Dillalai Da Makaranta Jarida Sun Jinjina Wa Fitowar LEADERSHIP A YAU

Daga Sharfaddeen Sidi, Sokoto

Masu sayar da jarida a fadin Nijeriya sun bayyana jin dadi da gamsuwarsu kan fara fitar LEADERSHIP A YAU a kasuwar jaridu ta Nijeriya a matsayin jaridar Hausa ta farko da ta fara fita a kowace rana.

A cewarsu, kamfanin LEADERSHIP ya shige kan gaba wajen daga daraja da bunkasa Harshen gida ta hanyar samarwa al’ummar Hausawa abin karatu domin sanin halin da kasa da duniya take ciki.

Wani mai sayar da jarida a Bauchi Samuel Dibine a yayin da yake tattaunawa da wakilin mu ya bayyana cewar fara buga LEADERSHIP A YAU ya nuna cewar rukunin kamfanin LEADERSHIP ya shirya tsaf domin bunkasa wallafa jarida a Harshen Hausa.

“Na yi magana da ‘yan uwa na masu sayar da jarida a Nijeriya sun kuma nuna mani matukar farin cikin su kan bayyanar LEADERSHIP A YAU a kasuwa a matsayin jaridar Hausa da ake bugawa a kullum.”

Haka kuma wani ma’aikacin Gwamnati a Jihar Bauchi Aliyu Usman a tattaunawa ta wayar tarho ya bayyana fara wallafa jaridar a matsayin “Abin tarihi ne a tarihin Tarayyar Nijeriya.”

Ya ce kaddamar da LEADERSHIP A YAU ‘yar manuniya ce da ke nuna cewar Harshen gida ba zai taba bacewa ba a Nijeriya.

Ya bayyanawa yakininsa na cewar jaridar za ta samu kasuwa.”Ina taya murna ga bakidaya Rukunin Kamfanin LEADERSHIP kan wannan namjin kokarin da suka yi ta hanyar tserewa tsara. Yadda jama’a suka karbi jaridar bisa ga yadda masu sayar da jarida ke bayyanawa abin yabawa ne.” Inji shi.

Malam Abubakar Ali tsohon dan jarida ne da ke zaune a Sakkwato ya kuma bayyana ra’ayinsa da cewar kamfanin LEADERSHIP ya kafa tarihin da ba a taba kafawa ba ta hanyar wallafa jaridar Hausa da ke fita a kowace rana.

“Kamfanin LEADERSHIP ya kafa babban tarihi na fara wallafa LEADERSHIP A YAU. Abin farin ciki ne jama’a su rika karanta labaran su a kullum maimakon mako- mako. Na yaba kwarai kan yadda ake tsara bango da shafukan cikin jaridar.” Ya bayyana.

Ya kuma ce “LEADERSHIP A YAU kalubale ce ga sauran jaridun Hausa wadanda ke fita a sati. Baya ga wannan yana da kyau a bayar da kulawa sosai wajen tabbatar da zuwan jaridar cikin lokaci domin idan har jarida ta na zuwa a makare to hakan zai shafi cinikinta a kasuwa.”

A ra’ayinsa Sirajo Al- Mustapa bayan ya nuna jin dadin sa kan fitowar wannan jaridar ya kuma bayyana cewar “A inda aka fito mun gamsu da ayyukan LEADERSHIP Hausa don haka fatar mu ita ce LEADERSHIP A YAU ta tsayu kamar yadda muka santa a baya wajen tsage gaskiya, aiki tukuru da kuma nemarwa al’umma musamman talaka makoma mai kyau. Idan da hali a kara fito da filaye domin mata da matasa, sa’anan kuma wurin farashi a kula da yanayi domin a yau abin ya zama kullum.” Inji matashin.

Shi kuwa Sani Dallatu cewa ya yi bai taba tunanin za a wayi gari da jaridar Hausa mai fitowa a kowace rana ba. “Ban san yadda zan fasalta farin cikina kan wannan muhimmin ci-gaba da daukaka da Harshen Hausa ya samu ba. A matsayina na dalibin Hausa wannan abin alfahari ne kan yadda LEADERSHIP ta yi hobbasar kwazon kara raya Harshen Hausa wanda a inda aka fito ba mu taba tunanin samun jaridar Hausa mai fitowa a kowace rana ba. Muna murna fatar mu Allah ya fitar da A’i daga rogo.”

An fara buga jaridar LEADERSHIP Hausa shekaru 11 da suka gabata wato a shekarar 2006 daga bisani a farkon wannan makon kamfanin ya daura damarar kai jaridar a kololuwar matakin aikin jarida ta hanyar fara wallafa ta a kowace rana wanda hakan ne dalilin da yasa aka inganta sunan zuwa LEADERSHIP A YAU da zummar zama jaridar Hausa ta farko da za ta rika labartawa al’umma labarai ingantattu kuma sahihai a kowace rana cikin kwarewa da gogewar lakantar aikin jarida a mataki ba kwararru.

Ilmance a sahun jaridu da mujallu, LEADERSHIP A YAU ta bayyana a matsayin uwa ma ba da nama. A Hausance azama da karin habaka harshen Hausa, LEADERSHIP A YAU ta bayyana a matsayin gagara gasar masu gasa.

 

Exit mobile version