Harun U. Jahun" />

Dimokardiyya A Nijeriya: Tsakanin ‘Yanci Da Kangi

Da wuya a samu fassarar dimokaradiyyar da ta fi dace wa da ita, irin shahararriyar fassarar nan da tsohon shugaban kasar Amurka wato Abraham Lincoln ya yi ma ta “Gwamnati ta jama’a wadda jama’a suka zaba domin amfaninsu” shi kuwa Malam Bahaushe  take ya yi wa  mulkin dimokaradiyya  da “ Siyasa rigar ‘yanci” wato ke nan wannan na nufin dimokaradiyyar  salon shugabanci ne da su mutane za su zabi wakilan da za su wakilce su a matakai daban-daban na gwamnati. Saboda haka, idan aka hada aka fito da ma’anar maganar a sarari, sai a ce gwamnatin dimokaradiyya gwamnati ce ta wakilai da ake zaba domin su aiwatar da ayyukan da za su amfani jama’a.

Domin a samu daidato wajen gudanarwa sai aka dora gwamnatin a kan tubali guda uku wato shugabanni ma su zartarwa da majalisar dokoki da kuma sashen shari’a. A siyasance da kuma uwa uba a kundin tsarin mulkin kasa wadannan tubala kowannensu yana da dama ta kashin kansa, sai dai kuma  akwai alaka da tuntubar juna a tsakani. Don a kara karfafar tsarin. Masana siyasa da mulki sun jaddada muhimmancin  kungiyoyin fararen hula da kuma jajirtattun jam’iyyun adawa da za su zama masu sa ido a kan ita gwamnati da masu jagoranta.

Idan muka waiwaya baya, za mu ga yadda tarihi ya kebance wasu shugabannin siyasar kasar nan da kyakkyawan ambato. Sai ma wani har ya yi tunanin cewa kamar ba su fuskanci matsalar komai ba a  zamaninsu. To amma fa abin ba haka ba ne, hasali ma dai nasarar da suka samu a kan kulen zamaninsu ne ya sa sunayensu suke yi fice. Sun sha fama domin ganin tabbatuwar kasar da kuma yunkurin dora ta  a kan wata hanya mikakkiya da za ta bulle. A kan haka duk da irin gazawarsu a wasu fannonin ake yi musu uzuri ake kuma girmama su da daukaka su a matsayin gwarazan kasa. Alal misali, duk irin butulcinta, ta ya ya Nijeriya za ta manta da ‘yan kishin kasa, ta ya ya za ta manta da ‘yan siyasarta musamman na jamhuriyya ta farko?  Bayan a kasa gaba daya ga masu ganin Nijeriya da tabarau na bangaranci, labarin da kullum ya gagara karewa a  tsakanin al’ummar Gabashi,da Arewa da kuma Yammacin kasar nan ita ce dai gwagwarmayar wadannan ‘yan kishin kasa. Shekaru da yawa kafin iri na su zo tambarinsu ake buga wa, har yanzu su din ne kuma bisa dukkan alamu dukkan bangarorin kasar ba su shirya samun wadanda za su dora daga kan inda wadannan mutane suka tsaya ba.

Abin tambayar shin daga kan wadannan mutane Nijeriya za ta tsaya? Ba yadda za a yi ai maganar shugabanci nagari da siyasa a Arewa ba a ce Sardauna ba da Tabawa Balewa da kuma Malam Aminu Kano. Idan kuwa a  kasar Yarbawa ne sai ka ce musu Awolowo haka zancen yake ga kabilar Ibo ba su da kamar Azikiwe. Wadannan mutane ne da suka tafi shekara da shekaru maimakon yanzu a ce an yi nisa sosai da inganta wuraren da suka gaza, amma ina! Matsalar ma an bar hanyar da suka tafi a kanta balle a iya gane wurin da suka tsaya. Yatsu ba za su dauki lissafin abubuwan da su ka assasa yau kuma aka wargaza su ba.

Wacce irin al’umma ce haka mai ci gaban mai hakan rijiya? Wacce irin kasa ce da kullum baya take fin gaba? Me ya kawo wannan kwan-gaba-kwan-baya, musamman ga shugabannin da ‘yan kasa suka zabe su domin kai su Tudun mun tsira? Ba shakka akwai gagarumin bambamci tsakanin shugabannin jiya da na yau. Shugabannin jiya suna da manufa da kuma akidar ci gaban kasa wadda kowannensu da gaske yake. Kuma duk da cewa suna da sabanin fahimta ba ta hana su haduwa tare domin yi wa kasa aiki ba. Idan batun na ba da dan misali ne cikin ‘yan siyasar Arewa na da, yana da wahala a samu adawa mai tsanani irin yadda ta kwashe tsakanin Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna da kuma Marigayi Malam Aminu Kano. Adawa ce zunzurutu, to amma saboda kowannensu ya saba da abokinsa ne ba a kan bukatar kansa ba, sai domin bukatar  ci gaban al’umma yanzu ba wanda ba a ganin darajarsa da kima a dukkan fadin Arewa. Idan kuma tsakanin Kudanci da Arewanci ne mu tuna muhawarar Marigayi Sardaunan da Marigayi Anthony Enahoro dangane da bai wa Nijeriya ‘yanci a shekarar 1956 kowanne ya saba da abokinsa ne bisa manufa da bukatun al’ummar yankin da yake wakilta.

