Connect with us

Ka San Jikinka

Dimbin Amfanin Da Shan Ruwa Ke Yi A Jikin Dan’Adam

Published

on

A gaskiya kamata ya yi a ce ruwa shi ne mafi soyuwa a cikin abubuwan da ake sha, saboda a yayin da dan’Adam ka iya kwashe sati uku ba tare da cin abinci ba, to ba zai iya kwashe kwana uku ba tare da ya shan ruwa ba.

Da akwai bukatar adadin yawan ruwa da ake so kowanne mutum ya sha a rana. Masana sun gudanar da bincike da dama da ya nuna cewar, kwakwalwar mutum na da bukatar adadin yawan ruwa a rana don samun gudanar da aiki yadda ya kamata.

A cewar wani babban likita Dakta. Robert A. Huggins, na asibitin koyarwa a jami’ar

Connecticut, ta kasar Amurka, ya ce “kwakwalwar mutum na bukatar akalla yawan ruwa da ya kai “8*8” wanda ya yi dai-dai da yawan ledar fiyowata 5 a rana”. Ya kara da cewar kwakwalwar mutum na da nauyin kashi 3.5% na nauyin mutum,

amma ita ke cin fiye da kashi 20% na duk wani abu da mutum ya ke ci” Hakan na nuna cewar kwakwalwa tafi kaso mai yawa da sauran sassan jikin mutum. Hakan ya sa tana bukatar ruwa mai tsafta da yawa don gudanar da aiki yadda ya kamata a cikin lokaci.

Sai ya kara da cewar hakama idan jiki na lafiya akwai bukatar motsa jikin, don ta hakan kwakwalwar ke kara samun kuzari da aiki yadda ya kamata. Domin kuwa idan jini ya isa cikin kwakwalwa zai bukaci yawo a bangarori daban-daban na kwakwalwar. Wannan binciken ya kara tabbatar da muhimancin ruwa a cikin jikin mutun a kowane lokaci.

Cututtukan Da Shan Ruwa Ke Warkarwa

• Ciwon zuciya ya zama ruwan dare a tsakanin mutane kuma a kullu yaumin yana kara gagarar magani. Amma a sani ruwa na da alaka da ciwukan da suka shafi zuciya. Bincike ya nuna shan kofi 5 na ruwa a rana na rage yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya da kashi 50 bisa 100.

• Maganin ciwon amosani, idan mara lafiyar na yawan shan ruwa. Ruwan zai taimaka wajen kawar dasinadaran dake taruwa a jiki masu samar da amosanin.

• Ciwon mara lokacin al’ada. Idan mace na fama da ciwon mara sai ta dinga shan ruwan dumi, domin yana fitar da jinin da ya daskare a marar mace.

• Shan ruwa yadda ya kamata zai taimaka wajen baiwa koda cikakkiyar lafiya, ta hanyar wanke ta, saboda aikin koda da hanta ne fitar da duk wani nau’in datti a jikin dan’Adam.

• Yana wanke duk wata cuta ko dauda dake jikin mutum yayin da ya farka.

• Maganin sanyi. Tsarki da ruwan dumi na taimakawa mata wajen maganin cututtukan sanyi da kaikayi da kuraje.

• Yana sa kyaun fatar jiki.

• Yana sa mutum ya ji karfi a jikinsa.

• Shan ruwa yana gina jikin dan’Adam.

• Yana haduwa da jini don kai kowane sinadari jikin mutum wajen aikinsa.

• Maganin ciwon Ido. Idan idon mutum yana yi masa ciwo, sai ya samu ruwan dumi mai tsafta, ya zuba a cikin kwano mai kyau sai ya shigar da fuskarsa ciki ya bude idanuwansa, wannan yana wanke datti da kuma kwayoyin cutar dake cikin ido.

• Yana maganin cushewar ciki.

• Yana sa jiki ya yi sanyi kuma yana yaye zazzabi da zafin jiki.

• Yawan shan ruwa yana sa mutum walwala da fara’a.

