Connect with us

KIWON LAFIYA

Dinbin Amfanin Rogo A Jikin Danadam

Published

on

Rogo yana daga cikin abinci wanda ake amfani da shi na yau da kullum, yana da wasu faidodi masu yawa da kuma sinadarai na abinci masu gina jikin Danadam.
Amma babban abin da za mu yi bayani shi ne, sinadari wanda yake a cikinsa wato Vitamin (B17), wannan sinadari yana daya daga cikin abinci masu jina jikin Danadam, kuma magani ne wanda yake hana Kamuwa da ciwan daji (Cancer), sannan yana kuma magance cutar a matakin farko idan ba ta yi tsanani ba. Haka shi ma dankali yana da irin wannan sinadarin, amma hanyar da ake amfani da shi shi ne, ana dama shi sai a sha kamar yadda ake shan wasu naikan abin sha. Wani kwararran likita mai suna Dakta Shuaibu ya tabbatr da wannan bincike.
Bayan haka kuma, bincike ya nuna cewa, a kan sami irin wannan nain sinadarin a mafi yawa daga cikin ‘yayan itatuwa, kamar kwallon mangwaro da dai sauran su.
Gargadi
Cin danyen garin rogo kan illata lafiyar Danadam cikin sauri. Tabbas danyen rogo guba ce ga rayuwar Danadam, saboda gubar da yake dauke da ita mai suna Cyanide a turance. A kasar larabawa ba sa cin danyen rogo har sai sun shanya shi, sannan su mayar da shi garin kwaki, kafin su ci ko su kai kasuwa. Saboda babbar hanyar rage wannan guba na Cyanide ita ce, shanya garin kwaki a rana ko jika shi da ruwan zafi, shi ya sa cin teba ya fi inganci kan jika gari a ci shi haka nan. Babbar illar da garin kwaki yake wa jiki ya hada da matsalar ido, ciwon hanta, ciwon makogworo da dai sauran su. Sanin kowa ne cin danyen rogo ya sha kashe mutane har lahira, kai har ma dabbobi, saboda yanzu haka akuya ko tinkiya ta ci danyen rogo, to tabbas ba ta kwana duniya, idan baka sani ba tambayi Bafulatani. Duk dai hakan na faruwa ne saboda gubar nan ta Cyanide. Saboda haka, muna kira ga masu cin kwaki da su rinka jika shi da ruwan zafi, ko a yi teba a ci shi. Sannan a kiyayi cin danyen rogo dan kare kai daga mutuwa ko afkuwar cuta. Allah kyauta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: