'Dimokradiyya Irin Ta Amurka' Ta Bar Iraki Cikin Rugujewa
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Dimokradiyya Irin Ta Amurka’ Ta Bar Iraki Cikin Rugujewa

byCMG Hausa
3 years ago
Amurka

A ranar 29 ga watan Agusta, wani mummunan rikici ya barke a Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 30, tare da jikkata daruruwa. Hatta yankin “Green Zone” da sojojin Amurka ke ba da kariya, an kai musu hari da rokoki.

Jaridar New York Times ta ce, mai yiwuwa hakan na iya zama mafarin wani yanayi mafi hadari ga Iraki.

  • Gwamnatin Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan 10 Ga Manoma Domin Tabbatar Da Shuka Da Girbin Hatsi A Lokacin Kaka

Tun bayan zaben da aka yi bisa tsarin “dimokiradiyya irin ta Amurka” a Iraki a shekara ta 2005, ba a taba samun nasarar kafa gwamnati ba.

Amurka

Bayan kusan shekaru 20 da fara aiwatar da abin da aka kira “Gyare-gyaren demokradiyya”, matakin ya lalata Iraki kwarai da gaske.

A fagen siyasa, Amurka ta shigar da tsarin siyasar dimokuradiyya na yammacin duniya zuwa cikin Iraki, wanda a zahiri ya haifar da rarrabuwar kawuna a fannin siyasar kasar, kuma da wuya bangarorin siyasa daban-daban su cimma nasarar sulhu.

Ta fuskar tattalin arziki, yake-yake da tashe-tashen hankula sun haifar da asarar da ba za a iya misaltawa ba ga tattalin arzikin Iraki.

Alkaluman sun nuna cewa, a shekarar 1990, GDP na kowane mutum a Iraki ya kai dala 10,356, amma ya zuwa shekarar 2020, adadin ya yi kasa zuwa dala 4,157 kacal.

A fannin tsaro, saboda rudanin siyasar da aka samu a cikin gidan a Iraki, ta’addanci ya bazu cikin sauri, kuma al’ummar kasar sun sake zama wadanda abin ya shafa kai tsaye.

Ahmed al-Sharifi, kwararre kan al’amuran da suka shafi dabarun Iraki ya yi nuni da cewa, manufar mamayar da Amurka ta yi a Iraki, ba wai don a taimaka wa Irakin wajen tabbatar da dimokuradiyya kamar yadda ta fada ba ne, sai dai don karfafa ikon Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, mutane kusan miliyan daya a Gabas ta Tsakiya, sun fada karkashin rugujewar gidaje irin na “dimokradiyyar Amurka”.

Dole ne kasashen duniya su yi la’akari da laifukan da Amurka ta aikata a Gabas ta Tsakiya, tare da neman adalci ga wadanda suka yi hasara sakamakon hakan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Asalin Abin Da Ya Sa Jama’a Ba Su Ganin Alfanun Tallafin Mai – Dakta Yakubu

Asalin Abin Da Ya Sa Jama’a Ba Su Ganin Alfanun Tallafin Mai - Dakta Yakubu

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version