kamfanin haƙar albarkatun Man fetur na Shell (SPDC) wanda kuma bayan ya ritaya a wannan kamfani ya koma gida ya zama shugaban ƙabilan Epie-Atissan da ke Yenaka a jihar Bayelsa. Mahaifiyarta Beatrice Agama tohuwar malamar makaranta ce. Kodayake iyayenta ba masu hali ba ne sosai, kamar yadda ake ta kururuta wa, amma duk da haka sun yi rayu wa cikin rufin asiri. Deizana ta taso a rukunin gidajen kamfanin Shell kusa da unguwar Rumuomasi da ke cikin garin Fatakwal, ta yi makaranta a Warri da Fatakwal da kuma Mubi.
Gudummawar da kakanta N.K Porbeni, wanda shugaba ne a cikin ƙabilar Ijaw daga jihar Delta ya ba ta, a kan harkar ilimi ya taimaka mata wajen yin karatu a fannin zane-zane, maimakon fannin koyon Fasahar sana’o’i. A wata hira da aka taɓa yi da ita a shekara ta 2007, ta bayyana cewa, kakan nata ya tashi takanas daga Warri zuwa wajenta a ƙasa Turai wanda ya gaya mata cewa, babanta ba zai ɗauki ɗawainiyarta ta yi karatu a fannin zane(Fine Arts) ba, sai dai, in tana buƙatar taimakonsa ta yi karatunta a fannin zane-zane (Architecture).
Ann Pickard,mutumin ƙasar Amurka ne da ya riƙe wannan kamfani daga shekara ta 2005 zuwa 2010, wanda kuma aka san shi da yawan ƙorafi, sai da ya jawo ta a jika ya ƙara mata matsayi saboda ya fahimci ƙwarewarta a kan aikin da take yi. Ta yi wu Mista Pickard, ya yi haka ne domin ya daɗaɗa wa gwamnatin Nijeriya, kamar yadda kafar sadarwa ta Wikileaks ta bayyana cewa, ya yi haka domin kowane ɓangare na al’ummar ƙasar su ji ana damawa da su wajen gudanar da harkokin kamfanin.
A cikin watan Yuli, 2007, ne aka naɗata Ministar sufuri. Sai dai ba ta daɗe a kan wannan matsayi ba. Bayan sauke ta daga wannan matsayi sai kuma a watan Disamba, 2008 aka naɗa ta Ministar ma’aikatar tama da ƙarafa har zuwa watan Maris na shekara ta 2010.
A lokacin da take riƙe da wannan muƙamin ne ta kafa wata Hukumar tattaro kayan ƙarau na gargajiya,wadda shahararren maƙerin farin ƙarfen nan Chris Aire ya shugabanta. An yi mamakin irin kayan ƙarau ɗin da aka zo da su a wani taro da aka yi a ƙasar Kalifoniya a watan Afirilu na shekara ta 2010, wanda Misis Alison-Madueke ta shirya, jim kaɗan bayan naɗa ta a matsayin Ministar mai. Ganin nasarar da aka samu, bayan kamar wata ɗaya, sai Ministar ta buɗa wa Mista Aire ƙofa a Ma’aikatar man fetur ɗin yadda zai wawashi nasa kason, har ma ya haɗa da na sauran jama’a, ta hanyar yi wa wani kamfani na sa rajista wanda aka dinga ba shi kwangilar fitar da ɗanyen mai, wanda kuma aka yi ƙiyasin cewa, kullum yana samun sama da Dala 30,000.
Sha’awar da take da ita, ta sa kayan ƙarau masu tsada, don ta yi fitar kece raini, ya sa take ƙoƙarin kwatanta irin shigar marigayiya Gimbiya Diana ‘yar ƙasar Ingila. Kan ka ce wani abu sai ƙawayenta da masu yi mata fatan alheri da muƙarrabanta suka shiga kiranta Gimbiya Di.
