Dokaji Jnr" />

Diflomasiyyar Larabawa A Siyasar Duniya

arabiandokaji@gmail.com   08180897610

Siyasar Gabas ta tsakiya na daf da zuwa babinta na karshe, domin kuwa da alama mulkin Donald Trump zai haifar da wasu abubuwa da ya kamata su faru ko don karawa tarihi gudu. Abin al’ajabi ne, kuma abin kyama abin da yake samun Falasdinawa sama da shekaru 40, babu wani wanda ya damu yayi abin da ya kamata. Babu abin da Falasdinawan ke samu daga gun ‘yan uwansu Larabawa face hira da alkawaruka da babu ranar cika su.

Akwai bukatar a gane cewa rikicin Falasdinu da Yahudawan Israila ba wai rikici ne da ya shafi Larabawa ko Musulmi kawai ba, rikici ne da ya shafi dukkan mutum mai hankali da tunani. Tarihin siyasar Larabawa, tarihi ne na alhini da rashin hangen nesa.

Kafin mu tattauna halin ko in kula da Larabwa ke nunawa akan halin da Falasdinawan suke ciki, da kuma yadda Turawa suke gara su kamar kwallon kafa a hannun kungiyar Barcelona, akwai bukatar mu koma baya mu duba abin da ya faru a Daular Turkiyya a zangon karshe na karni na 19 da kuma sanda ta karye. Siyasar da Larabawa suka buga a lokacin ta nuna rashin sani da fahimta akan diflomasiyyar zamani ta Bature. Tsiraru daga cikin su ne, dama sauran Musulmi suka fahimce ta har a yau!

Lokacin da Mahukunta a daular Turkiyya ta Ottoman, suka mike tsaye domin magance karyewar Daular, masana sun bada shawarar cewa dole ne fa a koma kan turba zamanantar da harkokin mulki dama rayuwa su koma irin na Turawa.

Duk da dai sun yi kuskuren kallon zamanantarwa a matsayin kwaikwayon Bature, hakan ya dan bada mafitar a wasu abubuwan, kamar misali ilimi da Diflomasiyya. Daular ta Ottoman ta yi ta kiraye-kirayen mazaunanta da suka hada da Turkawa, Larabawa, Turawan Balkan Europe da kabilun Slabs da su zo a zauna a hada kai a zama tsintsiya madaurinki daya ba tare da duba da addini ko kabila ba.

Wannan kira na Ottomanism wanda Namik Kamal ya jagoranta, dai bai nasara ba, domin daya bayan daya wadannan kasashe na Kirista suka dinga yagewa da taimakon yan uwansu na Turai ta yamma. Misali a shekarar 1909 hadaddiyar Daular Austria-Hungary ta kwace Bosnia daga hannun daular ta Ottoman.

Wannan rashin hadin kai na mazauna Daular yasa aka samu wani aji na Turkawa, wadanda ake kira ‘Young Turks’ da suka fara dabbaka akidar ‘Pan-Turanism’, wadda take kira da samar da Daular Ottoman mai dauke da Turkawa kawai. Tunda wannan akida na kokarin nunawa mazauna daular cewa kowa fa ya manta da al’adarsa ya zama Baturke, hakan bainsamungoyin baya da karbuwa ba, musamman daga gurin Larabawa. Wannan tasa Larabawa suka nuna kyamarsu ga wannan yunkuri, domin ganin cewa suma ai suna da nasu al’adun wadanda ma sun fi na Turkawa. Wannan ya taimaka kwarai wajen zaburar da Larabawa da su farka su san inda yake musu ciwo, tunda dai ai dama sanda suka waye, Turkawa mutanen jeji da kauye ne. Manyan masanan Larabawa irin Nasif Yaziji (1800-1875), Bitrus Bustani (1819-1883) da Abdur-Rahman al-Kawakibi sun mike tsaye haikan domin samar da litattafai akan yare, al’ada da siyasar Larabawa. Ta kai har Abdur’•Rahman al-Kawakibinya zama mutum na farko da a littafinsa na Ummul Kura ya kira dana raba Daukar Ottoman gida biyu, Kudancin daular ya zama karkashin jagorancin Turkawa wanda zasu zama jagororin mulki, Arewaci kuma ta zamo karkashin jagorancin Sharifi Balarabe, wanda zai zama shugaban addini. Ana wannan rikici sai kuma ga yakin duniya na farko ya bullo.

A lokacin da Yakin Duniya na Farko (YDNF) ya balle, Manyan kasashen Turawa kamar Birtaniya da Faransa da kuma daular Rasha sun fara shirye-shiryen yadda za su karya Daular Ottoman wadda suke wa shagube da suna “sickman of Europe”. Sun kira ta mara masifa ne saboda zamar musu kadangaren bakin tulu da tayi. Daular taki karyewa da kanta ta fadi, duk da ficewa da ‘ya’yantaTurawa ke yi (kamar Crete Island da kasar Bulgaria a 1909 da irin su Albania a 1910) daga cikinta da kuma rikice-rikicen cikin gida tsakaninta da  irin su Gwamnan Misra Muhmmad Ali (1805-1845). Tunani da shirin yadda za a raba gadonta shine abin da wadannan dauloli na Turawan Yamma sukai wa lakabi da “Eastern Kuestion.” Larabawa sun hadu a bayan Sharif Hussain domin ya zama shugabansu, in da shi kuma ya bude tattaunawa tsakaninsa da kasashen Turawan Yamma, musamman Birtaniya. Daga watan Yuli na shekarar 1915 zuwa watan Janairu na 1916 an yi musayar wasiku guda biyar (5) tsakanin Sharif Hussain da jakadan Daular Birtaniya a kasar Misra, wato Mr McMahon. Wasikun sun ta’allaka ne akan abin da Larabawa za su samu a rabon gadon daular ta Musulunci ta karshe da ta rage wa duniyar Sunna.

