Dirama Ta Kaure Tsakanin Dino Melaye Da ‘Yan Sanda

Ya Diro Daga Mota Bayan An Damke Shi

Za A Gurfanar Da Shi A Jihar Kogi

Daga  Sulaiman Bala Idris

 

Tun shekaran jiya aka soma wata ‘yar kwarya-kwaryar dirama tsakanin Mai Wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye da jami’an ‘yan sandan Nijeriya.

Diramar dai ta samo asalin damke Sanatan da Jami’an Shigi da Fici Na Nijeriya ta yi a Babban Tashar Jirgin Sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja a shekaran jiya.

A jiya ne Sanatan ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan SARS, wadanda kuma suka kuduri aniyar komawa da shi Jihar Kogi inda za a gurfanar da shi tare da wasu da ake zargi da safarar makamai marasa ka’ida.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da LEADERSHIP A Yau cewa, Sanata Dino Malaye ya diro ne daga motar ‘yan sanda dake dauke da shi, inda yayi yunkurin arcewa.

Lamarin na yunkurin arcewar Melaye ya auku ne a daidai shataletalen ‘Area 1’ dake unguwar Garki a Abuja. Inda bayan dirowarsa daga motar wasu katti hudu suka dakile yunkurin ‘yansanda na fita da shi daga Abuja. Diramar wacce aka fara ta daidai karfe 2:00 na rana an kwashe mintuna shida ana yi.

Sanatan ya nuna turjiya matuka ga jami’an ‘yan sandan, inda yayi ta fadin, “Sai dai ku harbe ni. Ku kashe ni a nan. Babu inda zan bi ku, ba zan je Kogi ba.”

Duk wani kokari da jami’an ‘yan sandan suka yi wurin ganin sun dauki Sanatan domin su jefa shi a mota, lamarin ya ci tura. Inda ana tsaka da wannan dirama sai ga wata mota kirar Hilud shake da wasu katti su uku, suka sungumi Sanatan suka jefa a motarsu.

Yayin da lamarin ke tsaka da afkuwa, ‘yan kallon da

Exit mobile version