Amfanin Ruwan Dumi A Jikin Dan’Adam

farko dai kafin mu fara muna so mu fada ma ku cewa shan ruwan sanyi na da matsala da dama. Idan mutum ya sha ruwan sanyi da zaran ya gama cin abinci ya kan je ya toshe magudunar jinin jikin mutum kuma yin hakan na janyo cututtuka da dama kamar  ciwon suga, ciwon daji. Ruwan sanyi ya kan zamanto kamar guba a cikin  mutum musamman ma  idan har mutum yana yawaita shan sa a kowane lokaci hakan ya zama kamar cuta a cikin jikin mutum.

Shan ruwa mai dumi yana da matukar amfani a jikin mutum. Masana sun gano cewa shan ruwa mai dumi kamar lita 1 da safe kafin mutum ya karya kumallo,

musamman ma idan mutum ya sha

ruwan ya dan jinkirta bayan awa 1 kafin ya karya kumallo. Yin hakan na maganin cututtuka da dama kamar haka:

1. A farko dai shan ruwa mai dumi kafin awa 1 a karya kumallo. Idan har mutum         zai yawaita yin haka har na tsawon kwanaki 30, yana magance ciwon suga. Idan har mutum ya yi hakan ya tafi asibiti gwajin sugar, jikin zai ga yayi kasa.

2. Shan ruwa mai dumi yana maganin ciwon kunne. Idan mutum zai sha ruwan dumi da safe kafin ya karya kumallo har na tsawon kwanaki 10 zai rabu da ciwon kunne da yake fama da shi.

3. Shan ruwan dumi na maganin ciwon mara na ‘ya mace. Idan mace na fama da ciwon mara kafin zuwan jinin haila wato al’adanta, idan har za ta sha ruwan dumi da safe awa 1 kafin ta karya kumallo na tsawon kwanaki 15, da yaddan Allah(S.W.T) za ta samu saukin cewon da ta ke fama da shi.

4. Idan mutum na fama da ciwon zuciya. Idan mutum zai sha rowan dumi na tsawon kwanaki 30, zai samu sauki sosai da cewon dake damun sa.

5. Mutum mai yawan ciwon kai musamman ma wanda rabin kansa ke yawan ciwo, za ka ji kansa na tsarawa. Idan mutum ya sha rowan dumi na kwanaki 3 zai samu sauki.

6. Mutum mai fama da taruwan jini a jikin sa wato wanda jininsa bai gudana. Idan har mutum zai sha ruwan dumi har na tsawon kwanaki 30 jijiyoyin jikinsa za su warware sannan kuma jinin jikinsa zai samu guduna yadda ya kamata.

7. Mutum wanda bai samun isashen jinni na guduna a zuciyarsa. Idan har zai

sha ruwan dumi na watanni 4, da yaddan Allah(S.W.T) mutum zai samu sauki ciwon dake damunsa.

8. Yana maganin ciwon farfadiya. Idan har mutum zai sha ruwa dumi na tsawon wata 9 zai samu saukin ciwon.

9. Yana maganin ciwo fuka. Idan ana shan ruwan dumi har na tsawon watanni 4, in Allah (S.W.T) ya yadda mutum zai samu sauki.

10. Idan mutum na yawan samun minjirya, idan har mutum zai sha ruwan dumi na kwanaki 3o zai samu sauki haka da yaddan Allah (S.W.T) zai warke.

11. Ciwon Ciki. Idan dan’Adam na yawan fama da ciwon ciki, idan har

zai sha ruwan dumi na tsawon kwanaki 10 zai samun sauki ciwon.

12. Ciwon daji. Idan har mutum na fama da ciwon daji, idan har zai jira watanni 9 yana shan ruwan dumi to zai warke.

13. Mutum mara son cin abinci. Idan mutum ba mai son yawan cin abinciba ne to ya yawaita shan rowan dumi, idan har mutum zai yawaita shan ruwan dumi na tsawon kwanaki 10 zai samu damar cin abinci yadda ya kamata.

Abin Lura

-Ruwan dumi da ake nufin mutum ya sha, ana so ya zamo mai dan zafi kamar ruwan shayi.

-Ana so kuma a sha ruwa da safe ne.

– Ana kuma son ruwan kada ya yi kasa da lita 1. Bayan mutum ya sha ruwan ana so

mutum ya jinkirta har sai bayan awa 1 kafin ya ci abinci.
Advertisement

labarai