Larabawan sun yi alkawarin goyawa Turawan Ingila baya akan yarjejeniyar cewa idan suka bada gudunmawa aka karya Daular, to za a basu daularsu ta Larabawa, karkashin jagorancin Sharif Hussain. Birtaniya tayi amanna da wannan sharadi, Larabawa kuma suka taimakawa Turawan Yamma suka yi nasara akan Daular Ottoman. Sai dai wani abu da Larabawan basu sani ba shine, a lokacin da aka kulla waccan yarjejeniya tsakanin Sharif Hussain na Makka da Mr McMahon na kasar Birtaniya, kasashe da daulolin Turai wadanda suka zama rukunin ‘Allied Forces’ a YDNF, na ta tattaunawa suma domin cimma matsaya akan yadda za su raba gadon Daular ta Musulmi baki daya idan suka yi nasarar cin ta da yaki. Hakan kuma fa na faruwa ne a yayin da kasar Birtaniyan take yiwa Sharif Hussain alkawarin bashi shugabancin Larabawa idan an gama yakin. Anyi yarjejniya har guda uku. A ta farko wadda ake kira da ‘Constantinople Agreement’, an yi ta ne tsakanin Birtaniya, Faransa da kuma Daular Rasha kowa an abashi abin da ya jima yana muradi. Rasha aka bata Birnin Istanbul, da yankunan Bosporus da Dardanelles. Birtaniya aka bata Kudancin Iraki, Falasdinu da kuma wasu tsibirai a yankin tekun ‘Mediterranean’ da Gulf of Mandab. Kasar Faransa kuma aka bata Arewacin Iraki da Syria.

Wannan rabo ya bar baya da kura, domin sabuwar hadaddiyar daular Italiya an yi wannan rabo ba ita. Tana kuwa jin labari tace ai kuwa itama sai an bata kasonta, tunda dai ba ‘yar kishiya bace. An sake wani zaman a watan Afrilu na shekarar 1915, a Landan, wanda akai wa lakabi da ‘London Pact’. Inda aka bawa Italiya yankin Anatolia ta tsakiya da tsibirin Dodecanese dake tekun Aegean. A wani shirin na yaudara da munafunci diflomasiyya, a watan Fabrairu na shekarar 1916, Birtaniya da Faransa sun kuma shirya wani rabon gadon a sirrance. An tattauna tsakanin jami’an kasashen biyu, Mr Georges Picot na Birtaniya da jami’in Diflomasiyya na kasar Faransa a Landan wato Mark Sykes. A zaman dai kasashen biyu sun yarda za su bawa Sharif Hussain kudancin Arabiya ya mulka, inda su kuma suka raba Arewacinta wanda ya kunshi yankunan ainihin Iraki da Syria da Falasdinu. Wannan yarjejeniya tsakanin Birtaniya da Faransa wadda ta shahara da sunan jami’an da suka yi ta, wato ‘Sykes-Picot Agreement’, ta faru ne a lokacin da Sarki Hussaini ke tattunawa da Birtaniya akan za a bashi duka daular Larabawa ya mulka. Shin taya Larabawa suka san wannan tuggun da Yaudara da rashin wayonsu ya kai su akai musu?

Lokacin da akai rabon Sykes-Picot ba a saka Daular Rasha a ciki ba. Sai a watan Oktoba na shekarar 1916 sannan ta samu labari. Duk da cewa babban burin Daular ta Rasha shine ta mallaki yankunan Bosporus da Dardanelles, rashin samun rabon gadon Yankin Larabawa bai mata dadi ba. Sai dai bata da abin yi a lokacin n domin ana ta fama da rikice-rikicen cikin gida da yan juyin-juya halin gurguzu ke haifar wa. Larabawa su kuma ana chan ana ta shiri za a kafa daula. Sai dai kash! Shugaba Bladimir Lenin da ya jagoranci kafa mulkin gurguzu a daular Rasha a shekarar 1917, ya sanar da Larabawa wawancinsu na abin da su kai. Sharif Hussaini ya samu labarin cewa a lokacin fa da yake ta kokarin yadda zai taimaka a karya daular Musulunci ta Ottoman saboda an masa alkawari daula, Birtaniya fa da Faransa burinsu daban. Wannan ya faru ne saboda rashin goyon bayan mulkin mallaka da zalunci da tsarin Gurguzu ke dabbakawa akan kasashe mara karfi. Rikici ya balle tsakanin Sharif Hussain da Birtaniya. Birtaniya tace ita fa dama sanda ta ce za ta bashi Daular Larabawa, yankunan da ta hana shi basa cikin wadanda tayi niyyar ba shi, tunda dama fa tun can ba Larabawa bane. Sharif Hussain ku!a ya dage akan cewa ai fa tunda aka ce Larabawa, duk yankin da ake Larabci harda shi ake nufi, tunda dai ai ba’a banbance ba, musamman kuma tunda duk irin wadannan yankunan na kiran kansu da Larabawa. Domin jin yadda ta kaya tsakanin Larabawa da Birtaniya, da yadda wannan rikicin ya bude kofar bawa Isra’ila kasa a Falasdinu, mu tara a mako na gaba!

 

Exit mobile version