Wannan ita ake kira da adawa ta manufa da mutunta juna. Saboda haka wannan dabi’u nasu na  siyasa yana daga cikin sirrin samun nasarar su domin na farko dai sun fahimci cewa dimokaradiyyar ita ce kadai hanyar da za yi amfani da ita domin kai wa  ga manufarsu. Na biyu sun amince su yi aikin da ba sai an yaba musu ba a zamanin da suke raye, domin abin da suke so tasirin aikin ya kai ga baya. Kamar irin yadda ya zo a labarin tsohon nan mai hikima wanda aka gan shi yana shuka ‘ya’yan dabino aka tambaye shi cewa; baba a yaushe har wannan dabinon zai fito ya girma har ka ci ‘ya’yansa a wannan shekarun na ka da kake shuka shi? Sai tsohon ya kada baki ya ce “wanda nake ci yanzu wasu ne suka shuka shi shekaru masu yawa,saboda haka ni ma ina shuka wa ne saboda ‘yan baya su zo su ci daga abin da na shuka”.

Yau abubuwan da su ke faruwa a siyasar kasar nan akwai abubuwan takaici da rashin jin dadi sosai. Babu abin kaicon da kowanne bangare sun kasa zama magadan gwarazan da yankin da suke takama da su. Ibo sun ka sa samar da kwatankwacin ko da ‘Zik din Kudu masu Gabas ne’ ba ta batun Zik din Afirka ake ba domin shi kam ya tafi. Haka nan duk da babakeren Bola Tinubu a cikin Yarbawa amma har yanzu ya kasa zama Awolowon Kudu Maso Yamma. Su kuwa ‘Yan Arewa tun da aka sare musu Gamjinsu ba su dasa wani ba, balle ‘yan Arewan su shiga  karkashin inuwarsa su huta.

A siyasar yau, shugabanni sun kauce daga abin da aka tsammaci na gyara da ci gaba daga wurinsu. ‘Yanci ya zama kangi, talakawa ana harbinsu da harsasan da suka yaki zaluncin jiya. Abin kaico su ne  wadanda suka yi wa talakawa alkawarin aljannar duniya sun buge da dandana musu azaba. Sun gama cin moriyar ganga sun jefar da kwaurenta, sai dai da alama yanzu an fara gano cewa wannan kwauren aikinsa sa fa ya fara dawo wa. Domin mun fara ganin an fara zuwa bola ana kokarin dauko yasashen kwauren. Wani abu da na yi mamaki ga wadannnan ‘yan siyasar  da suke rike da madafun iko shi ne kasa fahimtar rawar da adawa take takawa a dimokaradiyya balle su amfana daga wasu abubuwan da ‘yan adawar suke fada hatta dan cikin gida bai gagara a gasa masa aya a hannu ba. Musamman idan har ra’ayin na sa ya saba da ra’ayin shugaba, to idan ko haka ne ta ya ya za a ci gaba? Wannan fa ba zancen sauran matsalolin gudanarwa ake ba. Irin hakan shi ya haifar da faduwar gwamnatin baya kuma ga tarihi yana neman maimaita kansa. Abin da ya faru na ficewar wasu daga cikin sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC ranar Talata ya isa misali.

Mai makon ganin daukar darasi daga matsaloli da kuma gazawar PDP sai suka kasa fahimtar kome daga tarihi. Sun kasa gane cewa dimokaradiyya fa ake yi wanda ana zabar mutum  ne domin ana zaton zai yi abin da ya dace. Ba kuma kiyayya ba ce da zarar an fahimci shugaba ya kauce layi ko da kuwa jam’iyyar da kake cikinta ne to a kira shi zuwa ga saiti. Yin hakan shi ne siyasa ta  manufa da ci gaba ita ce siyasar akida, sabanin abin da muke gani a siyasar  Nijeriya ta yau. Siyasar da naka ba ya laifi ba ko da ya yi wa mutane alkawarin zuma amma ya bige da dura musu madaci! Kasar da ma fi yawan ‘yan siyasarta da suke mulki a yau sun yarda da dimokaradiyya ne kawai  lokacin da suke neman kuri’ar talakawa amma a ofisoshinsu ba su da mararraba da mulkin Dan Tulu na cikin littafin “Gandun Dabbobi”.

Exit mobile version