- ’Yan Tawagarta
Daga cikin ‘yan tawagar ta ta akwai, Lauya Donald Chidi Amamgbo,wadda ta ce, sun zama ƙawaye tun lokacin da suke karatu a jami’ar Howard, ita ce ‘yan jarida ke bayyana ta da matsayin babarta. ‘Yar asalin jihar Imo ce, ba Bayelsa ba. Ta yi aikin lauya a ƙasar Amurka ƙarƙashin, Amamgbo & Associates. A shekara ta 2012, ƙungiyar lauyoyi ta Kalifoniya ta dakatar da ita, saboda kama ta da aka yi da laifin rashin ɗa’a.
Bayan gama zaɓe, lokacin da aka yi naɗe-naɗe, kowa ya fara aiki, sai abokai da masu fatan alheri da ‘yan kwangila da masu ruwa da tsaki a wasu ma’aikatu, suka dinga miƙa saƙon fatan alheri da bayar da kyaututtuka ga waɗanda suka samu muƙamai da taya su murna a kafafen yaɗa labarai, duk don kar a manta da su in wani alheri ya taso, ko kuma in suna neman wata alfarma.
“Idan wani ya aiko maka da kyautar Dala10,000 da wasu kayan ƙarau masu tsada, ba tare da ya nemi wani abu a gurinka ba, ya kamata ka kira shi wata rana ka gode masa kuma ka gayyace shi don ya kawo maka ziyara”, In ji wani tsohon ma’aikaci a Ma’aikatar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, saboda har yanzu yana aiki a Ma’aikatar, kuma akwai doka a aikin gwamnati wadda ta hana ma’aikaci yin magana da ‘yan jarida. “Ko a ce ‘yarki ta kira ki daga ƙasar Dubai ta gaya miki cewa, wani mutum ya biya mata kuɗin makaranta na shekara biyu, sannan kuma ya kama mata ɗakin da za ta zauna, za ki ce a’a ba ki so? Ko littafi Maitsaki ya ce,” ba a mayar da hannun kyauta baya.”
Saboda haka, Allah kaɗai ya san irin kyaututtukan da Misis Alison-Madueke ta samu daga mutane daban-daban a faɗin duniya.Wasu kuma hidima suka yi mata saboda kusanci da suke da shi da ita. Daga cikinsu akwai Kola Aluko,ɗan kasuwar Mai, da ke son ya haɓaka kasuwancinsa, akwai Mista Omokore, shi ma ɗankasuwa ne, wanda ke neman sa’a, sannan akwai mutane irin su Benedict Peters da Walter Wagbatsoma waɗanda dukkansu muƙarrabanta ne. Sannan daga cikn ‘yan tawagar ta ta akwai:
Kola Aluko: Hamshaƙin attajirine da aka Haifa ya kuma taso a garin Legas. Yana daga cikin ‘ya’ya taran da mahaifinsu Akanni Aluko,ƙwarrare a fannin ilimin ma’adanai kuma fitatccen shugaba a garin Ilesha, da ke jihar Osun ya Haifa. Ya fara tsoma ƙafarsa a kan kasuwancin Mai a shekara ta 1995, bayan ya shafe shekaru yana gararamba tsakanin ma’aikatar harhaɗa magunguna da ta haɗa motoci. Daga nan, sai Allah ya yi masa gyaɗar dogo, ya samu ɗaukaka a wannan kasuwanci, har ya kafa kamfanin Mai na Besse Oil, A tsakiyar shekarun 2000, Ɗaya daga cikin kamfanoninsa, Eɗoro Energy International ya yi haɗin gwiwa da kamfanin Weatherford, suka zama Seɓen Energy. Mista Aluko ne ya ci gaba da tafiyar da wannan kamfanin tare da taimakon Mista Omokore da kuma Phillip Ihenacho.
Mista Omokore: Ɗan asalin jihar Kogi, wanda aka ba shi sarautar gargajiya ta Elegbe na Egbe a garinsu a watan Oktoba na shekara ta 2014, saboda gudummawar da yake ba al’ummarsa, kuma yana daga cikin Dattawan jam’iyyar PDP tun daga jiha har zuwa ƙasa. Yana cin moriyar gwamnat a wajen harkokin kasuwancinsa, kasancewarsa cikin jam’iyya mai mulki. Omokore ya taɓa bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a shekara ta 2012.
- Yadda aka yi babakere a kamfanin NNPCda NPDC
Ranar 1 ga watan Satumba na shekara ta 2011, aka ƙulla yarjejeniyar tafiyar da tsarin baiɗaya (SAA), tsakanin kamfanin NPDC da Septa Energy,wanda yake wani ɓagare ne na Seɓen Energy don mallakar fili bisa tsarin OMLs 4 da 38 da 41. Haka kuma an sake ƙulla wata yarjejeniyar da Atlantic Energy Drilling Concepts (AEDC) Ltd a kan tsarin OMLs 30 da 34. Waɗannan kamfanoni na biyan haraji ga gwamnatin Nijeriya kamar yadda kamfanonin ƙasashen waje ke biya.
Saboda haka sai ya zama dukkan kwangilar da za a bayar ta hannun wannan kamfanin take fito wa, wanda kuma ya nuna yadda aka bijire wa yi wa dokar bayar da kwangila, wadda ta tanaji cewa, dukkan kwangilar da za a bayar sai an yayata a kafafen yaɗa labarai don duk wanda ke da sha’awa ya kuma cika ƙa’ida ya nema, in ya samu, ya yi. Don haka sai Misis Alison-Madueke ta yi fatali da dokar kamfanonin haƙar Mai da samar da Iskar Gas ta 2010, da ke cewa dukkan kamfanonin haƙar Mai da samar da Iskar Gas su dinga nuna tsarin gudanar da ayyukansu na shekara goma.
Kamfani biyu ko sama da haka ne kan haɗu su ƙulla yarjejeniya, kan wata manufa da suke son cim ma kamar ta, samar da ƙwararru, ko ƙara ƙarfin jari ko kuma yadda za su rage yawan kuɗin da suke kasha wa wajen gudanar da aikace-aikacen kamfanin. NNPC ta yi amfani da irin wannan yarjejeniya wajen samar da ƙarfin jari da ƙwararrun ma’aikata.
A shekara ta 2014, Malam Sanusi ya gaya wa Majalisar Dattawa cewa kamfanint Atlantic ya samu ribar sama da Dala biliyan 7 tsakanin watan Janairu na shekara ta 2012 zuwa watan Yuli na shekara ta 2013, duk da wannan ɗimbin kuɗi da ya samu, bai bayar da harajin ko kwabo ba, wanda ya saɓa wa dokar bayar da haraji ta kamfanonin haƙar mai ta 2007, amma shi kuwa kamfanin kamfanin NPDC ya biya gwamnati harajin Dala miliyan 400.
“An yi adalcia wajen rabon ribar kamfanonin haƙar mai”, kamar yadda aka bayyana a wani bincike da aka yi a babi na 10 ƙarƙashin (d) daga (i) zuwa (ɓ), wanda ya bayyan cewa, kamfanonin za su raba ribar Mai da ta Iskar Gas bisa kason kasha 90 daga cikin 100 na NPDC kashi10 cikin 100 kuma na Atlantic, sannan kuma bisa jarin da suka zuba za a bayar da kashi 40 da kashi 60, amma da aka yi bincike sai aka gano kamfanin Atlantic na wawushe kashi 70 ya bayar da kashi 30 daga cikin 100.
Janar Abdulsalami da Sashe na 16
Indan muka waiwaya baya, lokacin da Abdussalamu Abubakar ke mulkin ƙasar n a matsayin soja a shekara ta 1999 zuwa lokacin miƙa mulki ga gwamnatin farar hula, an tura maganar dokar harkar kwangilolin Mai zuwa ofishinsa.
Dokar an yi ta ne don magance koma bayan da aka samu wajen zuba jari a harkar Mai ta a wancan lokacin, saboda rashin samar da ababen da suka kamata a ƙasa na gudanar harkar hada-hadar Man. A lokacin ne Nijeriya ta ƙulla wata yarjejeniya, kodayake dokar ba ta samu cikakken goyon baya ba. Musamman idan aka yi la’akari da sashe na 16.
Don tabbatar da ingancin gudanar da raba kwangilolin a bisa yadda ya dace tare da na haɗin gwiwa, ƙarƙashin wannan Dokar hukumar zuba jari ta ƙasa ta mai da gudanar da ayyuka,(NPIMS), ƙarƙashin wannan dokar. Sannan kuma aka sa kamfanonin da aka yi wa kwaskwarima ta shekarar 1990 cikin dokar.
A bisa wannan dokar, an ba NAPIMS haƙƙin haƙo Mai da kula kayayyaki da kaddarori na gwamnatin tarayya.
Hakan ya biyo bayan ɗabi’ar da wasu gwamnatocin ƙasar nan suka saba yi ne na rattaba hannu a kan ayyukan rikici a ƙarshen mulkin su.
Cikin kwana sha tara na mulkin Dimokiraɗiyya, na ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999. An sanya hannu a kan ƙudirin da ya zama doka, sai dai akwai wata dokar da aka sa ta a cikin tsarin, wadda daga baya aka kuma cire ta. Dokar ita ce ta sashe na 16.
Wata majiya a Ma’akatar Mai da ba ta son a ambaci sunanata, ta tsegunta cewar, kwaskwarimar ta bada wata dama wajen tabka almundaha , musmman saboda saƙala wani sashen da ya bai wa JƁs damar shiga cikin harkar.
Da NPDC ta biya dukkan Bil ɗinta kuma da an sa ɗanyen Man cikin ƙididdiga da ba bai wa kamfanin juicy OMLs ba .
Majiyar ta tambaya shin NPDC za ta yi amfani da kuɗaɗen masu ruwa da tsaki don aikata wannan shirmen ?”
Idan wannan sashen da aka cire naƙasu ne, ƙarfin ikon da aka bai wa Ministan albarkatun Mai, da ita ce Alison-Madueke ta yi amfani da damar ta ci karenta ba babbaka.
Gaba ɗayan Masana’antar Mai tana ƙarƙashin kulawar Shugaban Ƙasa da Ministar ce, shi shugaban ƙasar ya naɗa ta, Majalisar Ƙasa ce kawai za ta iya duba ƙarfin ikonta, amma ba ta iya wani kataɓus.
A cewar Bassey wanda aka sakaya sunansa amma aka bada sunan sa na ƙarshe ya ce,“ takurawar siyasa da aka ɗora a kan Ministocin ƙuɗi, sai aka mai da Kamfanin na NNPC tamkar injin fitar da kuɗi don a gudanar da zaɓe.”
Bassey ya ce, “Ministar ta ƙara sanyawa alamuran suka ƙara taɓarɓarewa saboda ƙarfin ikon da take taƙama da shi.
Ya ƙara da cewa,“ CBN ba ta cikin wannan sahun, domin kuwa Sanusi ya ci gaba da yin matsin lamba a kan badaƙalar da ke aukuwa a lokacin a NNPC.
Ya bayyana cewar, ɗaya abin da ya dinga hana ruwa gudu a lokacin shi ne yadda ma’aikatan gwamnati suka yi gum da bakinsu, ba don komai ba sai don kawai su tsira da aikinsu don gudun kada su haɗu da fishin shugabanninsu.
Har an kai matsayin ɗaga jajayen Tutoci saboda karon battar ƙarfe da ta auku tsakanin hukumomi na cikin gida da Bankuna da kuma masu tantance kuɗi.
Wani ɗan kare raji mai suna Kola Banwo mazauni a Abuja ya ce, “gwamnati kaifi ɗaya ce, kuma cibiyoyi sauna da rawar da suke takawa sai dai hanci da rashawa ya rikirkita alamuran.
Kamfanin NNPC yana da tsare-tsare na cikin gida da dabaru da zai iya daƙele duk wata kafa da za a iya yin almundahana.
Kwamitoci daban-daban na Majalisar Ƙasa ba su yi amfani da ƙarfin ikonsu na sa Ido ba, don taka wa badaƙalar birki ba, haka Ofishin Mai bincikin Kuɗi na Tarayya bai iya yin wani kataɓus ba, uwa uba, Hukumomin EFCC da ICPC da sauransu.
Abin takaici, duk waɗannan matsalolin an yi biris da su, maimakon a magance su a wancan lokacin, ko ba a magancesu duka ba, inda da niyya da an rage su.
Masu bibiyar al’amuran sun bayyana cewar, Misis Alison-Madueke ta yi wa dokar hawan ƙawara ce, saboda ɗaurin gindin da take da shi lokacin tsohuwar gwamnatin ta Jonathan. Akwai wasu lokuta da har ta kai ta kawo ba ta karɓar baƙi a ofishinta, takan kuma shanya Gwamnoni har na zuwa tsawon awowi ba tare da ta ba su dama sun ganta ba, da ƙin ɗaukar kiran wayar Manyan Jami’an Kamfanin na NNPC kuma Jiga-jigan masu hada-hadar Mai na ƙasashen waje sun ɗauki ma’aikatansu da ake biyansu a ƙarƙashin kamfanin na NNPC.
An yi zargin cewar Misis Alison-Madueke ta buƙaci waɗanda suka haɗa kai don gudanar da badaƙalar da su ba ta na goro don ta amince wa da wasu kwangiloli, haɗe da katafariyar kwangilar nan ta Mai da Shugaba Buhari ya ƙarashe ta a watan Nuwambar Shekarar 2015. Alal misali, Mista Aluko ya amsa laifinsa na cewar, ya biya kuɗin haya na gidan da uwargida Beatrice Agama ta kama a yankin Parkwood da na yankin Edmund’s Terrace da kuma na yankin John’s Wood duk a ƙasar Ingila, inda ya bayyana cewar, wannan kamar ‘yar kyauta ce kawai ga abokai.
A cikin watan Okotoba, na shekarar 2014, lokacin da za ake shirin gudanar da zaɓuɓɓukan shekarar 2015, Bernard Otti wanda Darakta ne a Kamfanin NNPC, an ƙara masa matsayi zuwa Mataimakin Manajan Darakta na sashen Kuɗi,inda wannan muƙamin an ƙirƙiro shi ne dare ɗaya, da nufin biyan wata buƙata ta son rai.
A takardar da aka raba wa manema labarai an bayyana cewa,an naɗa Bernard Otti a sabon muƙamin ne da nufin bunƙasa harkar kasuwancin na NNPC, amma a bisa maganar gaskiya, an yi masa naɗin ne don tabka badaƙalar yadda za a saci kuɗi don gudanar da yakin neman zaɓe.
Bayan an rantsar da Shugaba Buhari a matsayin Shugaban ƙasa, ya arce zuwa ƙasar Birtaniyaya, an kuma sha ruwaito wa cewar, daga baya ya bai wa Hukumar EFCC,haɗin kai wanda ta hanyarsa ta banƙaɗo kuɗin da aka ware don yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Ekiti da kuma sauran wasu batutu wa. Mista Kachikwu ne ya sanar da yi masa ritaya a watan Agustan shekarar 2015.
Binciken kuɗi da PwC da kuma KPMG suka yi ya nuna cewar, Kamfanin NNPC a kashin kanta ta kashe kimanin Dalar Amurka Biliyan 6 daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2013 and there were no, kuma abin takaici, an kasha waɗannan kuɗaɗen ba tare da an shigar dasu a rubuce ba.
Akwai wasu kuɗin da Kamfanin na NNPC ya saba shigar dasu duk shekar amma ba a shigar da su ba.
Bayan Tsohon Babban Bankin na CBN Sanusi ya gudanar da nazari da ƙirga, sai ya fasa Ƙwai, ta hanyar rubuta takarda mai shafi 20 zuwa ga Jonathan a watan Satumbar shekarar 2013, inda ya sanar da shi cewar, Dalar Amurka Biliyan 20 ta yi layar zana.
Kamafanin NNPC ya yi iƙirarin cewar, an kashe kuɗin ne wajen biyan tallafin na kananzir da kuma gyaran Bututun Manfetur, duk da cewar ‘Yar’aduwa, tuni ya kammala biya a watan Yuli na shekarar 2009.
Mista Banwo ya ce, PwC ta kuma ƙara yin wata ƙididdigar wadda ta miƙa ta kafin zaɓen shekarar 2015 aka kuma fitar da ita a ranar 27 ga watan Afirilun shekarar 2015.
Mista Banwo ya ƙara da cewa, “ƙungiyoyin kare raji sun sha bayyana cewar suna zargin cin hanci da rashawa a masana’antar ta mai Lokacin da aka bankaɗo maganar almubazzaranci a kan kuɗin da aka kashe wajen kula da jirgin sama ta fito fili, ƙungiyar kare rajin ta tayar da balli, inda ta buƙaci a yi bincike sannan kuma tsohuwar Ministan Man ta gaggauta sauka daga muƙamin na minista. Amma Jonathan ya yi kunnen-uwar shegu da kiran. Majalisar Ƙasa ma ta kafa kwamiti don bincika wa, amma ba abin da aka yi a kai.
A shekarar 2015, tsohon Gwamnan Bankin (CBN) ya yi zargin cewa, Misis Alison-Madueke na da cikakkiyar masaniya a kan ɓatan dabon da Dalar Amurka Biliyan 20 ta yi daga Asusun Kamfanin NNPC, inda hakan ta sa ƙungiyoyin kare raji, suka bazama wajen gudanar da gangami na a binciki Alison-Madueke da kuma cire ta daga muƙamin na Ministar Mai.
Sai dai, saboda ganin Alison-Madueke ‘yar lele ce a lokacin gwamnatin Jonathan, haka ta yi ta cin karenta ba babbaka, har maganar ta wuce. Idan Alison-Madueke Gimbiya ce, shi kuma Mista Aluko, an yi masa gani na ƙarshe ne a yankin Porza-Lugano da ke ƙasar Siwiziland a shekarar 2016, inda shi kuma ya zamo sabon Yarima.
Ya mallaki Jirgin Sama da kuma Galactica Star a watan Satumbar shekarar 2013 da kuɗinsu ya kai Dalar Amrka miliyan 80.
Ya bai wa shararrun Mawaƙan nan na Duniya, Jay-Z da Beyoncé haya a kan Dalar Amurka 900,000, zuwa tswon sati ɗaya ko kuma zuwa tsawon sati biyu lokacin da Beyonce ta yi bukin ranar zagayowar haihuwarta na shekara 32.
Mista Aluko babban mai ra’ayin shahararren ɗan wasan nan ne mai suna Ayrton Senna, kuma Aluko, yana sha’awar wasan tseren mota, ya taɓa zama na uku da Ferrari 458 GT2 a gasar tsren motoci da aka yi a filin tsre na Ɓallelunga dake Rome, a watan Disambar Shekarar 2012. Bugu da ƙari, Mista Aluko ya mallaki condo guda takwas masu tsadar gaske da ke New York, waɗanda aka ƙiyasta kuɗin su ya kai kimanin Dalar Amurka Miliyan 50.
Sashin Sharia’a na ƙasar Amurka ya shigar da ƙara a ƙarƙashin shirinsa na ƙwato kadara a kan wasu mutane da ake buƙatarsu su dawo da kadarorin da aka ƙiyasata kuɗinsu Dalar Amurka Miliyan 144 ribar da aka samu a kan kwagilar Mai.
Ganin Mista Aluko ya yi wuya, shi kuwa Mista Omokore, tuni aka gurfanar da shi a gaban Kotu tun cikin watan Yuli na shekarar 2016. Ita ma Misis Alison-Madueke ta shiga hannu, duk da cewar, har yanzu ba a fara yi mata Shari’a ba.
Gurzuwar da take yi mata a hankali, ga dukkan alamu yana haifar da ɗa mai Ido. Mista Bassey ya ce, “Ta sha nanatawa cewar in mun dawo, komai zai warware” Ga alamu ba ta san cewar, Jonathan zai sha ka ye ba a lokacin zaɓen na shekarar 2015 ba. Abin ke nuna wad a ya dawo da an ci gaba da tabka wannan badaƙalar.
Abin ya wuce maganar Misis Alison-Madueke da ‘yan korenta, sannan kuma babban abin da masu ruwa da tsaki a harkar Mai suke jin tsoro shi ne, dangane da wannan mulkin shi ne akwai alamun rufa-rufa.
Cikakkaun bayanan a kan badaƙalar da Alison-Madueke ta tabka lokacin tana riƙe da muƙamin na Ministar Mai, sai ƙara bayyana suke yi.
Har yanzu Kamfanin na NNPC cike yake da dambarwar siyasa, da ba shi da wani ‘yanci na ƙashin kansa ko aiwatar da aikinsa ba tare da aikata wata almundaha ba.