Dino Melaye: Ba INEC Ce Ta Kashe Zomon Ba…

Tare da Nasir S. Gwangwazo, Abuja

 

A kwanan nan ne a ke ta faman jin takaddama tsakanin Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi da hukumar zabe ta kasa, INEC, kan kiranye da jama’ar mazabar sanatan ke neman yi ma sa, to amma abin mamaki shi ne, maimakon sanatan ya kaddamar da yakin cacar baki tsakaninsa da al’ummar mazabarsa, sai kuma ya ke neman yin kaza huce kan dami, ya na mai hucewa a kan INEC, wacce ita kanta ba ita ce ta kashe zomon ba, rataya a ka ba ta.

To, amma duk a wannan rikita-rikita da ke faruwa, bat a yi kama da ainihin Dino da a ka sani ba kafin ya zama sanatan Nijeriya. Idan za a iya tunawa, ya na cikin ’yan siyasar da a kullum su ke caccakar gwamnatocin baya, inda ko a baya ya taba shiga cikin jerin gwanon masu zanga-zanga a lokacin da a ke yaki da gwamnatin PDP a karkashin Goodluck Jonathan.

Haka nan da irinsu Dino Melaye a ka taru a ka yi fafutukar balle kofar majalisar dokoki ta kasa a lokacin da a ka zargi gwamnatin baya da shirya kulla-kullar tsige tsohon kakakin majalisar dokokin kuma gwamnan jihar Sokoto a yanzu, Aminu Waziri Tambuwal.

Bugu da kari, ya na cikin ’yan gaba-gaba da su ka rika hada hannu waje guda da shugaban hukumar EFCC ta kasa na yanzu, Ibrahim  Magu, wajen adawa da masu cin hanci da rashawa a lokacin gwamnatin baya.

Ire-iren wadannan abubuwa sun sanya da yawan talakawan Nijeriya na da karfin gwiwar cewa, idan jagoran ’yan adawa na baya kuma shugaban kasa a yanzu, Muhammadu Buhari, ya kafa gwamnati, Melaye zai kasance cikin ’yan gaba-gaba wajen mara wa gwamnatin baya wajen fitar da jaki daga duma kan irin zargin da a ke yiwa jam’iyyar PDP na jefa kasar a halin da ta tsinci kanta tsawon shekara 16.

To, amma babban abin mamaki da takaici shi ne, tun da farar safiyar kafa gwamnatin, sai a ka wayi gari a ka ga Dino a cikin ’yan gaba-gaban hada kai da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, su na rigima da fadar Buhari kan abinda mafi yawan ’yan Nijeriya su na marawa shugaban kasar baya ne, duk da cewa, shi Dino ya na cikin sanatocin da a ke ganin albarkacin Buharin su ka ci a ka zabe su a jihohinsu, saboda sun shiga guguwar Buhariyya.

Baya ga nan kuma ya shiga rikici da gwamnan jiharsa ta Kogi, Yahaya Bello, wanda ke tare da fadar shugaban kasa. Rikicin ya janyo wa al’ummar mazabarsa asarar rashin samun cikakken wakilci a majalisar dattawa, saboda yadda hankalin mai wakiltarsu a kullum ba ya jikinsa. A na ganin cewa, ya ma fi mayar da hankalinsa wajen taruka da manema labarai, don yaki da gwamnan nasa.

Ta yiwu irin wannan rashin samun cikakken wakilci ya sanya al’ummar yankin da ya ke wakilta su ka gaji su ka lura da bukatar yi ma sa kiranye, don ya dawo gida ya zauna, in ya so su tura wanda zai fi shi mayar da hankali da ayyukan  majalisa. Wannan yunkurin kiranye ne ya bude babin rigimar sanatan da hukumar zabe ta kasa, INEC.

Maimakon Sanata Dino ya koma mazabarsa ya fara neman shiri da su al’ummarsa da su ka sanar da INEC bukatarsu ta a dawo da sanatan, sai ya bige da rigima da INEC a kotuna, ay kuma shiga yi wa hukumar turaja iri-iri, alhali ita kanta tilasta ma ta al’ummar yankin su ka yi a kan sai ta zo ta gudanar mu su da zaben kiranyen, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Za mu cigaba a mako gobe in sha Allahu.

Exit mobile version